Sunday, May 12, 2019

Gajeren Labari: ROMON DIMOKRADIYYA


ROMON DIMOKRADIYYA
Kabiru Yusuf Fagge

Muna tafe, tafiya mai nisa, kuma mai wahala, duk da motar da muke ciki akwai na'urar sanyaya wuri da kuma tausasan kujeru da nutsuwa, amma a hakan duk na jigata saboda rashin kyan hanya ga kuma zafin rana.
Cikin damuwa, na dubi Cif Kamfen na ce masa, "Wai shi ma wannan garin da za mu je, duk a cikin jihar Natsira yake?"
Cif Kamfen ya yi dariyar yake, shi ma dai kallona yake yi, ya ce "Honorabil ka manta ne, wancan karon fes tenuwa ai mun zo, garin Kumaji ne fa, ka tuna da muka zo, har muka yi musu alkawaruka, wadanda sun fi damuwa da batun ruwan sha..."
Na yi shiru ina tunani, can dai na tuna din, "Gaskiya kam, sai yanzu na tuna, ni tuni ma na manta da su da dukkan alkawuran da muka yi musu a wancan lokacin kafin mu ci zabe..."
"Kuma ka ga kamar yadda ka ce ka manta da garin, haka ma mun manta ba mu cika musu alkawarukan da muka daukar musu ba." Cewar Cif Kamfen.
Na girgiza kai, "Kwarai kuwa, ai abin ne da yawa, gari kamar Natsira ba karamin gari ba."
Cif Kamfen ya dube ni, "To yanzu dai ga shi mun dawo gare su da wata bukatar ya kake ganin za a yi?"
Na yi murmushi, "Idan ka dubi wahalar tafiyar nan da hanyar nan, ka san da wuya a samu masu ilimi a garin nan, bare kuma wayayyu, kawai muna zuwa zan sake yi musu wani alkawarin, don su sake zabarmu, daga baya idan mun tuna da su sai mu yi musu rijiyoyin burtsatse ko guda biyu ne, idan kuma mun manta shi kenan, ai ba su kadai ba ne mutanen jihar nan ba." Na kammala maganar tawa ina wage baki cikin yake, a raina Allah-Allah nake mu je garin mu yi abin da zamu yi, mu baro su.
Na lura da irin kallon da Cif Kamfen yake yi min, a zahiri yana so ya gaya min abin da na fada ba daidai ba ne, amma kawai ya yi min shiru. Kuma ni da shi mun san abin da muke yi zalunci ne, amma mun take gaskiya.

