Friday, April 7, 2023

Wednesday, February 15, 2023

TASIRIN GASAR ‘MUN GANI A KASA’ GA SIYASA DA RUBUTU






TASIRIN GASAR ‘MUN GANI A KASA’ GA SIYASA DA RUBUTU

Ranar Juma’a 10-2-2023 jagororin gasar ‘MUN GANI A KASA’ karkashin jagoranci Engr. Surajo Yazid Abukur da Abdulrahman Aliyu da Yazid Nasudan suka bayar da kyaututtuka ga zakarun da suka lashe kyautar ‘Mun Gani A Kasa’ na rukuni ukun

(1) Gajerun Labarai

(2) Rubutacciyar Waka da

(3) Kowa Ya Bi ‘Challenge”.

Manufar gasar shi ne bayyana tasirin zabar shugaba nagari. Yadda mawallafan suka barje guminsu wajen zakulo dukkanin wasu hanyoyi da tsari na zabar shugaban da ya fi cancanta.

Gasar tana da tasiri kuma za ta ci gaba da tasiri ga siyasa da ‘yan siyasa har ma da marubuta, domin ta zamo wani ma’auni da ya kamata al’umma su bi domin zabar shugabanni.

A cikin littafin da aka samar mai suna Mizani da kuma bidiyo na zakarun gasar za a karanta tare da ganin duk wasu hanyoyi da ya kamata al’umma su bi kafin zabe da lokacin yin zabe.

An dasa wani danba wadda a nan gaba ‘yan siyasa za su rinka amfani da hanyoyin. Sannan an fito da tasirin rubutu da marubuta ga shugabanni da ‘yan siyasa.

An yi taron a birnin Katsina.

Allah ya ba mu ikon zabar shugabanni nagari, amin.

Kabiru Yusuf


 

Wednesday, January 25, 2023

'YAR NAJERIYA COVER - Sumayya Abdulkadir


 

'YAR SAKI BOOK COVER


 

KALAR KYAMARA CE

KALAR KYAMARA CE

Kabiru Yusuf Fagge

Alhaji Adamu, mahaifin Habule ya kira shi.

“Na kira ka ne don in sanar da kai na yi maka zabin mata. Na zaba maka Nafisa, ‘yar Alhaji Mukhtar, ka je ku gana.”

Habule ya girgiza kai.

“Gaskiya Dad ka yi shigar sauri. Ina da wadda nake so zan aura.”

“Wace ce wannan?”

“Zizi, ‘yar gidan Hon. Bala Gunduma.”

Alhaji Adamu ya girgiza kai.

“Haba Habule, ai kuwa Nafisa ta fi Zizi hankali da addini…”

Habule ya yi dariya.

“Dad ke nan! Dad ai Zizi ta fi Nafisa komai.”

“Me da me ta fi ta?”

“Good, Dad! Da farko Zizi kyakkyawa ce, ‘yar gayu, kalar gaban mota, kuma kalar kyamara.”

“Yaro dai yaro ne, wane ne ya gaya maka yanzu ana bibiyar wata mace kalar kyamara ko gaban mota, ai kalar hankali da addini ake bi.”

“Dad, ka yi hakuri, ni dai gaskiya kalar kyamara nake so.”

“Habule, ina nuna maka gefen wuka, kana kara kai hannu. Yanzu wadannan ‘yanmatan da kake kira da kalar kyamara, ku suke mayarwa ababen daukar hoto, ka ganka kamar wayayye, amma su mayar da kai gaula a gaban kyamara, ka saki baki su yi ta daukar ka.”

“Dad, ni wayayye ne dan birni, dole ina bukatar macen da zan keta a bi ni da kallo, wacce idan na sa ta a gaban lens za ta dauki ido. Amma na ga kamar ba za ka gane ba.”

“Shi ke nan, Allah ya kai mu lokacin da za mu gane wane ne bai gane din ba.”

*

Wata biyu da yin auren Habule da Zizi, Habule ya fahinci duk wani kyalkyal da sheki da Zizi ke yi ashe maya-mayai ne da hodoji, ya fuskanci duk harkar danfare (packaging) ce. Ba ma wannan ba ne ya fi damun shi ba, yadda ta zama ba ta da lokacinsa. Bugu da kari duk ta tsittsince masa ‘yan kudadensa, ta ja jarin kanta, ta fi shi muwalatin harkoki.

