GABATAR DA LITTAFIN RUBUTUN FIM
Daga Bala Anas Babinlata
Barkan mu da Sallah, Allah Ya maimaita mana. Ya kare mu daga dukkan masifu, ya kawo mana karshen annobar data tsayar da al'amuran mu na rayuwa.
Kafin Azumi na nemi shawarwarin ku game da sakin sabon littafina mai take Rubutun Fim, in da aka samu rinjaye na shawarwari akan a yi hakuri a bar shi zuwa bayan sallah, Alhamdu lillahi, ga bayan sallah ta zo, amma dan sauyin da aka samu bai taka kara ya karya ba. A gaskiya zai zama kuskure idan muka ce zamu yi taron fuska da fuska na gabatar da wannan littafi, a taron da zai dauki kimanin mutune 300 a waje daya. Ba a gwamnatance ba ko a lafiyance kuskure ne babba. Saboda haka ne na yi nazari a tsanake game da gabatar da wannan littafi.
Dalilina na yin wannan littafin biyu ne, na farko ina so na bayar da gudunmawa ta ga 'yan uwana marubuta da masu sha'awar son yin rubutu musamman na fim. Na biyu wanda shi ne kashin bayan wallafa littafin. Zan yi bayaninsa a takaice duk da dogon labari ne. Da fatan zaku jure karantawa.
Rubutu shi ne Kashin bayan kowane fim, wannan ne ya sa finafinan da aka yi a baya suka yi tasiri, saboda akwai hannayen marubuta, musamman na littafi a ciki. Idan mutum yana da ja ya dubi gidan talabijin na Arewa24 kusan duk marubutan Drama dinsu 'ya'yanmu ne marubutan littafi. Sanin muhimmanci Marubuta a harkar fim ya sa na rinka janyo marubuta ta hanyar workshops don su bayar da gudunmawar su. Rubutattun Littattafai suna taimaka wa sosai a duniya wajen samar da labaran fim, amma mutuwar kasuwar littafi, ko na ce sauyawar kasuwar daga bookshop zuwa online ta kassara samuwar nagartattun littattafai.
A karshen shekarar da ta gabata (2019) na gano kasuwar littattafan ba mutuwa ta yi ba, makaranta sun rasa in da zasu samu littattafan su saya ne, wala a bookshop ko online. Na gano wannan ne daga tattaunawa da mutane a Facebook. Wannan ne dalilin da ya sa na kafa group a Telegram in da marubuta zasu gana da makaranta, su kuma nemi duk littafin da suke so su saya ta book on demand.
Sai dai in da gizo ke sakar, lokacin da muka kira taron Marubuta an samu halarta, amma sai muka fahimci yawancin Marubutan na Da dana Yanzu sun samu tabuwar tattalin arziki, ta yadda ko tsofaffin littattafan su ba zasu iya bugawa a kwamfuta ba, ba wai maganar dab'i ba. Wannan sai ya sa muka sake tara marubutan a ofis din Professor Yusuf Adamu da tunanin mu hada kudi mu yi kamfanin book on demand da website. A nan Professor ya janyo hankalina da kada a yi ta surutu na kawo Marubuta ofishin sa an yi musu wayo. Duk da mun yi dariya, amma maganar ta tsaya min a rai sosai.
Sai na shiga tunanin ta wacce hanya zan bi na taimaka a kafa wannan kamfani tun da Marubuta na cikin wani yanayi? A wannan gabar ne na karkade wannan littafin nawa Rubutun Fim na kammala shi, da tunanin idan muka tara masoyanmu muka gabatar da shi dan abin da aka samu sai na yi amfani dasu na kafa Hausa novels Foundation da zata samar da website da ofishin yin book on demand da zai amfani duk marubuta.
RANAR GABATAR DA LITTAFIN FIM
Kamar yadda na shirya za a gabatar da littafin nan kafin Azumi aka samu akasi, wanda ya sa aka daga zuwa bayan Sallah, to ga bayan Sallah Allah Ya kawo mu, amma taro fuska da fuska ba zai yiwu ba. Na so mu yi amfani da wannan gabatarwar mu gamu da masoyanmu amma Allah bai yarda ba. Amma duk da haka ba zamu fasa gabatarwar ba.
Za a yi gabatarwar ne online. Abin da muke bukata a wannan gabatarwar shi ne gudunmawa daga Marubuta da Makaranta. Akwai Marubuta Sahun farko da na ware wadanda kowane zai sayi kwafin littafin fiye da daya, ma'ana zai sayi nasa ya kuma dubi wani Marubuci mai karamin karfi ya sai masa. Haka nan sauran marubuta da suke da hali zasu sayi nasu kwafin. Sai Makaranta, su ma tasu gudunmawar ita ce su sayi kwafi na littafin, ma'anar wannan gudunmawar ita ce a karshe mu iya tara kudin yin website da bude ofis da na'urar buga littafi na Book on Demand na kowane littafi Makaranci ke bukata.
Sai dai a yi mana afuwa, don zamu wallafa sunayen duk wadanda suka bayar da gudunmawar su ta hanyar sayen littafin don kada tarihi ya manta da kokarin mutane.
Farashin littafi Naira dubu daya. (Tsurar kudin littafi ne wannan, ban da delivery.) Ga masu bukatar online copy za a iya samunsa a okadabooks.
Za a sanar da Lambar bankin da za a biya kudin a ranar Gabatarwar.
Ranar Gabatarwar ita ce Litinin 8 ga watan June, 2020.
Allah Ya ida mana nufi.
A taimaka a taya ni sharing.
Bala Anas Babinlata