Rubutunka
Tunaninka
MISALAI
DA BAMBANCEN-BAMBANCEN KARE-KAREN HARSHEN HAUSA
Kabiru Yusuf
Da
farko, bari in kara tuna mana tsarin yadda Hausar take ta haka za mu iya
bambance yadda Hausar kowanne bangare;
(1)
HAUSAR GABAS: su ne; Kananci, Bausanci, Zazzaganci, Kudduranci/Gudduranci,
Hadejanci
(2)
HAUSAR YAMMA: su ne; Sakkwatanci, Kabanci, Gobiranci, Zamfaranci
(3)
HAUSAR AREWA; wadda ta hada da: Dauranci, Gumalanci, Katsinanci, Damagaranci Da
sauransu.
KARIN
HARSHE DA DAIDAITACCIYAR HAUSA
Yanzu
bari mu dubi misalan yadda wasu kare-karen harshe suke da kuma yadda suke a
daidaitacciyar Hausa:
"TS"
Kare-karen
Yamma D/H
Tcimi tsimi
Hatci hatsi
Tcere tsere
Watce watse
Rantcatce rantsattse
(a
lura wajen furta "ts" sai su furta "tc")
MUSAYAR
KWAYOYIN SAUTI
A
nan ana nufin yadda wasu suke amfani da wata kwayar sauti madadin wata.
Sautin
"h" maimakon "f"
Yamma D/H
Hwata fata
Kahwa kafa
Sassahe sassafe
Hili fili
Laihi laifi
A
dangin Dauranci kuwa "sh" mai wasalin "i" ko "e"
ita ke zama "h". Mai wasalin "a" kuwa tana zama
"hy" ne, kamar haka:
Dangin
Dauranci D/H
Hirwa shirwa
Farahi farashi
Hekara shekara
Tahe tashe
Hyakka shakka
Hyayi shayi
Hya'ani sha'ani
Hyahyanci shashanci
Bayan
haka, dangin Dauranci, wani lokaci ma har da wasu kare-karenn yamma, sukan
dauri "I" maimakon "r", kamar haka:
Dangin
Dauranci D/H
Galgadi gargadi
Halbi harbi
Kalkashi karkashi
Malka marka
Walwala warwara
Zalbe zarbe
*A
Bausanci, "c" mai wasalin "i" tana zama "sh",
kamar haka:
Bausanci D/H
Shiki ciki
Shitta citta
Shigiya cigiya
Binshike bincike
Dagashi dagaci
Takaishi takaici
Idan
muka dan bi wadannan misalan za mu ga yadda wasu suke furta wasu kalmomi, ke
nan idan marubuci yana son ya bambace wa mai karatu, tauraro Basakkwace ko
Bakano ko Bakatsine ko Badamagare ko Bagumule ko Badauri ne yana bukatar
furucin da ya shafi karin harshensa, ba kawai ya ce tauraro kaza Basakkwace ne
amma Hausarsa ta Gumel ko ta Katsina da sauransu.
KA'IDOJIN
RUBUTUN HAUSA
Ci
gaba/Cigaba
Ta
farko ta zo ne a matsayin aiki, wato don haka a rabe take zuwa. Misali:
*Zo
ka 'ci gaba' da yin wannan aikin.*
Ta
biyu kuma a matsayin suna take, don haka a rabe take zuwa, misali:
*Lallai
na yarda an samu 'cigaba' a darasin nan."
Farinciki/farin
ciki
*Farinciki*
a nan suna ne, misali:
*Kodayaushe
yana cikin farinciki da annashuwa.*
*Farin
ciki* wannan kuwa, sifa ce ko aiki
*Za
ka yi farin ciki idan ka samu.*
*Daliban
suna ta farin ciki da samun nasarar.*
Bakinciki/Bakin
ciki
Hukuncinsu daya ne da farinciki/farin ciki
Shikenan
Shikenan;
na nufin an kammala abu, ko abu ya kammata. Misali:
1-
*Ai shikenan tun da ka siyar.*
2-
*Shikenan je kawai.*
3-
*Ai shikenan, sai mu tafi ko."
4- *Kurunkus, shikenan.*
4- *Kurunkus, shikenan.*
Shi
kenan
Kalmar
*shi* wakilin suna ne na mutum namiji, misali:
*Shi
kenan kullum cikin ciye-ciye.*
*Wai
har yanzu rigima yake?" "E mana, shi kenan cikin rigima a
kullum."
Manazarta:
Bunza,
A.M. (2002) "Rubutun Hausa: Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa. Don Masu Koyo
Da Koyarwa." Ibrash Islamic Publications Centre LTD., Surulere, Lagos.
Indabawa,
I.M da Fagge, K.Y (2000) Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai." Gimbiya
Publishers, Fagge, Kano.
Zarruk,
R.M. da wasu (2010) "Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Don Kananun Makarantun
Sakandire." Ibadan Press Plc, Ibadan Nigeria.
Yahaya,
I.Y. () "Darussan Hausa: Don Manyan Makarantun Sakandare." University
Press, Plc.
No comments:
Post a Comment