Tuesday, February 18, 2025

TARIHIN GASAR GUSAU INSTITUTE A TAƘAICE


 

Gasar Gusau Institute 

Daga Hassana Sulaiman Matazu

Gasar Gusau wata gasa ce da aka samar a tsakanin marubuta, ake kuma gudanar da ita duk shekara ta hanyar zaɓar mutane uku da suka fi cancanta domin ba su shaidar girmamawa da kuma ɗan abin da zai ƙara musu ƙarfin guiwa a karsashin rubutu. Bayan mutane uku akan ware mutane goma a ba su shaidar girmamawa (certificate). 


Waye Yake Ɗaukar Nauyin Gasar?

Mai girma General Aliyu Muhammad Gusau shi ne ya asasar da yin gasar tare da wasu magoya baya da suke aiki ƙarƙashin ɗakin karatunsa dake jihar Kaduna wato Gusau Institute.


Dalilin Kafa Gasar

An samar da gasar ne domin tabbatar da kawo ci gaban rubutu da marubuta ta fuskar kawo wata gasa da za ta kawo goggaya domin bayyana baiwar da kowa ne marubuci yake da ita a fagen rubutu.


Bambancin Gasar Gusau

Abubuwa da yawa sun bambanta gasar Gusau da sauran gasanni, wanda har wasu da yawa suke ganin cewar gasar Gusau ta fi ta BBC Hikayata. Domin ita gasar BBC labari ne gajere, kuma kalmomi kaɗan. Idan rabo da sa'a suka yi tasiri wanda bai taɓa cin gasa ba ma zai iya cin BBC Hikayata. Hakan ya faru sau ba adadi.

Dalilin haka ne da yawa suka yarda cewa, gasar Gusau sai jajjirtacen marubuci kuma mai bincike yayin gudanar da rubutunsa tare da tsantsar hikima ne yake iya haye matakan gasar. Kuma ba irin sauran gassanni ba ce masu ɗauke da kalmomi kaɗan da za ka je wani ya rubuta maka ka haye kamar yadda wasu suke yi.


Gwaraza da Labaran Gusau Daga 2018-2024


Shekarar 2018

Bello Hamisu Ida 1st

 SABO DA MAZA


Danladi Haruna 2nd

 ƁARAYIN ZAMANI


Nura Sada Nasimat 3rd

  INUWAR WANI


Shekarar 2019

Abdullahi Hassan Yarima 1st

 TAMANIN DA TARA


Zaharaddin Kalla 2nd

MURUCIN KAN DUTSE


Ado  Abubakar Bala 3rd

 HUSUFIN FARIN CIKI


Shekarar 2020

Jibrin Adamu Rano 1st

 DA MA SUN FAƊA MIN


Lantana Ja'afar 2nd

 ILLAR ALMAJIRANCI


Zulahat Sani Kagara 3rd

 ƊAN WAYE?

 

Shekarar 2021

Hassana Suleiman Isma'il Matazu 1st

 FITSARIN FAKO


Ibrahim Yahaya Shehu 2nd

 ƁADDABAMI


Mubarak Idris Abubakar 3rd

 RUMFAR KARA


Shekarar 2022

Bilkisu Muhammad Garkuwa 1st.

 ƘADDARAR RAYUWA


Hajara Ahmad Maidoya 2nd.

 ƊANYEN KASKO


Muttaƙa A Hasaan 3rd.

 ƊAUKAR JINKA


Shekarar 2023

Hauwa Shehu 1st

HARIN GAJIMARE


Ruƙayya Ibrahim 2nd

WATA DUNIYA


Fatima Sani 3rd

AMANATUN AMANA.


Shekarar 2024

Rufa'i Abubakar Adam 1st

MARUBUCIYA


Ummi Abba Muhammad 2nd

ABINDA KA SHUKA


Zainab Abdullahi 3rd

WASA DA RAYUWA


Jigunan Labaran 2018-2024


2018

1-Boko Haram

2-Cyber Security

3-Safara


2019

1-Jarida (Investigation)

2-

3-Gajerun Labarai


2020

1-Aljanu/Mafiya

2-Illar Almajiranci

3-Rashin Ilmi


2021

1-Garkuwa Da Mutane

2-Tsaro/Kishin ƙasa 

3-Rikicin Ƙabilanci


2022

1-Mata Maza/Zabiya

2-Mata Maza

3-Rikicin Ƙabilanci


2023

1-Cyber Security 

2-Sama Jannati

3-Fyaɗe


2024

1-Bincike/Rubutu

2-Kwaɗayi Son Zuciya

3-Matsalar Tsaro


Rubutawa Hassana Sulaiman Matazu.

