HAUSAWA: QABILA KO YARE?
Daga Kabiru Yusuf
Shin Hausawa sunan qabila ne ko sunan harshe?
Su dai Hausawa, suna ganin kansu qabila ne. To amma duk wanda ya tsaya ya bayyana ma’anar qabila sosai, sai ya ga Hausawa sun qi shiga.
Misali bisa bayanin marubuta, qabila al’umma ce mai asali xaya, da yare xaya, da kamanni (watau qirar jiki) kusan iri xaya, da al’adun gargajiya iri xaya, da ra’ayin zaman duniya (watau falsafa) xaya, da sauran irin su. Kuma lallai ne cikin wannan al’umma kowa yana da’awar shi xan qabilar ne.
To idan aka biya wannan bayani kuwa, sai a ga bai kamata a kira Hausawa da sunan qabila ba. Sai dai a ce su taro ne na qabilu daban-daban da suka cuxanya da juna, kuma suka taru, suke magana da harshe xaya. Ita kanta kalmar “Hausa” a wurin Bahaushe tana nufin “harshe” ne. Akan ji Bahaushe ya ce, “Ban ji wannan Hausar ba,” watau bai gane wannan yaren ba kenan. Ko kuma ya ce ya ji ana “wata Hausa,” watau, ya ji ana magana da wani harshe.
Bugu da qari, idan ka tambayi yawancin haifaffen qasar Hausa, ka nemi ya faxa maka qabilarsa, sai ya ce maka, shi Bafillace ne, ko Babarbare, ko Buzu, ko Banufe, ko wata qabila daban. Ga shi kuwa a wannan harshen bai san ko sannu ba.
Kuma ana samun qabilun da ba su ji Hausa ba, amma su riqa da’awar su Hausawa ne, misali Abakwa Riga na Wukari da Takum da Lafiya.
(an ciro wannan bayani daga littafin ‘Zaman Hausawa’ bugu na biyu, na Habib Alhassan da Usman Ibrahim Musa da Rabi’u Mohammad Zarruq)
Wlh ko waye me wannan rubutun jaki ne.
ReplyDeleteThis comment has been removed by the author.
ReplyDeleteIdan Hausa ba ƙabila bane,
ReplyDeleteTo tayaya aka samu waɗannan siffofin ?
Wanda duk al'ummar da suka cika waɗannan siffofin to hakan na nufin ƙabila ne
Kuma ko wacce da nata
1-tayaya al'ummar Hausa su samu ?
2-tayaya ƙasar Hausa ta samu ?
3-tayaya Ɗabi'un Hausa su samu ?
4-Tayaya al'adun Hausa su samu ?
5-tayaya harshen Hausa ya samu ?
6-Tayaya (DNA) genetic, ƊIN ƙabilar Hausa ya samu wanda yasha banban dana kowace
7-Tayaya Adabin Hausa ya samu
Duk mai wannan tunanin ya daina jahilatan kan shi
Hausa ƙabila ce wanda duk Afrika babu kamar ta