Thursday, August 20, 2020

SHARHIN LITTAFIN WATA SHARI’A… NA AMRA AUWAL MASHI.

 
 

 

SHARHIN LABARIN WATA SHARI’A… NA AMRA AUWAL MASHI.

                                               ZAHARADDEN NASIR.

Manazarta su kan nazarci labari ne tun daga bangon littafin (idan bugagge ne) ma’ana publisher, har zuwa kalma, ko harafin qarshe da marubucin ya rubuta ya cikin labarin. Amma kasancewar wannan labarin online ne, to zamu fara ne daga sunansa zuwa abinda ya sauwaqa.

Idan aka ce wata shari’a… to abinda ake tsammanin ya boyi baya shi ne, ko dai sai Allah, ko kuma sai a lahira. Waxanda dukkansu zasu iya xaukar  ma’ana xaya ne da ke nufin; tabbatar da haqqi a muhallinsa, ko a muhallin da ba nasa ba, bisa ga bayyanar hujjoji na zahiri. Waxanda zasu tilasta mai haqqin qyalewa dole sai anje lahira, Allah ya yi shari’ar da ita ce ta gaskiya.  Ga duk wanda ya karanta labarin, zai ga yadda marubuciyar ta yi qoqarin nuna hakan, tsakanin Salma Abubakar (Gentle) da kuma Aishatu Abubakar (Ummimah), a labarce.

SALO; (plot) A cikin rabe-raben salon bada labarai guda tara da manazarta suka rarraba, marubuciyar ta xauki xaya daga cikin salaye masu wahalarwa wajen bayar da labarin. Inda ta fara bada labarin daga lokacin da lauyoyin nan biyu (mata da miji) suke sharara gudu a mota, bayan sun dawo daga aiki, wanda nan xin kusan tsakiyar labarin ne.

Mixing Plot; salon bayar da labari daga tsakiya, sai a dawo farko, sannan a koma qarshe. Marubuciyar ta yi qoqari wajen bayar da labarin bisa wannan tsarin, ba tare da zaren labarin ya tsinke mata ba. Sannan ta yi qoqari wajen jeranta tunanin mai karatu.

RIKICI; (Conflict) A labari shi ne tarzoma ko savanin da zai faru tsakanin babban tauraron labari, da kuma maqiyinsa. Wanda wannan shi ke haifar da gaba-xaya labarin ma, wanda daga qarshe za a sanya ran ganin sakamako, ko hukunci, har ma da darussan da ake so mai karatu ya xauka a cikinsa. Kamar yadda aka nuna savani tsakanin gentle da Ummimah a wannan labarin, aka kuma yi qoqari wajen nuna sakamako, tare da jefa darussan da na tabbata duk wanda ya karanta labarin zai ci karo da su a wurare da dama. Marubuciyar ta bi wasu matakai guda biyar, na dasawa, da havvakawa, tare da warware rikicin cikin labarin.

Gabatarwa;  farko, ko gabatar da wani vangare na labarin, ta yadda mai karatu zai fahimci qashin bayan rikicin cikinsa. Shirya labarin, tare da bayyana taurarin ciki da alaqarsu da juna a cikin labarin. Kamar yadda marubuciyar ta nuna mana labara ne da ya shafi shari’a ko neman haqqi. Sannan ta nuna mana barista Umar, da Barista Sultana miji da mata ne da suke son juna, kuma suna aiki ne a waje xaya. Sannan ta nuna qashin bayan rikicin labarin a lokacin da saqon ku taimaka mata, kar su cutar da ita… yake shigowa cikin wayoyinsu.

Havvakawa; havvaka rikicin cikin labarin, tare da sanya zargin taurarin labarin a zukatan makaranta, da kuma haifar da zararrukan labara. Marubuciyar ta nuna mana hakan a labarinta, lokacin da saqonni suka yawaita shigowa na buqatar a taimaka, tare kuma da voye wanda ke turo da saqon, wanda hakan ya harzuqa lauyoyin biyu.