Wednesday, August 28, 2024

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA


 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA


Nabila Muhammad

Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi sani da Kabiru Anka ta ciri tuta a yayin gudanar da wata 'yar ƙwarya-ƙwaryar gasa ta bajekolin al'adun Hausawa a taron.

Ƙungiyar ta zama ta farko a cikin jerin ƙungiyoyin makarantun gaba da sakandire da ta fara nuna bajinta wajen bayyana zuri'ar Bahaushe ta hanyar sanya ire-iren sutturun da Hausawan ke sanyawa da kuma alamunsu har ma da irin karin harshen da suke amfani da su.

Wasu daga cikin makarantun da suka baje hajar fasahohinsu sun haɗar da FCE da jani'ar Yusuf Maitama Sule da sauransu.

Taron ya samu halartar manyan Farfesoshi da Daktoci na makarantu daban-daban tare da masu fasahohin baka da mawaƙa irin su Aminu Ladan Abubakar Alan Waka da tarin 'yan jarida da sauransu.


An gudanar da taron a ranar 26 ga wannan wata na Agusta, 2024 a ɗakin taro na makarantar YUMSUK da ke Ƙofar Nassarawa.


Thursday, May 30, 2024

SABON ƊAN ISKA

 SABON ƊAN ISKA

Ƙarfe biyar da ‘yan mintuna na yammacin ranar Asabar na ƙaraso ƙofar gidan galar, a lokacin samari ‘yan bana-bakwai da manyan banza ‘yan bariki, haɗi da tarin ƙananan ‘yanmata masu ƙananun shekaru, jingim a wajen, wasu a tsattsaye a ƙofar gidan, wasu kuma suna shiga ciki.

Ni ma, na bi layin shiga ina kallo da nazarin al’ummar da ke wurin, musamman ƙananan ‘yanmatan da suke a matsayin karuwai. Da yawan yaran suna da siffar mutanen kirki, wasu siffofin ababen tausayi, haka nan akwai masu siffar dolaye, kai wasu ma za ka iya rantsewa idan aka saka musu hannu a baki ba za su cije ka ba, amma Alƙur’an idan ka biye musu sai su tsunduma ka a jahannama.

A haka muka ƙarasa bakin ƙofar na biya, na shiga. Yanayin cikin gidan irin na gala ne, kujeru ne da bencina a wani makaken fili sun zagaye dandamali. A cakuɗe ake maza da matan, wasu ma yaran matan a kan mazajensu suke a zazzaune suna ta shafa tare da lala iskancinsu.

Akwai DJ mai sako kiɗoɗi a gefe, ban ga ɓangaren ‘yan rawa ba sai na fuskanci a kan iya ba duk ja’irar da take so dama ta fita kan dandamali, ta cashe, ‘yan liƙi su yi mata liƙi.

Can gefe na koma, na zauna don in nazarci wurin a tsanake. Ina zama wani ƙaton farin mutum ya nufo inda nake, kafin ya iso na tuno tun a waje yake yi min kallon rashin yarda. Na haɗiyi yawu, ya ƙaraso, ya zauna dab da ni yana fuskantata har numfashinsa na karo da nawa, ya zuban jajayen na mujiyarsa.

“Sunana Uban Rabaje. Wane ne kai?” Ya tambaye ni.

“Kamar yaya?”

“Saboda ban yarda da kai ba.”

“Me ya sa?”

“Ban taɓa ganin ka a gidan nan ko sauran gidajen gala ba, sannan da ka shigo, ka dawo nan gefe ka rakuɓe, abu na uku ko irin ‘yar sigarin nan ba ka sha bare in gan ka da wata cika kuna holewa.”

“Ka sani ko ni sabon zuwa ne.”

“Ko sabon zuwan ne, ban yarda da kai ba, ka gaya min gaskiya, me ka shigo yi, kuma wane ne kai?”

“Ni sabon ɗan iska ne.”

