RAMA CUTA GA MACUCI BA LAIFI NE BA
Amma gane wanzami,
Mai bidar mai jarfa,
Rama alkhairi ga mai cuta ba illa ne ba,
Alan Waka.
Kar ka ruda rudadde,
Kar ka murda murdadde,
Rama cuta ga macuci ba illa ne ba,
Alan Waka.
Hakuri yana da maauni ba za ka dauki raini ba,
Hakuri yana da misali ba za ka dauki wasa ba,
Hakuri yana da suriri ba za ka dauki zambo ba,
Ba ka zo da cuta ba ba hali na zambo ba,
Ba da tsigunagun ba,
Rama cuta ga macucinka ba illa ne ba.
Kar ka juya juyayye,
Kar ka rikita rikitacce,
Maida alkairi a kan sharri ba tsoro ne ba.
Mun zamo madubin duban alumma na ci gaba,
Mun zamo fitulun da ke hasken binne su ba wai ba,
Mun zamo abin shaawar a gani a ji ba fahar ne ba,
Kar ka fara yin zamba,
Kar mu koyi yin zamba,
Ba batu na tsoro ba,
Mu ake duba da alkairi ba masu sharri ba.
Sara da sassaka ba zai hana gamji tofo ba,
Kainuwa dashen Allah ba shukawar mutane ba,
Tsiron da Allah ke so zai tsiro ba da lura ba,
Ba da kai ruwa gun ba,
Rabbi kai na sa gaba,
Ban nufi ga cuta ba,
Sama sassauci ga mai cuta ta ba tsoro ba.
Kar ka zagi zagagge,
Kar ka doki jemamme,
Kau da zambo ga mazambaci ba kasawa ba.
Hakuri yana da faraga da ba ai wa kaidi ba,
Hakuri yakan dafa dutse ya sha ba za ya kosa ba,
Hakuri yana saka bawa ya hau abokanan gaba,
Ba a ma yi komai ba,
Ba ka ma ga komai ba,
Ba ka riski komai ba,
Maida alkairi ga mai sharri ba illa ne ba.
Ba zai zo da gwalli ba,
Shi ba jahilci ba kauna ce,
Ba ja-in-ja ai ba,
Ku ne madubin dubawa ai rayuwa baba,
Ba a fara komai ba,
Ba ka riski komai ba,
Ku zo mu yo tuba,
Yanzu anka sa kamba,
Taimako da idanunka ka kauna bai ma ba.
Godiya nake a gurin Allah da ba za ta kirgu ba,
Da ya ba ni abokanan hulda ba yan taadda ba,
Ba yan izan wuta ba yan hikima ba yan baranda ba,
Fantimoti ag gaba,
Da Maryam A. Baba,
Ga Murja Yar Baba,
Da Fasihiya Fati Nijar mai hali babba.
An ciro wannan waka a littafin DIWANIN WAKOKIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA) Na Salisu Ahmad Yakasai da Abu-Ubaida Sani
No comments:
Post a Comment