Tsanantawa;  kai wa maqura wajen tsananin da rikici ya kai, tare da sanyawa makaranci tunanin ta ina nasara zata zo, ko ta ina faxuwa zata zo? Ta yadda masu karatu zasu cika shauqin son sanin abinda zai faru a gaba. Mun ga hakan a zaman kotun qarshe ta farko. A yayin da aka nemi Dr. Rafiq shaida ta qarshe da su barista Umar suka dogara da shi aka rasa.

Sassaurawa; nemo bakin zaren matsala, tare qoqarin warwaresu a hankali, ta yadda za a samu wata madogara qwaqqwara da zata jagoranci warwarewar komai. Kamar yadda bayyanar Dr. Rafiq, YB da sarki Manu, suka jagoranci warwarewar matsalar Ummimah.

Warwarewa; qarqare labari, tare da warware dukkan matsalolin da ke cikinsa. Da yin hukunci ga taurarin labarin. Kai tsaye mai karatu zai iya gane a inda labarin nan ya zo qarshe, tun ma kafin alqali ya yanke hukunci.

Marubuciyar ta yi amfani da salon qarqare labara cikin murna, wato Happy Resolution.

TAURARI DA XABI’UNSU

Daga irin rawar da taurarin labarin suka taka, za mu fahimci qwarewar da marubuciyar ta yi a fagen rubutu da kuma sanin xabi’u da halayen mutane.

Duk da kasancewar Barista Umar da Barista Sultana miji da mata ne da suke qaunar juna, tare da qoqarin farantawa junansu, daga rayuwarsu muna iya fahimtar yadda kowanne yake aiki tuquru don ganin ya yi abinda ya dace. Burin Barista Umar shi ne ya sauke haqqin iyalanshi, tare da qoqarin ganin cewa waninsu bai nemi wani abu ya rasa ba. A wurare da daman a labarin, muna ganin  yana ajiye aiki a cikin gida duk muhimmancinsa, da zarar matarsa tazo gareshi. Daga xabi’unsa zamu fahimci xabi’ar maza ta rashin damuwa da duk wani abu da ake voye musu.

Burin Barista Sultana shi ne, kula da mijinta, ‘ya’yanta, da tarbiyarsu, da farin cikinsu. Ta yadda idan xayansu yayi kuka za tayi qoqarin sanin abin da ya sanya shi kukan tare da rarrashi. A xabi’unta zamu fahimci yadda mace ke damuwa da abinda ake voye mata.

Haka idan ka bi dukkan taurarin labarin zaka ga kowa ya dace da sunansa, da kuma irin rawar da ya taka.

SAITI

A labari saiti na nufin wuri, lokaci da kuma yanayin da labarin ya faru. Wanda duk za su iya zama na zahiri ko kuma qirqirarru. A labarin Wata shiri’a, marubuciyar ta yi amfani da wurare na zahiri lokaci da kuma yanayi. Kamar katsina, jalingo. Dama tun a farkon labarin muka fahimci a yanayin damuna muke. Sannan ko da ba a ambaci shekara ba, za mu iya fahimtar cewa a wannan zamanin ne labarin ya faru, duba da irin matsalolin da labarin ya qunsa waxanda duk irin na zamanin nan ne.

TSINKAYE

A kan samu nason hali ko xabi’ar mai aikin adabi a cikin aikinsa. Daga cikin abubuwan da zumu iya tsinkaye na halaye, ko buri, ko ra’ayin marubuciyar a cikin rubutunta, sun haxar da; tsafta, kulawa. Mun rula marubuciyar a kaloli tafi son kalar pink, sannan ko dai tana son ta iya sarrafa girki, ko kuma ta qware a fannin. Hakan ya bayyana ne ta wajen Barista Sultana.

Tana da son son ‘yan uwanta, tana son iyayenta, da matuqar yi musu biyayya, sannan tana da saurin kuka. Wannan ya bayyana ne ta vangaren Aisha Abubakar.

