Tuesday, January 15, 2019

TASKAR ASIRAI BOOK COVERS 2





TASKAR ASIRAN BOOK COVERS





Short Story: ADDU'AR MAKABARTA



ADDU'AR MAKABARTA

Gajeren Labari
(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Da zarar an binne mamaci kamar yadda shari'a ta tanadar, to ana bukatar kowa ya watse yana mai yi masa addu'ar samun rahama, face 'yan'uwan mamaci da za su tsaya su yi masa addu'a da tuni ga ababen shaidawa da gaskiya don tambayar kabari, sai kuma wadanda za su iya tsayawa don yi wa iyalai da 'yan'uwan mamacin addu'a.

Sunday, January 13, 2019

TALAKAWA SUN FI YIN AURE





TALAKAWA SUN FI YIN AURE
Labari
(c) Kabiru Yusuf Fagge 


An tambayi Sheikh Abu Yusufa Alfagawy cewar, "Aure a kasar Hausa yana da tsada, to amma me ya sa sau tari talakawa sun fi yin aure da yawa fiye da masu hannu da shuni. Kuma sun fi yin saki fiye da masu hannu da shuni..."
Sheikh Alfagawy ya murmushi ya ce, "Ai idan ka ji an ce an yi da yawa dole a yi sakin da yawa. To amma Alhamdulillahi, na yi farin ciki da wannan tambayar taka matuka, ba don komai ba, sai don irin wannan abu ya shafe ni sosai, kuma na sami kaina a cikinsa, wato..."
Ya fara ba da labari.

Wednesday, January 9, 2019

Gajeren Labari: SANYI NE

SANYI NE...

Gajeren Labari


(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Wani mahaukaci ya zo wucewa ta bakin Kasuwar Sabongari, kawai sai ya ji wani mai sayar da maganin gargajiya yana talla, mahaukaci ya tsaya cike da mamaki yana kallo tare da sauraron mai maganin nan kunne bude, bakin wangame a lokaci guda kuma ido tarwas.

Shi kuwa mai magani, bai san me ke gudana ba, yana ta tallansa bilhakki:

Friday, January 4, 2019

Short Story: NI MA HAKA NAKE!


NI MA HAKA NAKE!
Gajeren Labari

(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Ina isa wajen dan restaurant din na yi kici6is da wata kyakkyawa mace wadda ta sha hoda da gazal da jan baki tana yi min murmushin sace zuciya da ilahirin jiki.

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...