DANFILLO MAI KANKARA
Gajeren Labarin Dariya
Danfillo ne ya shigo birni cikin azumin nan, ko'ina ya je
sai ya ga ana hada-hadar siye da sayarwar kankara babu kama hannun yaro. Danfillo
bai yi kasa a gwiwa ba, ya matsa kusa da wani Bahaushe, ya ce "Hwai Kado,
do Allah me aka yi da dutsen ruwa haka naga ana ta siyenta?"
Bahaushen ya dube shi, ya ce "Danfillo kenan, ai
kankara ce, mugun tsada take, yanzu ka ganta nan ana siyar da ita Naira
dari-dari da an jima za ta iya komawa Naira dari da hamsin ko dari biyu, domin
da Naira talatin Naira hamsin ake siyar da ita, kafin ta koma darin."
Danfillo ya koma gefe ya yi shiru yana tunani yana girgiza
kai, ya ce "Lallai harkar kasuwanci ta samu, ai wannan kawai sai in sara,
ba zan sayar ba sai ta yi kwana biyu."
Haka kuwa aka yi, Danfillo ya yi sauri, ya koma ruga, ya
siyar da shanunsa guda biyu, ya hada da kudin da ke hannunsa, ya dawo cikin
birni ya rinka bi, yana siye duk kankarar da ya tarar, yana kaiwa masaukinsa
yana jibgewa, har ya siyi buhunhunan kankara da yawa iya na kudinsa ya jibge,
kana ya zauna yana hutawa.
Ya ce, "Alhamdulillahi, ka ga yanzu zuwa jibi ko gata
sai in fito da su in rinka siyarwa Naira dari dari biyar-biyar hankalina
kwanshe." Ya yi dariyar mugunta kana ya dora da cewa, "Kado bai san
kasuwanci ba, ni zan nuna musu mun san binni."
Washegari, Danfillo shiga masauki don gewayar kankara, tun
daga kofa ya ci karo da ruwa malale, sannan ga buhunhunan kankara sun yi
lankwam a cikin ruwa, duk kankarar ta zagwanye ta zama ruwa. Ai kuwa Danfillo
ya dora hannu a ka, ya dasa ihu, wasu da ke kusa suka matso gare shi, suna
tambayar lafiya.
Danfillo ya zayyane musu abin da ya faru, cewar ya siyi
dutsen ruwa ta koma ruwa. Mutanen nan suka yi kokarin kecewa da dariya, amma
suka gintse, daya daga cikinsu ya ce, "Yo kai Danfillo wa ya gaya maka ana
ajiyar kankara?"
Suka fashe da dariya.
(c) Kabiru Yusuf Fagge
No comments:
Post a Comment