Thursday, November 18, 2021

The Desirable English Teach Yourself Book Cover


 

SIRA BOOK COVER


 

RUDANI BOOK COVER


 

NEW LEARNING GRAMMAR BOOK COVER


 

MASARAUTARMU BOOK COVER


 

KOMAI DA RUWANKA BOOK COVER


 

KHADDUL ARABI BOOK 2 COVER


 

HAUSAWA: KABILA KO YARE?

HAUSAWA: QABILA KO YARE?

Daga Kabiru Yusuf

Shin Hausawa sunan qabila ne ko sunan harshe?

Su dai Hausawa, suna ganin kansu qabila ne. To amma duk wanda ya tsaya ya bayyana ma’anar qabila sosai, sai ya ga Hausawa sun qi shiga.

Misali bisa bayanin marubuta, qabila al’umma ce mai asali xaya, da yare xaya, da kamanni (watau qirar jiki) kusan iri xaya, da al’adun gargajiya iri xaya, da ra’ayin zaman duniya (watau falsafa) xaya, da sauran irin su. Kuma lallai ne cikin wannan al’umma kowa yana da’awar shi xan qabilar ne.

To idan aka biya wannan bayani kuwa, sai a ga bai kamata a kira Hausawa da sunan qabila ba. Sai dai a ce su taro ne na qabilu daban-daban da suka cuxanya da juna, kuma suka taru, suke magana da harshe xaya. Ita kanta kalmar “Hausa” a wurin Bahaushe tana nufin “harshe” ne. Akan ji Bahaushe ya ce, “Ban ji wannan Hausar ba,” watau bai gane wannan yaren ba kenan. Ko kuma ya ce ya ji ana “wata Hausa,” watau, ya ji ana magana da wani harshe.

Bugu da qari, idan ka tambayi yawancin haifaffen qasar Hausa, ka nemi ya faxa maka qabilarsa, sai ya ce maka, shi Bafillace ne, ko Babarbare, ko Buzu, ko Banufe, ko wata qabila daban. Ga shi kuwa a wannan harshen bai san ko sannu ba.

Kuma ana samun qabilun da ba su ji Hausa ba, amma su riqa da’awar su Hausawa ne, misali Abakwa Riga na Wukari da Takum da Lafiya.

 

(an ciro wannan bayani daga littafin ‘Zaman Hausawa’ bugu na biyu, na Habib Alhassan da Usman Ibrahim Musa da Rabi’u Mohammad Zarruq)


 

Monday, November 15, 2021

BAMBANCIN KARIN MAGANA DA HABAICI

BAMBANCIN KARIN MAGANA DA HABAICI

 Kabiru Yusuf Fagge (anka)


MAGANGANUN HIKIMA

Ma’anar Magaganun Hikima

Da farko, Karin Magana da Habaici suna cikin maganganun hikima na Hausawa.

Wannan nau’i na adabi yana nufin maganganu ne guntattaki na hikima masu bukatar karin bayani.

Wadannan maganganu kamar yadda masana suka fada, sun samo asali ne daga wata siga ta boye manufa wadda ba lallai ne mutum ya gane ta farat daya ba, ana amfani da su a cikin harshe da badda-bami da kuma sakaya (takaita) magana.

Maganganun hikima sun hada da:

1.     Karin magana

2.     Bakar magana

3.     Ba’a

4.     Zambo

5.     Habaici

6.     Barkwanci

7.     Zaurance

8.     Kirari

9.     Karangiya/Salon magana

10.                        Kacici-kacici

11.                        Shagube

12.                        Tumasanci

13.                        Sara

14.                        Arashi

15.                        Gatse

16.                        Gugar zana

17.                        Dungu

18.                        Waskiya

19.                        Saye

20.                        Wake

21.                        Santin magana

 

BAMBANCIN DA KE TSAKANIN KARIN MAGANA DA HABAICI DA BA’A

 

(1)KARIN MAGANA

“Karin magana dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kadan cikin hikima.”

 

Masana da dama sun yi bayani dangane da ma'anar karin magana, kamar haka:

"Karin magana tsararren zance ne wadda ke zuwa a gajarce na hikima da zalaka tare da bayar da ma'ana gamsasshiya, mai fadi, mai yalwa musamman idan aka tsaya a ka yi bayani daki-daki." (Yahya 1992).

 

Akasari kafin mutum ya fahinci ma'anar karin magana sai ya nakalci al'adu da dabi'un Hausawa kai har ma da tarihinsu. Misali idan Bahaushe ya ce "Yau na yi kunar bakin wake." Ga wanda bai nakalci harshen Hausa yadda ya kamata ba zai dauka cewa "wake baki yau na kona." Asalin ma'anar kalmar cikin hikima shi ne kasada ko kuru ko shiga hadarin da ke da wuya ainun wajen fita.

Daga ra'ayoyin magabata dangane da ma'anar karin magana za mu ga cewa karin magana ta tattara abubuwa kamar haka:-

·        Gajartacciyar magana

·        Hikima da zalaka

·        Bayar da ma'ana gamsasshiya

·        Dabarun dunkule magana

·        Takaita magana cikin hikima da basira

·        Ma'ana mai yawa da ta zunzurutu

·        Guntuwar magana ta hikima

 

Dangane da tubalan ginin karin magana kuwa, kusan za a iya cewa karin maganar Hausa sun taba duk harkokin rayuwa; amma za a iya samun yin amfani da mutane kamar malamai, attajirai, tambadaddun mutane cikin al'umma da abubuwan da suka shafi addini. A kan kuma yi amfani da sunayen dabbobi, kwari, tsuntsaye da ma muhimman abubuwa ko wurare da sauran su da dama.

 

YADDA AKE AMFANI DA KARIN MAGANA

Jazaman ne, wai shiga karuwa wuta, idan mutum na son iya amfani da karin magana sai ya san al'adu da dabi'un Hausawa da tarihinsu ciki da bai, domin akwai wasu karorin magana da aka gina su bisa tarihin abubuwa da suka wanzu tsakanin al'ummar Hausawa da kasarsu. Dole ne mai son yin amfani da karin magana sai ya saki jikinsa yadda ya kamata ba tsoro ba jin kunya a lokacin da yake magana, hakan zai iya ba shi damar baje-kolinsa ya fadi abin da ya kudiri aniyar fada.

 

Sau da yawa kuma, karin magana na zuwa ne a salo irin na bangare biyu:

-Bangare na farko na dauke ne da bayani akan wata manufa a jimlace.

-Yayin da bangare na biyu kuwa sharhi ko karin bayani kawai ya ke yi kan bangare na farko. Misali:

Banza a banza, Nasara ya ga Zagi.

Kanku ake ji, mahaukaci ya fada rijiya.

 

Bugu da kari, karin magana na nuna iya magana da nuna lakantar harshe na mai magana kuma yakan sanya masu sauraro rashin kosawa da zancen da ake yi masu komai yawansa. Duk wanda ya iya sanya ko amfani ko sarrafa karin magana a zantukansa, yakan samu farin jini wurin masu sauraro.

 

Yana da wahala a ce ga wanda ya kirkiro ko kago karin magana da ake amfani da su ko kuma lokaci ko yanayin da aka kago su; amma ana iya cewa naso ne na al'adu da dabi'un al'ummar Hausawa ya samar da karin magana.

 

Shudewar tsohon zamani da zuwan sabon zamani kan taka muhimmiyar rawa wajen mantawa da tsofaffin karin magana da kirkiro sababbin karin magana ta hanyar afkuwar wasu abubuwa a rayuwa.

Ana hasashen cewa, mutanen da su ka fi taka rawa gagaruma wajen yin karin magana da kirkiro sababbi su ne mata, maroka, makada da mawaka, 'yan daudu, mahauta da ma masu sayar da goro da sauran daidaikun jama'a a cikin al'ummar Hausawa.