Tana da matuqar sadaukarwa, da tsayawa a kan gaskiya.

QARQAREWA.

Daga qarshe, zan qarqare da maganar wani masani da yake cewa;

Ba a amintar da gaskiya a kan cewa zata sha wahala ba, amma an amintar da ita a kan cewa ba zata tozarta ba.ba

Tabbas! Labarin wata shri’a… ya hau kan doron wannan maganar, ga duk wanda ya karanta zai tabbatar da haka.

 

ALHAMDULILLAHI.

ZAHARADDEN NASIR

07060861140

www.zaharaddennasir9@gmail.com

 

 

Wednesday, August 12, 2020

BITAR SANIN MAKAMAR AIKI A FANNIN RUBUTUN FIM 2020

 

BITAR SANIN MAKAMAR AIKI A FANNIN RUBUTUN FIM 2020
Bala Anas Babinlata
 
Assalam alaikum wa rahmatul lahi wa bara katuhu.
Biyo bayan fitowar littafin Rubutun Fim a watan shida na wannan shekarar, zan yi amfani da wannan damar wajen sanar da marubuta da masu sha'awar rubutu cewa, za a shirya taron bitar sanin makamar aiki a fannin rubutun fim. Wannan bitar za a yi ta ne don yin fashin baki na yadda za a iya amfani da Littafin Rubutun Fim don gina labari mai sarkakiya.
 
Taron Bitar wanda za a yi a Kamfanin shirya finafinai na iStudios dake kilomita 20 Kwanar Dawaki, kan titin Zaria zai dauki tsawon kwanaki hudu, wato Alhamis, Juma'a, Asabar da Lahadi a makon farko na watan September mai kama wa. Wanda ya zo daidai da 3 ga wata zuwa 6 ga watan September, 2020. Mutum 20 ne kacal zasu samu shiga wannan bita.
 
Haka nan za a yi makamancin sa, amma ta yanar gizo ga wadanda ba a Kano suke da zama ba a makon karshen wata. Daga 24 zuwa 27 ga watan September, 2020.
Saboda haka masu bukatar halarta zasu iya tuntuba ta ta Wannan lambar 08036253479 ta waya ko ta WhatsApp don jin karin bayani.
Na gode.
Bala Anas Babinlata

 

Monday, July 27, 2020

HIKAYOYIN KAIFAFA ZUKATA na Malam Aminu Kano




GABATARWA

A kowanne zamani, a ko'ina a duniya za a ga koyaushe mutane suna da hanyoyin koyar da 'ya'yansu hankali, tsinkaya da basira, jurewa, hakuri, azanci da dabara da dai sauran halayen da za su taimake su lokacin da suka fara ma'amalar zaman duniya.

Daya daga cikin hanyoyin nan yakan kasance iya amfani da harshe wajen magana. Daga nan sai labarai na gaske da na almara, zaurance, karin magana, azancin tatsuniya, habaici, wa'azu, waka, cita-cita da sauransu.

Harshen Hausa ko kadan bai gaza wajen wadannan ba; haka kuma wajen labaran ban dariya, azanci, tausayi, wayo da dabara.

Ganin abubban nan sun fara bacewa a kasar nan, da kuma ganin rashinsu zai tauye mana wata daraja nan gaba balle ga ba da ilimi kyauta ga 'ya'yanmu ya zo, na duaki nauyin rubuta wadannan dan littafi da fatan taimakawa a wannan siffa. Kuma ina kara fata da addu'a cewa zai zama kafin alkalami ne ga sauran marubuta.

Mai karatu zai ga na debo abubba daga sassa; har da labarai na gaskiya bayan na almara saboda manufa dai ita ce kaifafa zukatun yara don kafin su girma su sami wukar gindi maganin aron ta wani. Allah ya yi mana muwafaka.