A yanzu kam sai dai ya hango ta a a social media. Haka take rangwada make-up ta yi radau da ita, ta dauki hotuna ta watsa, ana ta yi mata comments da liking.

Da abin ya ishe shi, ya je, ya sami mahaifinsa cikin damuwa. Yana magana da alamun jin kunya.

“Dad ya batun Nafisa?”

Alhaji Adamu ya sa halin da yake ciki, har zai yi dariya sai ya basar.

“Me kake nufi da batun Nafisa?”

“Ina nufin a nemar min aurenta.”

Yanzu dariya ta kwacewa Alhaji Adamu.

“Nafisa tana dakin mijinta cikin kwanciyar hankali. Ina matar taka?”

“Gaskiya Dad ba zan boye maka ba, wannan yarinya ba kala ta ba ce.”

“Don me, yarinya kalar kyamara, ka ce min ba kalar ka ba ce?”

“Lokaci da nake fadar haka ba na yin hangen nesa, amma yanzu ina tafe da hangenka Dad.”

“Ai kuwa Zizi kalar kyamara ce.”

Ya tsokane shi.

“Ni ma na san kalar kyamara ce Dad. Amma ba kala ta ba ce. A yi hakuri.”

Alhaji Adamu ya kyalkyale da dariya.

“Ai kuwa Zizi kalar kyamara ce.”

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Sunday, November 27, 2022

RAMA CUTA..

 RAMA CUTA GA MACUCI BA LAIFI NE BA


Amma gane wanzami,

Mai bidar mai jarfa,

Rama alkhairi ga mai cuta ba illa ne ba,

Alan Waka.


Kar ka ruda rudadde,

Kar ka murda murdadde,

Rama cuta ga macuci ba illa ne ba,

Alan Waka.


Hakuri yana da maauni ba za ka dauki raini ba,

Hakuri yana da misali ba za ka dauki wasa ba,

Hakuri yana da suriri ba za ka dauki zambo ba,

Ba ka zo da cuta ba ba hali na zambo ba,

Ba da tsigunagun ba,

Rama cuta ga macucinka ba illa ne ba.


Kar ka juya juyayye,

Kar ka rikita rikitacce,

Maida alkairi a kan sharri ba tsoro ne ba.


Mun zamo madubin duban alumma na ci gaba,

Mun zamo fitulun da ke hasken binne su ba wai ba,

Mun zamo abin shaawar a gani a ji ba fahar ne ba,

Kar ka fara yin zamba,

Kar mu koyi yin zamba,

Ba batu na tsoro ba,

Mu ake duba da alkairi ba masu sharri ba.


Sara da sassaka ba zai hana gamji tofo ba,

Kainuwa dashen Allah ba shukawar mutane ba,

Tsiron da Allah ke so zai tsiro ba da lura ba,

Ba da kai ruwa gun ba,

Rabbi kai na sa gaba,

Ban nufi ga cuta ba,

Sama sassauci ga mai cuta ta ba tsoro ba.


Kar ka zagi zagagge,

Kar ka doki jemamme,

Kau da zambo ga mazambaci ba kasawa ba.


Hakuri yana da faraga da ba ai wa kaidi ba,

Hakuri yakan dafa dutse ya sha ba za ya kosa ba,

Hakuri yana saka bawa ya hau abokanan gaba,

Ba a ma yi komai ba,

Ba ka ma ga komai ba,

Ba ka riski komai ba,

Maida alkairi ga mai sharri ba illa ne ba.


Ba zai zo da gwalli ba,

Shi ba jahilci ba kauna ce,

Ba ja-in-ja ai ba,

Ku ne madubin dubawa ai rayuwa baba,

Ba a fara komai ba,

Ba ka riski komai ba,

Ku zo mu yo tuba,

Yanzu anka sa kamba,

Taimako da idanunka ka kauna bai ma ba.


Godiya nake a gurin Allah da ba za ta kirgu ba,

Da ya ba ni abokanan hulda ba yan taadda ba,

Ba yan izan wuta ba yan hikima ba yan baranda ba,

Fantimoti ag gaba,

Da Maryam A. Baba,

Ga Murja Yar Baba,

Da Fasihiya Fati Nijar mai hali babba.


An ciro wannan waka a littafin DIWANIN WAKOKIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA) Na Salisu Ahmad Yakasai da Abu-Ubaida Sani

Alƙalancin Gasar Rubutu

 Alƙalancin Gasar Rubutu Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkay...