Monday, November 15, 2021

'YA'YANMU


 

'YA'YANMU
 
Lokaci-lokaci, Lalo yakan kai wa su Ɗan'amadu ziyara. Lalo ya sauya sosai, ya yi kuɗi. Haka suke zama kowa yana kurin irin abubuwan da yake samu da irin gararanba ko kitimurmurar da yake yi. Suna hirar, suna shan kayan maye.
 
“Ku fa wahala kawai kuke yi?" Lalo ya ce da Ɗan'amadu, "Ga inda ake samun kuɗi a banza, kawai taku za ku sauya, ku zama manyan jajayen wuya."
 
"Ka yi mana bayani a buɗe mana, ka tsaya kana ja mana rai."
Lalo ya yi dariya, "To wanne irin bayani zan yi muku da ya wuce wannan. Mutum ɗaya kawai za ku sanƙame sai ku samu kuɗin sama da shekara biyu a wannan harkar da kuke yi na sayar da kayan maye."
"Sanƙamewa? Kana nufin sace mutane, kidinafin?"
"Harkar da ta ke ja kenan." Ya ci gaba da dariya. "A nan dai wahalar da kanku kawai kuke yi, ni ma ina kawo muku ziyara ne don mun saba."
 
Suka ɗan yi shiru na lokaci. Kana Ɗan'amadu ya jinjina kansa.
"Tuntuni na yi wannan tunanin, da za ka buɗe mana yadda aikin yake da mun fantsama ciki."
"Haka ne. Za ku bar harkar wuƙa, ku koma bindiga da kwanan daji a wasu lokutan." Cewar Lalo.
“To, me za a fasa. Kawai ka ɗora mu a hanya."
Lalo ya miƙe, ya kama hannun Ɗan'amadu, ya ja shi, suka bar wurin.
Wannan tafiya, ita ce silar komawar Ɗan'amadu da wasu abokansa harkar sace mutane da karɓar kuɗin fansa. Wasu lokutan akan ba su kwangilar kashe mutum a biya su.
Da yake su Ɗan'amadu, sun faro iskancinsu tun suna ƙanana, kuma sam ba su san tarbiyya ba, ba su san mutunci ko darajar mutane ba, nan da nan suka zamo manyan masu satar mutune a daji da kashe-in-biya ka.
 
Da tafiya ta yi tafiya, Ɗan'amadu da Lalo suka ja tawagarsu, suka ware, suka sami yaran da suke kamo musu mutane, a zo a biya kuɗin fansa.
Haka nan idan wata kwangilar kisa ce suka samu, sai su yi da kansu ko su ba yaransu su yi. Suka zama gagarumai 'yan ta'adda.
 
YA FITO KASUWA
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓi, Abubakar (0806 026 7571) ko Nazifi Mai Littafi (07038833021)

1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...