 

Rabe-Raben Karin Magana

A harshen Hausa, karin magana na da rabe-rabe da dama amma kadan daga ciki sun hada da:

1. KARIN MAGANA MAI LABARI:

Kamar yadda sunan ya nuna, wannan karin magana ya danganci labari ne na wani mutum, wuri ko wani abu muhimmi da ya auku. Irin wannan karin magana sai mutum ya san asalin labarin kafin ya kai ga fahimtarsu. Wadda ya san tarihin wani abu hakika tamkar ya rayu da abin ne. Saboda haka wannan karin magana sai an binciki tarihi. Misali:

                               i.            Fadan Gwaggo a Kofa

                             ii.            Lissafin dokin Rano

                          iii.            Zuwa fara Garko

                          iv.            Jifan Gafiyar Baidu

                             v.            Abin da ya ci Dama ba zai bar Awai ba

                          vi.            Jita-jita karatun Bamaguje

                        vii.            Gobarar Titi a Jos

                     viii.            Kunar bakin wake

                          ix.            Labarin kanzon kurege

 

2. MAI TAMBAYA:

Daga jin wannan sunan, wannan karin magana mai tambaya yana da bangare biyu; bangaren farko na dauke ne da jimlar tambaya wato dole ne a samu alamar tambaya a karshen jimlar. Bangare na biyu kuwa na dauke ne da bayani ko sharhi a kan bangare na farko. Misali:

                                           i.            Me na ci na asham? Balle na yi ramakon sallah

                                         ii.            Kai kuma a su wa? Kare da gudun layya

                                      iii.            Me ya fi raina? Cin tsiren mata

                                      iv.            In ce da wukarsa ya tafi? An ce da akuya sarkin fawa ya mutu.

                                         v.            Wa ya isa ya fada? Gyambon uwar sarki na doyi.

 

3. KARIN MAGANA MAI “IN JI”

                                           i.            Haka tara, in ji kishiyar mai mageduwa

                                         ii.            Zama wuri daya tsautsayi, in ji kifi

                                      iii.            Allah ya yi abin, in ji mafadin aurensa

                                      iv.            Haka tara, in ji kishiyar mai mageduwa

                                         v.            Ban sa a ka ba, in ji barawon tagiya

                                      vi.            To ku yi ku nade, in ji barawon tabarma.

 

4. KARIN MAGANA MAI “ANCE”

                                           i.            Har ka tuna mini, an ce da mahaukaci ba ka duka

                                         ii.            Ban ga dama ba, an ce da kare ya bayar da wuka

                                      iii.            Na nawa kuwa, an ce da kuturu Allah ya la'ance ka.

                                      iv.            Wai kai da neman suna, an ce da kare malam Mohammadu

 

5. KARIN MAGANA MAI “KOWA”

                                           i.            Kowa ya kona rumbunsa ya san inda toka ke kudi

                                         ii.            Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha

                                      iii.            Kowa ya ji dauke ni, ya ji sauke ni.

                                      iv.            Kowa ya yi maka kan kara, yi masa na itace

                                         v.            Kowa ya daka rawar wani, ya rasa turmin daka tasa

                                      vi.            Kowa ya sake, a yi masa sakiya

 

6. KARIN MAGANA MAI NASIHA

                                           i.            Sannu ba ta hana zuwa

                                         ii.            Hakuri wadar mai shi

                                      iii.            Alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza

                                      iv.            Arziki rigar kaya, kana ja tana janka

                                         v.            Komai ya yi zafi maganinsa Allah

 

7. KARIN MAGANA KAFIN MUSULUNCI

                            i.        Jita-jita hadisin Bamaguje.

                          ii.        Kida a ruwa mai tada hankalin dodo

                        iii.        “Samun lamuni ga dodo kansa a shiga ruwa lafiya.