Daga karshe ina so in mika godiyata ga 'yan Komitin Inganta Hausa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano musamman ma Marafan Sakkwato Alhaji Ahmadu da Dr. Dandatti Abdulkadir, Dr. Kabir Galadanci, da Alhaji Abdulmalik Mani da Alhaji Usman Mairiga, da Alhaji Abdullahi Khalil, da M. Ibrahim Yaro Yahaya wadanda suka karfafa mini gwiwa a taron da muka yi a Sakkwato cikin watan Oktoba 1976 kan wallafar wannan littafi don tarbiyyar yaranmu da inganta hikimomin Hausa.

 

Aminu Kano.

Kano, 21st January, 1977

DAUKAR FANSA na Nasir Ibrahim Umar



A yadda ta ce, wai dole ne ta dauki fansar iyayenta, ko da kuwa yin hakan na iya zama sanadin salwantar rayuwarta.
Sai dai kuma, ta furta hakan ne tun sa'ar da take zaune a kasar Labanon kafin ta sauka a kasar haihuwarta. wanda nan ne tushen faruwar al'amarin.
Watanni uku da zuwanta, sai abubuwa suke sauya a wajenta, domin kuwa tana nema ta kashe, ana nema a kashe ta.

Sunday, July 26, 2020

SANIN MAKAMAR FASSARA na Salisu Ahmad Yakasai




"SANIN MAKAMAR FASSARA"

Sabon littafi ne da yake dauke da bayanai da darussa dangane da Fassara A Hausa. Littafi ne da Farfesa a harshen Hausa, kuma gwani a fannin Fassara ya wallafa. Farfesa Salisu Ahmad Yakasai qwararre ne sosai a fannin fassara kuma ya baje-kolin qwarewarsa ta tsawon shekaru a fannin fassara a cikin wannan littafin nasa. Ina masu son "Sanin Makamar Fassara" a Hausa, za a iya tuntubar Alfarah for Hausa Translation, reshen "Alfarah Educational Enterprise" a kan wannan lambar: 09081606066, a kan farashin naira 2,200.

Allah Ya yi jagora, amin!

Daga shafin Muhammad Sulaiman Abdullahi

Monday, July 20, 2020

NASABA TSAKANIN LABARI DA LABARIN FIM -Daga Rahma Abdulmajid





NASABA TSAKANIN LABARI DA LABARIN FIM

 

Rahma Abdulmajid

 

Bismillahirrahmanirraheem. Assalaatu Ala RasulilKareem.

 Kalmomin "Story By", "Screenplay By" "Written By" kalmomi ne da mai biye da jawabin godiya na kammala fim kan hadu da su, kuma su rikita shi, saboda tunanin kowa a karon farko akan fim shi ne; mai labari fa shi ne marubucin labari da tsara shi. Amma kuma ga shi a nan an karkasa aikin wa mutane da yawa, shin me hakan ke nufi? Haka ma da yawa marubuta ko masu dauke da labari a zuciya kan ji cewa ai da zaran ina da labari to fa ni marubuci ne har kuwa rubutun fim!

Muddin ba a samar da hanyar fallasa wannan tunani da wartsakar da shi ba, to zai yi wuya mutane su san abin da ke kunshe a wannan littafi da muke kaddamarwa na rubutun fim a yau, domin da zaran mutum yana da labari ji yake ya zama marubuci, in ko ya zama marubuci ai baya bukatar irin wannan littafin don koyon dabarun zama marubuci.

Don haka me ake nufi da Labari? Me ake nufi da rubutun fim? Sannan wace alaka ce tsakaninsu?

 

LABARI shi ne wani bayani da za a bai wa mai saurare ya saurara ko ya karanta, amma ba shi da damar ganin sa sai dai zuciyarsa ta sauwara masa labarin da jarumansa.

 

LABARIN FIM kuwa shi ne tsararren hoton labarin da aka hutasshe da zuciyar mai sauraro da kallo daga sauwara wa kansa ta hanyar nuna masa shi akan idonsa da taimakon allon kallo.

