Thursday, May 30, 2024

SABON ƊAN ISKA

 SABON ƊAN ISKA

Ƙarfe biyar da ‘yan mintuna na yammacin ranar Asabar na ƙaraso ƙofar gidan galar, a lokacin samari ‘yan bana-bakwai da manyan banza ‘yan bariki, haɗi da tarin ƙananan ‘yanmata masu ƙananun shekaru, jingim a wajen, wasu a tsattsaye a ƙofar gidan, wasu kuma suna shiga ciki.

Ni ma, na bi layin shiga ina kallo da nazarin al’ummar da ke wurin, musamman ƙananan ‘yanmatan da suke a matsayin karuwai. Da yawan yaran suna da siffar mutanen kirki, wasu siffofin ababen tausayi, haka nan akwai masu siffar dolaye, kai wasu ma za ka iya rantsewa idan aka saka musu hannu a baki ba za su cije ka ba, amma Alƙur’an idan ka biye musu sai su tsunduma ka a jahannama.

A haka muka ƙarasa bakin ƙofar na biya, na shiga. Yanayin cikin gidan irin na gala ne, kujeru ne da bencina a wani makaken fili sun zagaye dandamali. A cakuɗe ake maza da matan, wasu ma yaran matan a kan mazajensu suke a zazzaune suna ta shafa tare da lala iskancinsu.

Akwai DJ mai sako kiɗoɗi a gefe, ban ga ɓangaren ‘yan rawa ba sai na fuskanci a kan iya ba duk ja’irar da take so dama ta fita kan dandamali, ta cashe, ‘yan liƙi su yi mata liƙi.

Can gefe na koma, na zauna don in nazarci wurin a tsanake. Ina zama wani ƙaton farin mutum ya nufo inda nake, kafin ya iso na tuno tun a waje yake yi min kallon rashin yarda. Na haɗiyi yawu, ya ƙaraso, ya zauna dab da ni yana fuskantata har numfashinsa na karo da nawa, ya zuban jajayen na mujiyarsa.

“Sunana Uban Rabaje. Wane ne kai?” Ya tambaye ni.

“Kamar yaya?”

“Saboda ban yarda da kai ba.”

“Me ya sa?”

“Ban taɓa ganin ka a gidan nan ko sauran gidajen gala ba, sannan da ka shigo, ka dawo nan gefe ka rakuɓe, abu na uku ko irin ‘yar sigarin nan ba ka sha bare in gan ka da wata cika kuna holewa.”

“Ka sani ko ni sabon zuwa ne.”

“Ko sabon zuwan ne, ban yarda da kai ba, ka gaya min gaskiya, me ka shigo yi, kuma wane ne kai?”

“Ni sabon ɗan iska ne.”

Ya harare ni, “Kar ka yi min ƙarya, ni ɗin nan da kake gani, sunana Uban Rabaje na ƙyanƙyashe sabbin ‘yan iska sun fi dubu maitan, idan na ga sabon shiga ina ganewa.”

A lokacin aka fara shagalin galar, yaran matan ke fitowa su rinƙa bin kiɗan da waƙar da ake yi da rawar tamɓele, tare da haɗuwar jiki da samarinsu, waɗanda aka burge sukan yi liƙi, wasu kuma su yi shewa.

Sha’anin shargalle a gidan nan ba sai na siffanta a nan ba, saboda tsaro. Uban Rabaje ne ya karkato da hankalina gare shi.

“In gaya maka gaskiya, ko kai ɗan iska ne ko ɗan hisba ko soja ne ba ka isa ka yi komai ba. Duk fitar da ‘yan hisba ke yi ba sa iya zuwa nan su hana mu aikinmu ba . ‘Yansanda kai ko kwamishina bai isa ya yi kame a gidan nan ba.”

“Saboda me?” Na tambaye shi.

Ya harare ni, “Kar ka raina min waye, na tambaye ka wane ne kai ba ka ba ni amsa ba, kana tambaya ta.”

“Ai na gaya maka, ni sabon  ɗan iska ne.”

Ya ƙara matso ni, yana huci kamar a cikin hancina, ya ƙwalolo min idanu har sai da na ji dam.

“Wane ne kai na ce?”

“Ni marubuci ne.”

“Me ya kawo ka?”

“Harkar rubutu, yadda kuke haɗa ƙananan ‘yanmata da samari kuna casu ba tare da Hisba ko hukuma ta hana ku ba, shi ya sa na ga ina da abin rubutawa da zan yaɗa wa duniya ta karanta.”

“Da kyau, tun da a iya rubutu ka tsaya. Ka ji dai na gaya maka hisba ko ‘yansada ma ba za su iya yi mana komai ba bare rubutunka da a yanzu mutane ma ba karantawa suke yi ba, in ma sun karanta a matsayin tatsuniya za su ɗauka.”

Kallon shi kawai nake yi.

“Kai yanzu har sai ka shigo ka ga ƙwaƙwaf?”

“E mana, ta haka zan rubuta zahiri.”

“To in haka ne, zan iya taimaka maka?”

“Da me?”

“Zan iya haɗa ka da wata sokuwar ƙaramar yarinya wadda tun a nan za ta iya saka kuka.”

“Saboda daɗi ko wuya?”

“Saboda da daɗi mana, yadda za ka ji daɗin yin rubutun.”

Na girgiza kai, “a’a.”

“To a yi maka shokin mana.”

“A’a.”

“Anya kana son rubutu yadda harkar take sosai kuwa?”

“E mana, ai a haka ma zan yi ginin da tunani irin namu na marubuta yadda za a karanta abin kamar yadda yake.”

Ya girgiza kai, “Ba ka isa ba, dole sai  ka yi a zahiri, ai na san darajar rubutu ni ma.”

Ya tashi, ya nufi can wani ɓangare na gidan, ina hango shi ya tattaro wasu yara ‘yanmata masu siffar ƙwallaye sa ƙartai kuka, ya nufo inda nake, suna zuwa ya tarar ba na nan yana ta dube-dube, ina can ɓoye ƙarƙashin wani tebur ina hango shi.

Yana juya baya na nufi bakin ƙofar fita ya hango ni, “Kai marubuci ina kuma za ka je?”

Na ɗaga masa hannu, “Ina dawowa,” na fice. Kuma fa zan koma, amma neman labari.

Rubutawa: Kabiru Yusuf Fagge (anka)

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...