 

8. KARIN MAGANA BAYAN ZUWAN MUSLUNCI

                                           i.            Allah Sarkin dadi, in ji barawon takanda

                                         ii.            Bin na gaba bin Allah

                                      iii.            Kumfar ilimi, ilimi ne

                                      iv.            Rokon Allah maganin wayyo Allah

                                         v.            Ga mu ga Allah, mai takaba ta taka gawa

 

9. KARIN MAGANA BAYAN ZUWAN TURAWA

                            i.        Banza a banza, Nasara ya ga Zagi

                          ii.        Ba a iya Bature ba, Inyamuri ya ga Zabiya

 

KADAN DAGA WASU KARIN MAGANAR HAUSA

1.           Ba a shan zuma sai an sha harbi

2.           Kowa ya ci zomo ya ci gudu

3.           Barin kashi a ciki baya maganin yunwa

4.           Karamin sani kukumi ne

5.           Kwai a baka ya fi kaza a akurki

6.           Ba dadewa zan yi ba, an yi wa mai kwadayi Bismillah

7.           Ba a gama abinci ba, an yi wa marowaci sallama

8.           Ba shiga ba fita, an sa mahaukaci gadin kofa

9.           Hayaniya ta yi yawa, an sa wawaye tsere

10.      Gobe ma a kara, an ci garin sadaka an hana maye

11.      A bar kaza cikin gashinta

12.      A bari ya huce shi ke kawo rabon wani

13.      Abin da dama ta jure, hagun ba ta jure ba

14.      Abincin wani ba na wani ba ne

15.      Abin da mutum ya shuka shi zai girba

16.      Abin da ya kora bera wuta, ya fi wutar zafi

17.      Auren baya shi ne sadakin na gaba

18.      Kararrawar jirgi mai tada hankalin fasinja

19.      Banza ba ta kai zomo kasuwa

20.      Bikin magaji, ba ya hana na magajiya

21.      Sai a hankali, shi ya kashe dan jaki

22.      Ci bai zama daya ba, ai koshi ba zai zama daya ba

23.      Da babbar rowa, gara karamar kyauta

24.      Da ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki.

25.      Don kai ake hula har kunne yake samu

 

HABAICI

Shi kuma Habaici "Kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum."

 

Habaici zance ne na hikima da ake amfani da shi wajen yi da mutum a kaikaice amma ta kan canza halin mai mummunan hali yayin da ya fahimci da shi ake.

 

Dangambo (1982) ya bayyana habaici da cewa "Magana ce mai boyayyiyar manufa." akan yi magana da nufin niyyar wani abu ga wadda aka yi abin dominsa.

 

To, amma shi habaici idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai ya ke gane wadda aka yi habaici dominsa ba. Misali idan wani na da budurwar zuciya wato mai neman mata da halin da ba na kwarai ba za a iya masa habaici da cewar "Wannan tsohon tauren ya dame mu." To daga jin wannan wadda aka yi dominsa tuni zai fahimci cewa da shi ake.

A takaice Habaici shi ne yi da mutum a kaikaice. Habaici ya fi yawa inda kishi ko kyashi ya ke. Galibi mutane sun dauka cewa habaici salo ne na mata. Dalili kuwa shi ne tsakanin mata kishi da gasa da kyashi su ka fi yawa (Zarruk da wasu 1986).

Sai dai habaici yayin da ake yinsa duk wanda ya tsargu ya dauka da shi ake, to da shi ake. Wani zai yi kokarin maida martani ko da kuwa ba da shi ake ba domin mai kaza a aljihu ba ya jimirin "as."

Maroka da makada da wasu manyan mutane musamman mata kan yi ruwa da tsaki wajen yin habaici. Yara musamman samari da 'yanmata da 'yandaudu su ma kan yi nasu ruwa da tsaki.

 

Hausawa kan yi amfani da habaici ne ko don huce takaici, rowa, kishi, tsokanar fada, bayyana hassada, yakan kuma habaka rumbun harshe da kawo nishadi a tsakaninsu.

