Tuesday, May 14, 2019

DA ME ZAN BIYA ALLAH....? 1

DA ME ZAN BIYA ALLAH?....1
Gajeren Labari
Kabiru Yusuf Fagge

Wani hamshakin attajiri, wanda ya yi shekaru tamanin da daya a raye, watarana rashin lafiya ta same shi, yana fama da ciwon mafitsara, baya samun yin fitsari.
Wane tudu wane gangare, bayan aune-aune da aiki irin na likitoci tare da ba shi magunguna attajiri ya samu sauki, aka yi masa lissafin kudaden asibiti da na magunguna da na aiki, ya sa 'ya'yansa suka cake kudin har da kari saboda jin dadi.

A lokacin da likitan ke godiya, a lokacin shi kuma attajirin ya fashe da kuka, nan da nan hankalin likita ya tashi, ya dubi attahiri ya ce, "Alhaji fatan dai lafiya? Ai yanzu ba ka da wata matsala, ka samu lafiya sosai."
Attajiri ya ce, "Likita na san na sami lafiya, kawai na tuna wata buwaya ce daga buwayar Ubangiji da ta sani dole in yi wannan kukan, in sake kuka ba don bijirewa ba sai don kara tabbatar da ni'imar Allah da ya yi mana, amma hankulanmu na wani wurin daban."
"Kamar ya ya?" Likita ya bukata.
"Kamar yadda ya faru yanzu,s hekaruna sama da tamanin a raye, a rayuwar tawa kuma Allah yana ba ni damar yin fitsari a duk lokacin da na so yi, bai taba tambayata in biya kudi ba, yau dai Allah ya jarrabe ni da gaza yi sai da aka yi min aiki aka ba ni magunguna sannan na yi, gashi kun caje ni kudade kuma sai da na biya, me kake tsammani a ganinka da ace a duk shekarun nan idan zan yi fitsari biya nake, shin kana tsammanin zan iya biya?"
Likita ya girgiza kai alamun a'a.
Attajiri ya ci gaba da cewa, "To ka gani, fitsari ma kenan, bare kashi. Sannan mai gaba daya numfashin da nake yi, kana tunanin duk yawan kudina zan iya siyen numfashin awa daya a rayuwata?"
Likita ya sake girgiza kai.
"To bari in ba ka labari Likita, akwai wani babban mai kudi kuma dan siyasa a jihar nan, a lokacin da zai mutu da ace ana siyen numfashin da ya bayar da dukkanin miliyoyin kudadensa don ya sayi na kwana daya kacal saboda ya isar da wani sako, amma ina ba shi da abin da zai iya biyan Allah har ya samu wannan garabasada." Ya dan yi shiru. Kana ya dora da cewa,
"To idan ka ajiye batun numfashi a gefe guda, ka dauki GANI na ido da dukkanin hikimomin da baiwar da ke cikinsa, ka dauki JI, ka dauki JIN DANDANO na baki, ko SANSANE na hanci, ka dauki MOTSA GABOBI na jiki kamar tashi da zama da tafiya da kwanciya da sauran dukkan wadannan abubuwa, ka auna, ka gaya min idan biya ake yi duk duniyar nan wane ne zai iya juren siyen na wuni daya har ya siyaw wa wani?
"Duk tarin kudin mutum ko da shi ke da dukkan kudin duniya, ka gaya min wanda zai iya sayen ko ya taba siyen numfashin awa daya a rayuwarsa?"
Suka yi shiru, kafin attajiri ya dora da cewa, "Ba a taba yin mai kudi a duniya kamar Karuna ba, lokacin da numfashinsa ya kare ko sakan daya bai iya siya ba, don da za a yi masa lissafi zai ga bai mallaki komai da zai biya ba, shi din dai wanda ya ba shi dukiyar shi ke da numfashin. To haka ya yi ta rayuwa bai taba siyen dukkan wadancan baiwa da Allah ya yi masa ba. Ka san me Allah ke so?"
Likita ya gyada kai.
Attajiri ya ce, "Babu abin da Allah ke bukata a wurin dan'adam da zai amfane shi, hatta bauta masa da kadaita shi da Ya ce a yi, ba shi yake amfana ba face shi dan'adam din, don idan kai bawa ka yi bautar ma, kai dai ake bai wa lada, sannan a hada maka da kyakkyawan sakamakon rayuwa a ranar lahira da ta fi ta nan. Shin Likita idan dan'adam bai bauta wa Allah ba mene ne amfanin rayuwarsa?"
Likita ya ce, "Babu amfani."
"To Allah ya ba mu ikon bauta wa Allah buwayi gagara misali ka ji,"
Likita ya ce, "Amin." Cikin gamsuwa.


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...