Lokacin da muka karasa cikin garin Kumaji, a raina na tabbatar lallai garin ya ci sunansa kumaji, gabadaya a cikin damuwa nake, farinciki daya da ya darsu a raina, shi ne da muka tarar da mutanen garin suna jiranmu. Na dubi Cif Kamfen na ce, "Wai har kun cika aiki, kun tara mutane?"
Cif Kamfen ya ce "Kwarai kuwa, ai tun kwanaki hudu da suka wuce na sa aka gaya wa Dagaci zuwanmu, kuma ka san ba zai ki tara wa maigirma Gwamna mutane ba. Idan ka lura ma, da alamu tun dazu suke jiranmu."
Na ce, "Na ga alama, to mu yi sauri, mu gama abin da ya kawo mu, mu bar kauyen nan, wallahi na gaji."
Babu bata lokaci muka firfito daga cikin motocinmu, muka hau kan dandamalin da aka tanadar mana don yi wa jama'ar bayanin makasudin zuwanmu, da kuma bukatar kuri'unsu. Sai dai na lura da al'ummar garin, ba kamar na sauran garuruwan da muka jejje ba, wadanda suke rinka yi mana kirari da bambadanci, su wadannan sun yi jugum, suna ta muzurai kamar mayu. Koda yake ba lallai ba ne su gane fifikon matsayina na gwamna ba, don haka na yi musu uzuri.
Shugaban jam'iyya ne ya fara jawabi, sannan ya gabatar da ni a matsayin gwamnan jiha, kana ya nemi jin wani abu daga bakin Dagaci.
Dagacin garin, wani tsoho ne wanda ya haura shekaru tamanin a raye, yana dogara sanda ya matso kusa damu, a tare da shi akwai wani saurayi dauke da ruwa a cikin wata matsakaiciyar kwarya, ruwan ya yi fari-farin farar kasar . Haka muka tsaya muna kallonsu cikin mamaki, tare da tunanin ko dai mutanen nan wani siddabaru za su yi mana na cin zabe, don mu komai ma muna maraba da shi in dai yadda zamu ci zabe ne.
Dagaci ya fara magana cikin rawar murya ya ce, "Maigirma gwamnanmu, a wancan zuwan kafin ka hau wannan kujera, lokacin da ka zo neman mu zabe ka, ka yi mana alkawarin samar mana da tsaftataccen ruwan da zamu rinka sha muna ibada, da amfanin yau da kullum, to wannan shi ne ruwan da muke yin duk wadancan abubuwan da su..." Dagaci ya nuna kwaryar ruwan nan, "Al'ummar wannan kauye sun ce sun yarda za su zabe ka, amma a matsayinka na bako sai ka sha wannan ruwan, wanda yanzun nan aka debo shi daga gulbi saboda girmama bakinmu."
Dagaci ya umarci saurayin nan ya miko mana ruwan, ni da Cif Kamfen muka yi wa juna kallon-kallo, cikin karfin hali na mika hannu na karbi kwaryar don in nuna musu zan sha. Abin da ba su sani ba, a irin wannan lokacin babu abin da ba zan iya yi ba, don samun kuri'arsu. Na karba.
Ina kai kwaryar saitin bakina tare da kokarin runtse idona don kar in ga yadda ruwan yake, don in samu in sha a haka, amma sai wani wari mafi gigitawa ya daki hancina, na yi yunkurin cillar da kwaryar, amma na sai na fasa, haka dai na yi jim na 'yan sakanni kaina na juyawa, ban san lokacin da na kifa kai, na kurbi ruwan ba, wanda har wani galmi-galmi yake yi, kamar wanda aka jika karkashi a cikinsa.
Amai ya antayo zai fito min na guntse shi, na yi kicin-kicin, na mayar da shi, idanuna suka yi gulu-gulu don ma a cikin gilas suke. A haka, cikin wannan halin aka ba ni dama, na samu, na dan furta 'yan kalmomin da kowa a wurin ya san ba a nutse nake ba, ni kaina ban san abubuwan da na fada ba, na san dai kalamai ne na karya da alkawura da muka saba wadanda na dade da haddace su, muka yi abin da ya kawo mu, muka bar kauyen nan.
Tun da muka bar kauyen Kumaji na shiga halin rashin lafiya, don haka babu wani waje da muka kara zuwa, sai gida. A haka na kwana cikin rashin lafiya, washegari ma na farka ba lafiya, ban yi wata-wata ba, na sa aka shirya tafiya ta zuwa Jamus, don a duba lafiyata kar in mutu a banza, ban koma kan kujerata ba.
Sai dai abin da ban sani ba, 'yan jarida da 'yan midiya sun fahimci duk abubuwan da suka faru, don haka wasu daga cikinsu wadanda ba ma toshewa baki da cin hanci, da wadanda ba su yarda da cin hanci ba, suka rubuta labari a kan hakan, suka watsa.
Wannan shi ya hana ni zarcewa a kan kujerata, na yi biyu babu, ga rashin lafiya, ga rasa kujera. Sai dai akwai tunanin da ya fi damuna, shi ne; su al'ummar Kumaji irin wannan ruwan suke sha kuma su rayu? Wa zai ba ni amsa?
Na gode.

Kabiru Yusuf Fagge

1 comment:

  1. Hmmmm...tsakani da Allah Al'umman ƙauyen kumaji sun yi matukar burgeni ina ma ace wannan labarij jama'ar kasarmu za su karanta shi su dauke shi a wani makami mai girma tsakanin su da shugabanni su na tabbaya ba karamar nasara za a samu da sauyi ba

    ReplyDelete

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...