TASIRIN
GASAR ‘MUN GANI A KASA’ GA SIYASA DA RUBUTU
Ranar
Juma’a 10-2-2023 jagororin gasar ‘MUN GANI A KASA’ karkashin jagoranci Engr. Surajo Yazid Abukur da
Abdulrahman Aliyu da Yazid Nasudan suka bayar da kyaututtuka ga zakarun da suka lashe
kyautar ‘Mun Gani A Kasa’ na rukuni ukun
(1)
Gajerun Labarai
(2)
Rubutacciyar Waka da
(3)
Kowa Ya Bi ‘Challenge”.
Manufar gasar shi ne bayyana
tasirin zabar shugaba nagari. Yadda mawallafan suka barje guminsu wajen zakulo
dukkanin wasu hanyoyi da tsari na zabar shugaban da ya fi cancanta.
Gasar tana da tasiri kuma za
ta ci gaba da tasiri ga siyasa da ‘yan siyasa har ma da marubuta, domin ta zamo
wani ma’auni da ya kamata al’umma su bi domin zabar shugabanni.
A cikin littafin da aka samar
mai suna Mizani da kuma bidiyo na zakarun gasar za a karanta tare da ganin duk
wasu hanyoyi da ya kamata al’umma su bi kafin zabe da lokacin yin zabe.
An dasa wani danba wadda a nan
gaba ‘yan siyasa za su rinka amfani da hanyoyin. Sannan an fito da tasirin
rubutu da marubuta ga shugabanni da ‘yan siyasa.
An yi taron a birnin Katsina.
Allah ya ba mu ikon zabar
shugabanni nagari, amin.
Kabiru Yusuf
No comments:
Post a Comment