Habaici na son yin kama da karin magana domin wani masani ma na cewa ana samun habaici ne daga karin magana tare da la'akari da irin yanayin da aka yi amfani da karin magana sai ya zama habaici. Daga cikin rabe-raben habaici akwai wadda ake yin su cikin zantuka, akwai kuma wadda mawaka ke yi a wakokin su don muzanta abokin gaba.

 

MISALAN HABAICI

1.   Abokin mutum biyu, munafukin mutum daya

2.   Allah wadan naka ya lalace

3.   Allura ta tono garma

4.   Aikin banza, talaka ya girmi sarki

5.   An dai fadi ba nauyi

6.   Akuya ba ta gasa da kura

7.   Banza ta kori wofi

8.   Duk lalacewar tsohon zaki ya fi saurayin kare

9.   Kowa ya debo da zafi bakinsa

10.       Ban san ana harara ta ba sai ido ya fadi

11.       Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa

12.       Duk lalacewar tsohon zaki ya fi saurayin kare

13.       Idan maciji ya sare ka, in ka ga tsumma sai ka gudu

14.       Duk lalacewar masa ta fi kashin shanu

15.       Na ruwa ba ya zagin kada.

16.       Da ka koya wa mutum cin kifi gara ka koya masa yadda ake kamunsa

17.       Berayen gidan nan sun dame mu da sata

18.       Kowace gauta ja ce

19.       Ina ruwan makaho da kunya

20.       Habaicin Kura na mai akuya ne

 

BA'A

Ba'a magana ce da ake yi wa abokin zance da niyyar raha don aji dadin zance ko da niyyar shammata don a yi dariya. Wani lokaci ba'a kan bata ran wadda da aka yiwa.

Samari da 'yanmata masu neman aure da abokai da mahauta, makada da mawaka da masu sayar da goro su suka fi yin ba’a.

Ba'a na zuwa ne cikin nau'o'in kwatance; inda ake kwantata mutum da wasu abubuwa. Akan samu ba'a mai nau'i na nishadi.

Tana kuma a matsayin abin gwajin hakuri da duniya da juriya.

Ba'a kan kara wa hira kauri da tsawon lokaci ta hanyar saka karssashi da cire sigogin tsarguwa ko damuwa a zukata.

 

BAKAR MAGANA

Bakar magana wani salon magana ne da ake yi galibi don sosa zuciyar wani mutum.

Zarruk (1986) ya ce wani lokaci akan yi bakar magana ne a dalilin bacin rai. Akwai kuma wadda ake yi a cikin nishadi wadda ake yi a dalilin bacin rai; ma'ana samun wadda ake yi a fakaice wato ba a bayyana ba akwai kuma ta bacin rai a bayyanne.

Bakar magana ta bacin rai a fakaice ana yin ta ne idan wani ya bata ma rai sai ka ce "Ka kyauta" ko kuma idan wani ya yi maka wani aiki da ya bata rai sai ka ce dashi "Sannu da aiki." Ko idan aka aiki wani yaro ya je, ya dade a wani wurin idan ya dawo za a iya fada masa “har ka dawo?”

Ita bakar magana ta bacin rai a bayyane ana yinta ne ta hanyar kaurara magana a bayyane ba tare da boye wani abu ba.

Akwai bakar magana wadda kodayaushe tana nan kamar mai bata rai amma ba an yi ne cikin fushi ko don tashin hanakali ba. Irin wannan ita ake kira da bakar magana ta raha.

Akwai nishadi kwarai da hikima a bakar magana ta raha hasali ma hankali kwance mutum zai zabi abin da zai fada. Kodayake ma bakar magana salon kowane Bahaushe ne amma an fi sanin mahauta wajen yinta saboda haka ma galibi mutane kan zolaye su akan wannan salo su kuwa su ta kwararawa saboda ba sa tabuwa wajen iya bakar magana.

Dangantakar Ba'a da Bakar magana shi ne akwai raha da nishadi dukkansu akwai kuwa bacin rai da suka yi tarayya da shi sun kuma yi tarayya a masu kirkira da aiwatarwa.