Ya harare ni, “Kar ka yi min ƙarya, ni ɗin nan da kake gani, sunana Uban Rabaje na ƙyanƙyashe sabbin ‘yan iska sun fi dubu maitan, idan na ga sabon shiga ina ganewa.”

A lokacin aka fara shagalin galar, yaran matan ke fitowa su rinƙa bin kiɗan da waƙar da ake yi da rawar tamɓele, tare da haɗuwar jiki da samarinsu, waɗanda aka burge sukan yi liƙi, wasu kuma su yi shewa.

Sha’anin shargalle a gidan nan ba sai na siffanta a nan ba, saboda tsaro. Uban Rabaje ne ya karkato da hankalina gare shi.

“In gaya maka gaskiya, ko kai ɗan iska ne ko ɗan hisba ko soja ne ba ka isa ka yi komai ba. Duk fitar da ‘yan hisba ke yi ba sa iya zuwa nan su hana mu aikinmu ba . ‘Yansanda kai ko kwamishina bai isa ya yi kame a gidan nan ba.”

“Saboda me?” Na tambaye shi.

Ya harare ni, “Kar ka raina min waye, na tambaye ka wane ne kai ba ka ba ni amsa ba, kana tambaya ta.”

“Ai na gaya maka, ni sabon  ɗan iska ne.”

Ya ƙara matso ni, yana huci kamar a cikin hancina, ya ƙwalolo min idanu har sai da na ji dam.

“Wane ne kai na ce?”

“Ni marubuci ne.”

“Me ya kawo ka?”

“Harkar rubutu, yadda kuke haɗa ƙananan ‘yanmata da samari kuna casu ba tare da Hisba ko hukuma ta hana ku ba, shi ya sa na ga ina da abin rubutawa da zan yaɗa wa duniya ta karanta.”

“Da kyau, tun da a iya rubutu ka tsaya. Ka ji dai na gaya maka hisba ko ‘yansada ma ba za su iya yi mana komai ba bare rubutunka da a yanzu mutane ma ba karantawa suke yi ba, in ma sun karanta a matsayin tatsuniya za su ɗauka.”

Kallon shi kawai nake yi.

“Kai yanzu har sai ka shigo ka ga ƙwaƙwaf?”

“E mana, ta haka zan rubuta zahiri.”

“To in haka ne, zan iya taimaka maka?”

“Da me?”

“Zan iya haɗa ka da wata sokuwar ƙaramar yarinya wadda tun a nan za ta iya saka kuka.”

“Saboda daɗi ko wuya?”

“Saboda da daɗi mana, yadda za ka ji daɗin yin rubutun.”

Na girgiza kai, “a’a.”

“To a yi maka shokin mana.”

“A’a.”

“Anya kana son rubutu yadda harkar take sosai kuwa?”

“E mana, ai a haka ma zan yi ginin da tunani irin namu na marubuta yadda za a karanta abin kamar yadda yake.”

Ya girgiza kai, “Ba ka isa ba, dole sai  ka yi a zahiri, ai na san darajar rubutu ni ma.”

Ya tashi, ya nufi can wani ɓangare na gidan, ina hango shi ya tattaro wasu yara ‘yanmata masu siffar ƙwallaye sa ƙartai kuka, ya nufo inda nake, suna zuwa ya tarar ba na nan yana ta dube-dube, ina can ɓoye ƙarƙashin wani tebur ina hango shi.

Yana juya baya na nufi bakin ƙofar fita ya hango ni, “Kai marubuci ina kuma za ka je?”

Na ɗaga masa hannu, “Ina dawowa,” na fice. Kuma fa zan koma, amma neman labari.

Rubutawa: Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Tuesday, May 21, 2024

BAYAN TA FASHE

 *BAYAN TA FASHE*

(gajeren labari)


Ɗanbashir na tsaye shi da Jummala suna zance, mahaifin Jummalar mai suna Malam Iliya ya ƙaraso, yana kallonsu.

“Ke Jummala na san ba ki gaya masa saƙona ba, shi ya sa na zo da kaina.”

Cikin saddar da kai Jummala ta ce, “Yanzu zan gaya masa Baba...”

