Wednesday, November 8, 2023

KAWALCI A ƘASAR HAUSA

 


KAWALCI A ƘASAR HAUSA

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Kawalci yana ɗaya daga cikin munana ɗabi’u da suka zama ruwan dare ba kawai a ƙasar Hausa ba har ma a duniya bakiɗaya.

Kawalci shi ne ɗabi’ar haɗa namiji da mace ko namiji da namiji ko ma mace da mace don su yi aikin assha, inda yawanci mai haɗawar wato “Kawali” yakan sami wani abin masarufi.

A taƙaice za a iya kasa kawalci zuwa manyan kaso guda uku da suka haɗa da:

(1) Kawalcin Mata

Shi wannan nau’i na kawalci wasu mutane ne da suka ɗauki wannan ɗabi’a a matsayin hanyar neman abin masarufi suke nama wa wasu mutane mata suna kai musu da niyyar a aikata lalata, su kuma a biya su.

Suna gudanar da wannan ɗabi’a ne ta hanyar yarjejeniya ko kuma yanke farashi. Ma’ana tun kafin su kawo wa mutum mace sai an ƙayyade abin da za a biya su. Su waɗannan mutane suna nema wa mutum duk irin macen da yake so, sannan kuma kowacce mace tana da farashi, ya danganta da ƙirarta.

 

(2) Kawalcin Maza

Nau’i na biyu wanda ya fi kowanne muni shi ne masu yin sa sun mayar da hankali ne a kan nema wa mutane maza maimakon mata.

Su kawalan maza su ma mutane lalatattu, wasu ma suna aikata irin wannan lalatar da maza, sukan yi haka ne ta hanyar yaudarar mutane da wasu abubuwa. Sukan samu yara masu kwaɗayi su rinƙa ba su abubuwa na jin daɗin rayuwa da yi musu alƙawari na cewa za su saya musu mota ko babur ko kuma su ce za a kai su aikin Hajji idan suka amince aka aikata lalata da su.

Abin takaici a yanzu wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a cikin al’ummar Hausawa da ma duniya bakiɗaya.

 

(3) Kawalcin Mata Da Maza

Wannan nau’i na kawalci ya fi sauran nau’o’in shahara da ɗaukaka. Masu aikata wannan ɗabi’a sukan nemawa mata ko maza waɗanda za a yi aikin assha da su.

Zaurancen Kawalai

Kawalai suna da zaurance na musamman da suke amfani da su a lokacin da su a lokacin da suke aiwatar  da wannan ɗabi’ar. Misali a lokacin da suke zaune a majalisarsu ko dandali duk mutumin da ya tunkaro su, idan suka ga ya yi kama da irin mutanen da suke hulɗa da su, bayan sun gama gaisawa abu na farko da za su ce masa shi ne.

“Alhaji me ake buƙata, kaza ko zakara?”

Shi kuwa idan abin da ya kawo shi kenan, sai ya zaɓa ya ce; “Kaza” ko ya ce, “Zakara”

A zaurancen nasu abin da wai suke nufi da “kaza” shi ne “mace” haka kuma abin da suke nufi da “zakara” shi ne “namiji.”

A mafi yawancin lokuta kawalai suna gane abokan harkar su wato waɗanda za a nema a kai wa mutane ta hanyar wasu alamomi.

A ƙasashen da suka ci gaba kuwa sukan gane mata lalatattu ta hanyar saka wata irin sarƙa a ƙafarsu ta hagu ko ta dama, ko kuma yin wani ƙunshi na musamman a ƙafafuwansu ko kuma saka zobe a yatsan ƙafa.

Haka kuma sukan gane maza ta hanyar yin wani irin aski ko kuma gyaran gashi na musamman. Ta haka ne su kawalan suna ganin su ko da kuwa ba su taɓa ganin su ba, za su gane su, ta irin waɗannan alamomi.

Waɗannan alamomi sun yi nisa da zuwa ƙasar Hausa da kewayenta.

Ba kowa ake yi wa kawalci ba, sai wasu keɓaɓɓun mutane waɗanda ba sa so a gan su suna aikata irin wannan ɗabiu’ar. Snanan kuma yawanci shugabanni ne a cikin al’umma, akan haka ne suke neman waɗanda za su riƙa yi musu kawalci, suna biyan su.

Waɗansu daga cikin waɗanda ake yi wa kawalci akwai attajirai da masu mulki da kuma wasu manyan mutane.

A mafi yawan lokaci kuwa su ne suke riƙe da ragamar tafiyar da jagoranci na al’umma.

(A sani: Akwai wasu alamomi da alamtattuka da na ɓoye don kar su zama abin koyi ga gurɓatattu)

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...