 

Koda yake za a iya ji ana amfani da kalmar labari da nufin rubutun fim, sai dai kalmar "Labari" ko "Story" a fannin rubutun film ta sha bambam da kalmar labari da mutane suka fi sani.

 

A cewar Patrick Cattrysse: Kalmar Labari a fannin fim tana nufin wasu sadarori hudu ko biyar da ke bayar da labarin jarumin da kalubalensa cike da amfani da hanyoyin da za su ja hankalin masu zuba jari a labari ba masu zallar sauraro ba, Nasarar wannan salon labarin shi ne ya karbu a wajen masu hannu da tsaki don ya zamo "Screenplay" har ya iso matakin hoto mai motsi.

 

Mahadar abubuwan biyu kuwa a bayyane take a salon ba ni gishiri-in ba-ka manda tsakanin labari da rubutun fim, domin a yayin da labarin ke zama jari ko uwar kudin "Screenplay", Shi kuma "Screenplay" shi ne ribar wannan uwar kudi wato labari.

 

Daraja daya Labari ke iya nuna wa "Screenplay" a wannan dangantaka shi ne: A kowane "Screenplay" akwai labari, amma ba a kowane labari ne akwai "Screenplay" ba ko kuma a wani salon mu ce gundarin labari ne ke haifar da tsararren labarin film.

 

Hakan na nufin duka abubuwan biyu na bukatar marubuci ne ya rubuta su, amma kuma abin mamakin shi ne hakan baya nufin kowane marubucin labari ne marubucin fim, sai dai a ce ya fi yi wa marubucin labari saukin zama marubucin fim fiye da farar hula a harkar.

 

Dalilai fiye da daya sun zamo sanadiyyar hakan cikinsu akwai:

1. Rubutun Fim, labari ne da ake shirya shi bisa ka'idoji tsaurara da ba su da jimirin bai wa marubuci uziri kamar wanda sauran labarai ke ba shi.

 

2. Labarin Fim tun daga samansa zuwa kasansa kasuwanci ne da ke bukatar kwarewa maimakon zallar kirkira da tunani don a mafi yawan lokuta yana dauke ne da jarin wanin marubuci ba marubucin kai tsaye ba.

 

3. Samar da Idea ba ta tattare da wata asara ko kuma uwar kudi, domin aikin kwanya mai tunani ne, ita kuma kwanya mai tunani tana kasancewa ne cikin aikinta na tunani yana so ko ba ya so, da riba ko hasara, amma inda gizo ke sakar, shi ne wannan Idea din na iya zame masa babban jari idan ya iya sarrafa shi ta hanyar rubuta labarin Fim.

 

Wani producer ya taba samun wani marubuci yana bayar da wani labari da na kirkira, ka da bakinsa sai ya ce "kana ta bayar da labari idan aka sace maka fa?" Marubucin ya yi dariya na amsa masa "Sai na kirkiro wani, wannan ne ya sanya ake kira na storyteller, saboda a duk inda nake ya kamata na iya samar da sinima ga abokan hirata ko da babu majigi. Amma idan na mai da shi Script to ya tashi daga Story ya zama jari har ya hau kan takarda, a nan ne ba zan bari kowa ya saci jari na ba"

Don haka Labari shi ne uwar kudi amma ba shi ne jari ba, iya mayar da labarin jari shi ne jari, shi kuma iya mai da labari jari ana yin sa ne bisa kwarewa da bin matakan ilminsa wanda su aka tattara a wannan littafin da muka taru don karramawa Da fatan duk wanda ke wurin nan zai yi kokari ya mallaki wannan dabara.

Assalamu alaikum


an karanta wannan rubutu a ranar da aka gabatar da littafin Rubutun Fim na Bala Anas Babinlata

Alƙalancin Gasar Rubutu

 Alƙalancin Gasar Rubutu Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkay...