KALAR KYAMARA CE
Kabiru Yusuf Fagge
Alhaji
Adamu, mahaifin Habule ya kira shi.
“Na
kira ka ne don in sanar da kai na yi maka zabin mata. Na zaba maka Nafisa, ‘yar Alhaji Mukhtar, ka je ku gana.”
Habule
ya girgiza kai.
“Gaskiya Dad ka yi shigar
sauri. Ina da wadda nake so zan aura.”
“Wace ce wannan?”
“Zizi, ‘yar gidan Hon. Bala
Gunduma.”
Alhaji Adamu ya girgiza kai.
“Haba Habule, ai kuwa Nafisa
ta fi Zizi hankali da addini…”
Habule ya yi dariya.
“Dad ke nan! Dad ai Zizi ta
fi Nafisa komai.”
“Me da me ta fi ta?”
“Good, Dad! Da farko Zizi
kyakkyawa ce, ‘yar gayu, kalar gaban mota, kuma kalar kyamara.”
“Yaro dai yaro ne, wane ne ya
gaya maka yanzu ana bibiyar wata mace kalar kyamara ko gaban mota, ai kalar
hankali da addini ake bi.”
“Dad, ka yi hakuri, ni dai
gaskiya kalar kyamara nake so.”
“Habule, ina nuna maka gefen
wuka, kana kara kai hannu. Yanzu wadannan ‘yanmatan da kake kira da kalar
kyamara, ku suke mayarwa ababen daukar hoto, ka ganka kamar wayayye, amma su
mayar da kai gaula a gaban kyamara, ka saki baki su yi ta daukar ka.”
“Dad, ni wayayye ne dan
birni, dole ina bukatar macen da zan keta a bi ni da kallo, wacce idan na sa ta
a gaban lens za ta dauki ido. Amma na ga kamar ba za ka gane ba.”
“Shi ke nan, Allah ya kai mu
lokacin da za mu gane wane ne bai gane din ba.”
*
Wata biyu da yin auren Habule
da Zizi, Habule ya fahinci duk wani kyalkyal da sheki da Zizi ke yi ashe
maya-mayai ne da hodoji, ya fuskanci duk harkar danfare (packaging) ce. Ba ma
wannan ba ne ya fi damun shi ba, yadda ta zama ba ta da lokacinsa. Bugu da kari
duk ta tsittsince masa ‘yan kudadensa, ta ja jarin kanta, ta fi shi muwalatin
harkoki.
A yanzu kam sai dai ya hango
ta a a social media. Haka take rangwada make-up ta yi radau da ita, ta dauki
hotuna ta watsa, ana ta yi mata comments da liking.
Da abin ya ishe shi, ya je,
ya sami mahaifinsa cikin damuwa. Yana magana da alamun jin kunya.
“Dad ya batun Nafisa?”
Alhaji Adamu ya sa halin da
yake ciki, har zai yi dariya sai ya basar.
“Me kake nufi da batun
Nafisa?”
“Ina nufin a nemar min
aurenta.”
Yanzu dariya ta kwacewa
Alhaji Adamu.
“Nafisa tana dakin mijinta
cikin kwanciyar hankali. Ina matar taka?”
“Gaskiya Dad ba zan boye maka
ba, wannan yarinya ba kala ta ba ce.”
“Don me, yarinya kalar
kyamara, ka ce min ba kalar ka ba ce?”
“Lokaci da nake fadar haka ba
na yin hangen nesa, amma yanzu ina tafe da hangenka Dad.”
“Ai kuwa Zizi kalar kyamara
ce.”
Ya tsokane shi.
“Ni ma na san kalar kyamara
ce Dad. Amma ba kala ta ba ce. A yi hakuri.”
Alhaji Adamu ya kyalkyale da
dariya.
“Ai kuwa Zizi kalar kyamara
ce.”
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
No comments:
Post a Comment