Dangambo (1982) ya ce “Ba'a da bakar magana dukkansu maganganu ne da kan bata ran wadda aka yiwa. Wadanda aka fi sani da iya ba'a da bakar magana su ne mahauta da wasu daga cikin masu siyar da goro.

Misalin bakar magana da ba’a

Wata rana wani mutum ya je wurin wani Mahauci zai sayi nama (tsire) mutumin ya dubi naman ya ce “kai malam wannan naman ya gasu kuwa?” Sai Mahauci ya dube shi ya ce “a'a ai kiwo take yi.”

Wato Mahauci yana nufin dabbar ma ba a yanka ta ba tukunna mu ga karewar rashin gasuwa.

Haka kuma

Wata rana wani mutum zai sayi nama sai ya ce da Mahauci “Malam ya na ga naman ya yi kura ne?” Sai Mahaucin ya ce “Yakin Badar aka yi a kai.”

Wato ya nuna masa cewa gabadaya ma yakin akan naman aka yi karewar kura.

 

Har ila yau wata rana wani mutum ya je sayen nama sai ya ce da Mahucin “wannan naman na yau ne kuwa?” sai Mahaucin ya ce “Sa'an Kakata ne.”

Wato anan Mahaucin yana nufin cewa tsufan naman ya kai yawan shekarun Kakarsa.

 

Wani mutum kuma ya tambayi mahaucin ya ce "Yaya na ji naman yana wari? Sai Mahaucin ya ce masa “zanin mai jego ne”.

Wato ana nufin warin naman ya kai zanin mai jego wajen wari ke nan.

 

Wasu mutane su biyu masu sayar da goro da suke zuwa sari tare, wata rana sai daya daga cikin su ya riga dan’uwansa zuwa wurin da suke sari, ko da daya dan’uwan ya zo daga baya sai ya ce da na farko "Ai duk ka saye goron". Sai wadda ya zo da farkon ya ce "Shagamu na saye gabadaya". Wato wannan yana nufin garin da ake saro goron gabadaya ya saye, ba iya goron ba.

*

Wani mutum ya sayi goro da ya bare, ya wurga baki ya tauna sai ya ji daci, sai ya ce da mai goro “Yaya na ji goron da daci?” sai mai goron ya ce "Madaci na kasa ka saya ka tauna."

 

Manazarta

Dan Hausa, A.M. (2021) Hausa Mai Dubun Hikima, Kano, Century Research and Publishing Company, Kano Nigeria.

Gwammaje K.D. (2010) Karin Magana a Kasar Hausa, littafi na 1-3 K.D.G Publisher   Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (2002) “Harshe da Adabin Hausa a Kammale; Don Manyan Makarantun Sakandire.” Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan-Nigeria

Muhammad, Y.M. (2005) “Adabin Hausa.” Zaria: Ahmadu Bello Unibersity Press Ltd., Samaru-Zaria

Dangambo A. (1982) Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmacin Ga Rayuwar Hausawa, Triumph KanoNigeria.

Dangambo, A. (1984) “Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa.” Madaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Danhausa, A.M (2012) “Hausa Mai Dubun Hikima.” Kano: Century Research and Publishing Company, Kano-Nigeria

Yahya I.Y. (1988) Hausa A Rubuce, Tarihin Rubuce-rubuce Cikin Hausa N.N.P.C Zaria

Yahya I.Y. da wasu (1992) Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare Littafi na 1-2 Unibersity press PLC Ibadan

Yahya I.Y. da Dangambo A. (1986) Jagoran Nazarin Harshen Hausa N.N.P.C Zaria

Yunusa, Y. (2000) “Hausa a Dunkule.” Kano: Madaba’ar Jakara Bookshop.

Zarruk R.M da wasu (1986) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Kananan Makarantun Sakandire. Littafi na daya. Unibersity Press L.T.D. Ibadan


 

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...