Tuesday, June 11, 2019

Gajeren Labari: CAKIN FOYIN








CAKIN FOYIN (Checking Point)
Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Malam Tukuro Cakin Foyin yana zaune kan tsohuwar kujerarsa da mutanen unguwar suke kira da bugun Koje Masassaki saboda tsananin tsufanta, ban da tsananin dauda da ta yi saboda zama har tankwarewa ta yi ta yadda kullum idan Cakin Foyin zai zauna a kanta sai ya tokareta da dutse.
Wasu sun ce sama da shekaru arba'in da tara da aka sassaka kujerar nan kullum sai Cakin Foyin ya yi zaman sama da awa bakwai zuwa takwas a kanta, don haka dole ta jigata.
Tsananin zaman sa ido ne ya sa aka sa wa Malam Tukuro suna 'Cakin Foyin' saboda duk wanda ya zo wucewa sai Malam Tukuro ya lalube shi da idanu, musamman mata. An ce yakan iya sanin adadin mata da maza, yara da manyan da ke wucewa ta hanyar a kullum, kuma ya san iya adadin kayan da kowa yake sawa na yau da gobe, don wasu matan ma hatta dan kamfan da suke sawa Cakin Foyin ya sani. Ya haddace irin tafiyar kowa, ya san masu yi masa magana idan sun zo wucewa, ya san masu yi masa kallon banza ko tsaki.
Haka nan ya san adadin ababen hawan da suke wucewa, kana yana gane baki da kuma masu wucewa yau da kullum ta hanyar.


Bayan sunan 'Cakin Foyin' da ake gaya masa a yanzu, wasu na kiransa da Sikana (scanner) saboda yadda yake yi wa mutane kallon kurilla, wasu kuma su ce masa madubin-dubarudu (microscope), kai har da masu kiransa da suna 'Gajimare.'
Kamar yadda gashin bakin Cakin Foyin yake dan tsurut a kan gaban hancinsa mai kama da na Hitila, haka gemunsa dake haba yake ziriri kamar tsatso, wadanda duk da tsayin gemun gashin bai fi a kirga adadinsa ba - wasu sun ce tsabar yawan sa-idonsa ne ya sa gashin bakin da na gemun gaza samun zama a muhallinsu.
Idan Cakin Foyin na zaune a wurin nan, a wasu lokuta barci kan dauke shi idanunsa a rufe, amma za ka tarar hancinsa da bakinsa da kunnuwansa duk a bude, to wasu sun ce da su yake sa idanun.
Wataranar Asabar yana zaune ya yi fakare da shi yana aikin sa'ido, kamar daga sama sai ga wata kyakkyawar mace da mijinta sun zo wucewa, sai dai idanun Cakin Foyin gabadaya suna kan matar, sam bai ankara da garsamemen mijin nata ba, wanda baya iya barin matarsa zuwa unguwa saboda kishi.
Daf da shi, Cakin Foyin ya saki baki yana kallonta, yana fadin, "Carkwadi! Tanjirin! Tubarkallah. Baiwar Allah ke bakuwar mutum ce ko aljana, don ban taba ganinki a wannan labin ba..."
Lokacin da matar ta juya, ta dubi mijinta, ya yi daidai da lokacin da Cakin Foyin ya ji saukar wani wawan mari, wanda take ya tilasta masa fitar da hawaye, a lokaci guda kuma ya kumbura masa fuska, bai san lokacin da ya dafe wurin ba.
Sai a lokacin Cakin Foyin ya fuskanci ashe matar da mijinta suke tafe. Yana hawayen dole ya dubi mijin, murya na rawa yake cewa, "Bawan Allah kai Basamuden wanne zamani ne da za ka dubi bawan Allah tsofai-tsofai ka yi masa irin wannan barin mota da hannunka mai kama da faranti, kashe ni za ka yi?"
Duk da ran mijin a bace yake, sai da ya kusa yin dariya, amma ya murtuke ya ce da Cakin Foyin, "Ni Basamuden zamaninka ne, na zo don in hukunta ka saboda mummunan halinka..."
"Ai kuwa ka hukunta ni, don ina tsammanin ka dode min kunne daya. Wallahi da na ganka ko magana ba zan yi mata ba Basamude." Cewar Cakin Foyin.
Mijin ya ce, "Ko ba ka yi magana ba, ai kana kallon matan mutane, kuma ba zan kyaleka ba."
Cakin Foyin ya yi saurin kallonsa ya ce, "To idan na daina fa?"
Mata da mijin suka yi dariya, mijin ne ya ce. "Ka hutawa kanka. "

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...