Ya dakatar da ita, “Ai tun da na zo an gama.” Ya karkata ga Ɗanbashir, “Kai ya maganar da muka yi game da tsayar da ranar ɗaurin aure, mun gaji da ganinta a gida, kuma kai, ka ƙi ka turo mu tsayar da ranar.”

Cikin ladabi Ɗanbashir ya amsa da cewa, “E wallahi Baba, na gaya mata ina jiran mining ɗin da nake yi ta fashe ne zuwa ƙarshen watan nan sai in ƙarasa  kayan lefen da ginina sai a ɗaura auren.”

Malam Iliya ya sauya masa kallo, “Abin ya zo, in ji mijin karuwa, ashe kai ma kana cikin ire-iren mahaukatan yaran da ake yayi a wannan zamani, masu hauka da tunanin suna neman kuɗi.”

“Baba ba hauka ba ne, nema ne..”

“Nema wanne iri? Kai ban da ka samu taɓuwar ƙwaƙwalwa kawai don kana daddana tare da shasshafa fuskar waya sai a ɗauki kuɗi a ba ka, ba tare da aikin fari ba?”

“Baba wannan daddanawar da shasshafawar su ne aikin.”

“Aiki? A garin gaɓa-gaɓa ko?”

“A’a a duniyar cigaba da masu hankali.”

“Wai ta yaya?”

“Yauwa Baba kamar dai yadda kake zuwa aiki kasuwar Singa, ka sauke kaya, ke jera, ka yi lissafi, ka bayar da yamma a biya ka, haka muke yin namu aikin a ƙarshe a biya mu.”

“Kai, kar ka raina min hankali mana. Ni da nake biyan kudin mota, na je kasuwar, na ɗauki kayan a wuyana ko a kaina, in sauke in shigar a shago, ina gumi, shi ne za ka haɗa ni da kai mai halin ci-ma-zaune?”

“Baba zamani ne ya zo da yanayin haɗa sana’o’i kamar biyu zuwa uku, ka san ni tela ne, nake haɗawa da mining ɗin kuma aiki nake kamar yadda kake yi sai dai a zamanance.”

“Kai ɗan zamani saurara, na daɗe a duniyar nan kafin kai, kuma ga ni a zamanin bare ka layance min, don haka daga yau ba kai ba Jummala, ba zan miƙa ta ga mai matacciyar zuciya ba,” Ya kalli Jummala wacce ke tsaye cikin damuwa, ya daka mata tsawa, “Wuce gida, kin yi min ƙuri kamar tsohuwar mayya.”

Jummala ta nufi gida tana kuka. Ɗanbashir ya marairaice, “Don Allah Baba kar ka raba ni da Jummala, wallahi ina son ta, tana fashewa zan...”

Ya kuza masa tsawa, “Ɓace min da gani kar in yi buju-buju da kai, ka je can ta fashe maka.”

Cikin damuwa Ɗanbashir ya tafi kamar zai yi kuka.

Kwanaki tara tsakani aka ɗaura auren Jummale da wani Ɗankarota. Dole Ɗanbashir ya haƙura, kuma kuɗin da yake tsammanin zuwansu na mining ba su zo ba a ƙarshen watan, sai bayan kwanaki ashirin da shida, inda ya sami manyan kuɗaɗen da shi kansa bai zata ba.

Da yake ya tsara, sai ya kammala ginin gidansa, sannan ya ƙara jari a sana’arsa ta ɗinki inda ya haɗa har da buɗe sabon shagon sayar da atamfofi da lesuna, kuma ya sayi sabuwar mota.

A lokacin kyawawan ‘yanmata da suka ninka Jummala kyau sau ɗari da goma sha uku suka rinƙa tururuwa gare shi, suna son shi da aure.

Sai da ya zaɓa, ya sami mai son shi don Allah ya darje, wata yarinya mai suna Zahra, ya aura.


-Kabiru Yusuf Fagge (anka)

2024

Wednesday, November 8, 2023

KAWALCI A ƘASAR HAUSA

 


KAWALCI A ƘASAR HAUSA

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Kawalci yana ɗaya daga cikin munana ɗabi’u da suka zama ruwan dare ba kawai a ƙasar Hausa ba har ma a duniya bakiɗaya.

Kawalci shi ne ɗabi’ar haɗa namiji da mace ko namiji da namiji ko ma mace da mace don su yi aikin assha, inda yawanci mai haɗawar wato “Kawali” yakan sami wani abin masarufi.

