ROMON DIMOKRADIYYA
Kabiru Yusuf Fagge
Muna tafe, tafiya mai nisa, kuma mai wahala, duk da
motar da muke ciki akwai na'urar sanyaya wuri da kuma tausasan kujeru da
nutsuwa, amma a hakan duk na jigata saboda rashin kyan hanya ga kuma zafin
rana.
Cikin damuwa, na dubi Cif Kamfen na ce masa,
"Wai shi ma wannan garin da za mu je, duk a cikin jihar Natsira
yake?"
Cif Kamfen ya yi dariyar yake, shi ma dai kallona
yake yi, ya ce "Honorabil ka manta ne, wancan karon fes tenuwa ai
mun zo, garin Kumaji ne fa, ka tuna da muka zo, har muka yi musu alkawaruka, wadanda
sun fi damuwa da batun ruwan sha..."
Na yi shiru ina tunani, can dai na tuna din,
"Gaskiya kam, sai yanzu na tuna, ni tuni ma na manta da su da dukkan alkawuran
da muka yi musu a wancan lokacin kafin mu ci zabe..."
"Kuma ka ga kamar yadda ka ce ka manta da
garin, haka ma mun manta ba mu cika musu alkawarukan da muka daukar musu
ba." Cewar Cif Kamfen.
Na girgiza kai, "Kwarai kuwa, ai abin ne da
yawa, gari kamar Natsira ba karamin gari ba."
Cif Kamfen ya dube ni, "To yanzu dai ga shi mun
dawo gare su da wata bukatar ya kake ganin za a yi?"
Na yi murmushi, "Idan ka dubi wahalar tafiyar
nan da hanyar nan, ka san da wuya a samu masu ilimi a garin nan, bare kuma wayayyu,
kawai muna zuwa zan sake yi musu wani alkawarin, don su sake zabarmu, daga baya
idan mun tuna da su sai mu yi musu rijiyoyin burtsatse ko guda biyu ne, idan
kuma mun manta shi kenan, ai ba su kadai ba ne mutanen jihar nan ba." Na
kammala maganar tawa ina wage baki cikin yake, a raina Allah-Allah nake mu je
garin mu yi abin da zamu yi, mu baro su.
Na lura da irin kallon da Cif Kamfen yake yi min, a
zahiri yana so ya gaya min abin da na fada ba daidai ba ne, amma kawai ya yi
min shiru. Kuma ni da shi mun san abin da muke yi zalunci ne, amma mun take
gaskiya.