BARAYIN BOYE
Wani manomi ne wanda ya tsufa sosai, aka kulle dansa a gidan
maza (fursuna) saboda laifin da bai ji ba bai gani ba. Wannan dattijo ya rasa
yadda zai yi, kuma ga tsufa, sai ya rubutawa dan nasa wasika kamar haka:
Ya kai dana, a wannan shekarar shi kenan ba zamu yi noman
da muka saba ba, sbaoda ba zan iya tonon kasa ba, dama kai ne kake tayani,
yanzu ga shi ba ka nan!"
Da aka kai wa yaron bayan ya karanta yana hawaye, sai ya sa
'yansandan da suka kawo masa wasikar, suka ba shi biro da takarda, ya rubutawa
mahaifinsa nasa amsa kamar haka:
"Ya Babana kar ma ka fara tunanin noma wannan gonar
domin a wajen na binne Miliyan dari din da suke zargina na sato."
Lokacin da 'yansandan nan suka taho domin kai wa Dattijo
wasikar nan, sai suka karantata a hanya, ai kuwa nan da nan suka nufi gonar
mutumin nan suka rinka haketa, suna tono, sai da suka nometa tas, amma ba su ga
komai ba.
Washegari yaron nan ya sake rubutawa mahaifinsa nasa wata
wasikar ta daban, yana cewa:
"Ya Babana yanzu za ka iya yin shukar da kake so,
don na tabbatar an nome maka gonar."
Da mahaifin ya je, ya gani, sai ya yi dariya ya ce,
"Lallai yarona kana da basira, kana daure a gidan maza amma ka sa barayin
boye sun yi maka aiki. Ai jiyan ina boye, ina hangosu, na ga yadda DPO da
yaransa suke ta faman noma, su ga barayi."
No comments:
Post a Comment