Thursday, July 15, 2021
CAMFI
CAMFI Camfi shi ma wani bangare ne na al’ada ba za a iya gani ko a taba shi ba.
Camfi yana koyar da akidu ne ko wasu zantuka a bias doro na imani da al’ada.
Misalan camfi: -Duk yaron da ya cika cin kwai, zai yi sata. -Idan mace ta yi
mafarkin maciji ya sare ta, za ta sami ciki. -Idan ka cika kallon wata da rana,
idan kai saurayi ne za ka auri tsohuwa. -Idan kana shara da daddare a gida za a
yi talauci, ko ka share gidan aljanu. -Idan aka doki mutum da kallabi (dankwali)
zai rasa matar aure ko idan aka share ka da tsintsiya. -Idan ka kwana a daki
daya da kuturu, to kar ka riga shi fitowa za ka kuturce. -Idan ka yi kaki ko
majina ka tofar ba ka rufe da kasa ba to za ka yi cutar makogoro. -Idan mace mai
ciki ta tsallaka tulu cikinta zai zube. -Idan mace mai ciki ta je bakin rijiya
ko rafi, ‘yanruwa za su sace dan cikintya. -Duk wanda ya tsallaka kare zai kamu
da matsanancin ciwon ciki. -Idan mutum na yawan cire farce (kubba) da hakoransa
zai tsiyace. -Barin yana a daki na kawo talauci. -Idan mujiya ta yi kuka a gida
to za a yi mutuwa a gidan ko unguwar. -Idan ka fita da safe ba ka karya ba maye
zai kama ka.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
MAKAHO MAI FITILA
MAKAHO MAI FITILA Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wa...
No comments:
Post a Comment