Tuesday, May 21, 2024

BAYAN TA FASHE

 *BAYAN TA FASHE*

(gajeren labari)


Ɗanbashir na tsaye shi da Jummala suna zance, mahaifin Jummalar mai suna Malam Iliya ya ƙaraso, yana kallonsu.

“Ke Jummala na san ba ki gaya masa saƙona ba, shi ya sa na zo da kaina.”

Cikin saddar da kai Jummala ta ce, “Yanzu zan gaya masa Baba...”

Ya dakatar da ita, “Ai tun da na zo an gama.” Ya karkata ga Ɗanbashir, “Kai ya maganar da muka yi game da tsayar da ranar ɗaurin aure, mun gaji da ganinta a gida, kuma kai, ka ƙi ka turo mu tsayar da ranar.”

Cikin ladabi Ɗanbashir ya amsa da cewa, “E wallahi Baba, na gaya mata ina jiran mining ɗin da nake yi ta fashe ne zuwa ƙarshen watan nan sai in ƙarasa  kayan lefen da ginina sai a ɗaura auren.”

Malam Iliya ya sauya masa kallo, “Abin ya zo, in ji mijin karuwa, ashe kai ma kana cikin ire-iren mahaukatan yaran da ake yayi a wannan zamani, masu hauka da tunanin suna neman kuɗi.”

“Baba ba hauka ba ne, nema ne..”

“Nema wanne iri? Kai ban da ka samu taɓuwar ƙwaƙwalwa kawai don kana daddana tare da shasshafa fuskar waya sai a ɗauki kuɗi a ba ka, ba tare da aikin fari ba?”

“Baba wannan daddanawar da shasshafawar su ne aikin.”

“Aiki? A garin gaɓa-gaɓa ko?”

“A’a a duniyar cigaba da masu hankali.”

“Wai ta yaya?”

“Yauwa Baba kamar dai yadda kake zuwa aiki kasuwar Singa, ka sauke kaya, ke jera, ka yi lissafi, ka bayar da yamma a biya ka, haka muke yin namu aikin a ƙarshe a biya mu.”

“Kai, kar ka raina min hankali mana. Ni da nake biyan kudin mota, na je kasuwar, na ɗauki kayan a wuyana ko a kaina, in sauke in shigar a shago, ina gumi, shi ne za ka haɗa ni da kai mai halin ci-ma-zaune?”

“Baba zamani ne ya zo da yanayin haɗa sana’o’i kamar biyu zuwa uku, ka san ni tela ne, nake haɗawa da mining ɗin kuma aiki nake kamar yadda kake yi sai dai a zamanance.”

“Kai ɗan zamani saurara, na daɗe a duniyar nan kafin kai, kuma ga ni a zamanin bare ka layance min, don haka daga yau ba kai ba Jummala, ba zan miƙa ta ga mai matacciyar zuciya ba,” Ya kalli Jummala wacce ke tsaye cikin damuwa, ya daka mata tsawa, “Wuce gida, kin yi min ƙuri kamar tsohuwar mayya.”

Jummala ta nufi gida tana kuka. Ɗanbashir ya marairaice, “Don Allah Baba kar ka raba ni da Jummala, wallahi ina son ta, tana fashewa zan...”

Ya kuza masa tsawa, “Ɓace min da gani kar in yi buju-buju da kai, ka je can ta fashe maka.”

Cikin damuwa Ɗanbashir ya tafi kamar zai yi kuka.

Kwanaki tara tsakani aka ɗaura auren Jummale da wani Ɗankarota. Dole Ɗanbashir ya haƙura, kuma kuɗin da yake tsammanin zuwansu na mining ba su zo ba a ƙarshen watan, sai bayan kwanaki ashirin da shida, inda ya sami manyan kuɗaɗen da shi kansa bai zata ba.

Da yake ya tsara, sai ya kammala ginin gidansa, sannan ya ƙara jari a sana’arsa ta ɗinki inda ya haɗa har da buɗe sabon shagon sayar da atamfofi da lesuna, kuma ya sayi sabuwar mota.

A lokacin kyawawan ‘yanmata da suka ninka Jummala kyau sau ɗari da goma sha uku suka rinƙa tururuwa gare shi, suna son shi da aure.

Sai da ya zaɓa, ya sami mai son shi don Allah ya darje, wata yarinya mai suna Zahra, ya aura.


-Kabiru Yusuf Fagge (anka)

2024

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...