A taƙaice za a iya kasa kawalci zuwa manyan kaso guda uku da suka haɗa da:

(1) Kawalcin Mata

Shi wannan nau’i na kawalci wasu mutane ne da suka ɗauki wannan ɗabi’a a matsayin hanyar neman abin masarufi suke nama wa wasu mutane mata suna kai musu da niyyar a aikata lalata, su kuma a biya su.

Suna gudanar da wannan ɗabi’a ne ta hanyar yarjejeniya ko kuma yanke farashi. Ma’ana tun kafin su kawo wa mutum mace sai an ƙayyade abin da za a biya su. Su waɗannan mutane suna nema wa mutum duk irin macen da yake so, sannan kuma kowacce mace tana da farashi, ya danganta da ƙirarta.

 

(2) Kawalcin Maza

Nau’i na biyu wanda ya fi kowanne muni shi ne masu yin sa sun mayar da hankali ne a kan nema wa mutane maza maimakon mata.

Su kawalan maza su ma mutane lalatattu, wasu ma suna aikata irin wannan lalatar da maza, sukan yi haka ne ta hanyar yaudarar mutane da wasu abubuwa. Sukan samu yara masu kwaɗayi su rinƙa ba su abubuwa na jin daɗin rayuwa da yi musu alƙawari na cewa za su saya musu mota ko babur ko kuma su ce za a kai su aikin Hajji idan suka amince aka aikata lalata da su.

Abin takaici a yanzu wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a cikin al’ummar Hausawa da ma duniya bakiɗaya.

 

(3) Kawalcin Mata Da Maza

Wannan nau’i na kawalci ya fi sauran nau’o’in shahara da ɗaukaka. Masu aikata wannan ɗabi’a sukan nemawa mata ko maza waɗanda za a yi aikin assha da su.

Zaurancen Kawalai

Kawalai suna da zaurance na musamman da suke amfani da su a lokacin da su a lokacin da suke aiwatar  da wannan ɗabi’ar. Misali a lokacin da suke zaune a majalisarsu ko dandali duk mutumin da ya tunkaro su, idan suka ga ya yi kama da irin mutanen da suke hulɗa da su, bayan sun gama gaisawa abu na farko da za su ce masa shi ne.

“Alhaji me ake buƙata, kaza ko zakara?”

Shi kuwa idan abin da ya kawo shi kenan, sai ya zaɓa ya ce; “Kaza” ko ya ce, “Zakara”

A zaurancen nasu abin da wai suke nufi da “kaza” shi ne “mace” haka kuma abin da suke nufi da “zakara” shi ne “namiji.”

A mafi yawancin lokuta kawalai suna gane abokan harkar su wato waɗanda za a nema a kai wa mutane ta hanyar wasu alamomi.

A ƙasashen da suka ci gaba kuwa sukan gane mata lalatattu ta hanyar saka wata irin sarƙa a ƙafarsu ta hagu ko ta dama, ko kuma yin wani ƙunshi na musamman a ƙafafuwansu ko kuma saka zobe a yatsan ƙafa.

Haka kuma sukan gane maza ta hanyar yin wani irin aski ko kuma gyaran gashi na musamman. Ta haka ne su kawalan suna ganin su ko da kuwa ba su taɓa ganin su ba, za su gane su, ta irin waɗannan alamomi.

Waɗannan alamomi sun yi nisa da zuwa ƙasar Hausa da kewayenta.

Ba kowa ake yi wa kawalci ba, sai wasu keɓaɓɓun mutane waɗanda ba sa so a gan su suna aikata irin wannan ɗabiu’ar. Snanan kuma yawanci shugabanni ne a cikin al’umma, akan haka ne suke neman waɗanda za su riƙa yi musu kawalci, suna biyan su.

Waɗansu daga cikin waɗanda ake yi wa kawalci akwai attajirai da masu mulki da kuma wasu manyan mutane.

A mafi yawan lokaci kuwa su ne suke riƙe da ragamar tafiyar da jagoranci na al’umma.

(A sani: Akwai wasu alamomi da alamtattuka da na ɓoye don kar su zama abin koyi ga gurɓatattu)

Alƙalancin Gasar Rubutu

 Alƙalancin Gasar Rubutu Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkay...