GUDUMMAWAR MARUBUTA A SHIRIN FIM
A Takaice
Ado Ahmad Gidan Dabino MON
Gabatarwa
Ta hanyar rubutu ne marubuta suke
fitar da abubuwan da suke cikin zuciyoyinsu, wadanda suka faru da kuma wadanda
suke hasashen za su faru nan gaba, don jama’a masu karatu ko sauraro ta hanyar
rediyo su ji ko masu kallo kuma su karu da abubuwan da ke cikin rubutun wanda
ya shafi ilmantarwa ko tarbiyyantarwa ko nishadantarwa ko kuma akasin haka.
Rubutu rayayyen al'amari ne da kan
wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wadda in har an yi ta za a
girbi abin da aka shuka.
Wane ne Marubuci?
MARUBUCI DAN BAIWA NE, haihuwarsa
ake yi ba yin sa ake ba. Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar
rubutu yakan kirkiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi
amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa wadanda yake amfani da su don isar
da sako ga al'ummar da ke karatun rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne
ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar
ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa sidarori da
shafuka har zuwa cikakken littafi.
Wani ana haihuwarsa da rubutu wani
kuma koyo yake yi, amma duk marubuta za mu kira su. Shi marubuci mutum ne na
daban, ba wai ya fi sauran rukunonin bil'adama ba ne, a a, shi dai daban yake
da sauran mutane, wato dan baiwa ne. Marubuci na yin tunani ne iri na daban,
yana kuma kallon rayuwa da al'amuran rayuwa da wata irin fahimta tasa ta daban,
sannan ya bayyana ta a rubuce. Kamar yadda aka ambata a sama shi marubuci dan
baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne.
Mece ce Gudummawa?
Muwa wata mata ce mai tabin hankali
wadda take tafiya gudu-gudu sauri-sauri, idan ta zo ta tarar da mutane sai ta
ba su kyautar abin da ta zo da shi amma fa tare da ita za a cenye abin, wato za
ta zauna a ci abin tare da ita, idan ta ga ya kare sai ta tashi ta tafi, wannan
ita ce al’adarta kuma kowane lokaci haka take yi wa mutane, daga nan shi ne
idan mutum yana so ka ba shi taimako wanda yake sa ran nan gaba shi ma ya saka
maka ko kuma nan gaba kai ma ka amfana daga abin, ko kuma Allah ya saka maka,
sai ya ce wane me zai sa ba za ka yi min irin gudun da Muwa take ba, daga nan
ne mutane suka juya kalmar ta koma gudummawa kai tsaye. A dunkule kalmar
gudummawa tana nufin taimakawa da wani abu wanda kake sa ran samun sakamako a
nan duniya ko kuma lahira, wata kuma gudummawar ba a samun sakamako sai dai a
lahira.
Mene ne Fim?
Fim tantagaryar kimiyya da fasaha
ce, kuma rayuwar dan’adam ce ake nunawa. Fim yana dauke da tarihi da dabi’un
jama’a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu. Fim yare ne da kowane
mutum yake iya fahimtarsa a duniya, musamman bisa harshensa da tsarinsa na
rayuwa da hanyoyin tunaninsa da suka hada da gani da ji da motsi.
Har ila yau, fim hanya ce ta sanarwa
da ilmantarwa da jan hankali da nishadantarwa da fadakarwa da yada manufa da
tallatawa. A dunkule kafa ce daga cikin kafafen yada labarai, sannan kuma hanya
ce ta kasuwanci.
Wace Irin Gudummawa Marubuta Suka
Bayar a Harkar Fim?
Kacokan zan mayar da maganar ne a
kanmu wato masu shirya finafinan Hausa na asana’antar Kannywood, ba na son in shiga
wata uwa duniya gwara in tsaya iya inda muke muka fi fahimta, muka fi sani muka
fi wayo domin mu fi saurin kamo bakin zaren. Kuma za mu yi a takaice saboda nan
ba fage ne na Jami’a ba, wajen taron ga-ni ga-ka wanda za a baje koli ido da
ido ba a yi bayanai da baki da baki ba.
Kafuwar Kannywood
An kafa wannan masana’anta ne tare
da marubuta, marubutan kuma na littattafai ko in ce labarai. Wasu daga cikin mu
za su iya tuna lokacin, a wajejen shekarar 1994 zuwa 1995 aka yi yinkurin kafa
Kungiyar Masu shirya Finafinai ta Jihar Kano, wato Kano State Film Makers
Association. Mutanen suna da yawa amma wasu daga ciki da zan iya tunawa a
wannan kokari su ne:
1. Ibrahim M. Mandawari
2. Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
3. Aminu Hassan Yakasai (Marigayi)
4. Auwalu Muhammad Sabo
5. Auwalu Mashal
6. Dan’azumi Baba Chediyar ‘Yan
Gurasa
7. Bala Anas Babinlata
8. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
9. Balarabe Sango II
In muka dubi wannan jerin sunaye, za
mu ga sama da rabin mutanen marubuta ne, kuma duk suna da littattafai ko
labarai da suka rubuta a lokacin da suka yi wannan gangami na kafa kungiyar
masu shirya fim ta farko.
Yi wa fim Jaket: Wanda ya fara yin
sa shi ne Bala Anas Babinlata a shekarar 1995. Kafin ya gabatar da wannan
tunani, ba a sanya wa fim jaket sai da ya kawo wannan abu ne aka amsa ga shi
har yanzu ana yi wa fim jaket.
Samar da sunan Kannywood a shekarar
2002, Sunusi Shehu Daneji shi ne ya samar da wannan suna kuma marubuci ne na.
Marubuta da Suka Fara Kafa
Kamfanonin Shirya Finafinai Kuma Suka Zuba Jari
Ga wasu daga cikin marubuta da suka
bayar da gudummawa wajen kafa kamfanonin shirya finafinai a wannan masana’anta
ta Kannywood, sannan kuma suna rubutawa suna shiryawa suna bayar da umarni.
1. Ibrahim Mandawari
2. Aminu Hassan Yakasai (marigayi)
3. Bala Anas Babinlata
4. Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan
gurasa
5. Ado Ahmad Gidan Dabino
6. Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
7. Abubakar Ishak Zariya
8. Abdullahi Yahaya Mai Zare
9. Bashir Sanda Gusau
10. Balaraba Ramat Yakubu
11. Bala Muhammad Makosa
12. Nura Abdullahi Azara
13. Ibrahim Muhammad Kofar Nasarawa
14. Abba Bature
15. Nazir Adam Saleh
Wasu daga cikin Marubuta Jarumai a
Farkon Kafuwar Kannywood
1. Ibrahim Mandawari
2. Aminu Hassan Yakasai (marigayi)
3. Bala Anas Babinlata
4. Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan gurasa
5. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
6. Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
7. Abubakar Ishak Zariya
8. Nura Abdullahi Azara
9. Hamisu Bature
Mujallun da Suke Bayar da Labarin
’Yan Fim da Marubuta Littattafai
Kamfanin Gidan Dabino Publishers,
Kano, su ne suka fara buga mujalla ta farko a jihar Kano mai suna Zamani, wadda
take bayar da labaru a kan masu yin wasan kwaikwayo da kuma marubuta, a cikin
watan Yuli na shekarar 1994 aka fara buga ta. Wannan mujalla tunanin wasu
fitattun marubuta ne masu sha’awar ci gaban harshen Hausa, mutanen da suka
gudanar da ita su ne Aliyu Abubakar Aliyu da Bala Anas Babinlata da Dan’azumi
Baba Chedyar ’Yangurasa da Balarabe Abdullahi Sani da Farfesa Yusuf Muhammad
Adamu da Sunusi Shehu Daneji da marigayi Aminu Hassan Yakasai (Allah ya
jikansa) da Bashir Sanda Gusau da kuma Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.
Mujallar Tauraruwa ita ce mujalla ta
biyu da aka samar a wannan masana’anta, ta fito ne a watan Janairun shekarar
1999, Sunusi Shehu Daneji ne ya kafa ta.
Sai mujallar Fim da ta fito a watan
Maris, 1999, wadda Ibrahim Shehe ya kafa.
Ado Ahmad Gidan Dabino, MON- ya kafa
mujallat Mumtaz a cikin shekarar 2000.
Wasu Daga Cikin Sahun Farko na
Marubutan da Aka Juya littattafansu Zuwa Fim a Kannywood
1. Ado Ahmad Gidan Dabino- In Da So
Da Kauna
2. Dan’azimi Babba Chediyar ‘Yan
Gurasa- Bakandamiyar Rikicin Duniya
3. Aminu Hassan Yakasai-Madubi
4. Ibrahim Mandawari- Aminu Mijin
Bose
5. Khalid Musa- Kadaura (Hannun Da
Ya Ba Da Kyautar
6. Bala Anas Babinlata- Tsuntsu Mai
Wayo
7. Bala Muhammad Makosa -Halimatu ko
Jummai
8. Adamu Muhammad -Kwabon Masoyi
9. Yusuf Aliyu Lawan Gwazaye-
Cinnaka
10. Sunusi Shehu Daneji- Bankwana da
masoyi
11. Abba Bature - Auren Jari
12. Abdul’aziz Sani Madakin Gini-
Idaniyar Ruwa
13. Aminuddin L. Abubakar (Ala)- Bakar
Aniya
14. Abubakar Ishak - Da Da Kyar Na
Sha
15. Kabiru Ibrahim Yakasai – Suda
16. Auwalu Y. Hamza- Gidan Haya
17. Aminu Aliyu Argungu- Haukar
Mutum
18. Bashir Sanda Gusau - Babu Maraya
Sai Rago
19. Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa -
Ki Yarda Da Ni
20. Balaraba Ramat- Alhaki Kwikwiyo
21. Ibrahim Birniwa- Maimunatu
22. Maje Elhajij- Sirrinsu
23. Ibrahim M. K/Nassarawa Soyayya
Cikon Rayuwa
24. Muhammad .B. Zakari - Komai
Nisan Dare
25. Nazir Adam Saleh -Naira Da Kwabo
26. Zuwaira Isa - Mowar Mata
27. Zilkifilu Mohammed - Su Ma
‘Ya’ya Ne (marigayi)
28. Halima A.D. Aliyu - Muguwar
Kishiya
29. Rabi’u Abdullahi Sharfadi-Halak
30. Dalhatu Ibrahim Basawa-Cizon
Yatsa
31. Kamilu Tahir-Rabi’a
32. Habibu Hudu Darazau – Zafin Nema
33. Lubabatu Ya’u -Yaya Kenan
(Kasko)
34. Ibrahim Mu’azzam Indabawa -
Boyayyiyar Gaskiya (Ja’iba)
35. Sadiya Garba Yakasai- Wake Daya
(Yana)
36. Fauziyya D. Sulaiman- Rumaisa
37. Nasir Umar Ciromawa-Mata Da Kudi
38. Kabir Yusuf Fagge Anka-Kushewar
Badi - Hakkin Miji
Gudmmawara da marubuta suka bayar ba
ta tsaya nan ba kawai, ta gangaro har ga kafa wasu sababbin kamfanoni
sanadiyyar zaman da wasu mutanen suka yi a karkashen wadannan marubuta. Sannan
ta haka ne wasu ma suka zama marubuta a wannan masana’anta, wasu suka zama masu
shiryawa da bayar da umarni, wasu kuma suka zama jarumai, wato sun raini wasu
sun koyawa wasu su ma sun iya.
A shekarar 2003, Ado Ahmad Gidan
Dabino, MON da Bashir Mudi Yakasai sun gabatar da takarda mai taken: Matsaloli
da Nasarorin Masu Shirya Finafinan Hausa Musamman na Kano, an buga takardar a
cikin littafin Hausa Home Videos: Technology, Economy and Society wanda Farfesa
Abdalla Uba Adamu da Yusuf Adamu da Umar Faruk Jibrin suka zama editocinsa. Ana
iya dubawa don samun Karin bayani da kuma ganin yadda marubuta suka bayar da
gagarumar gudummawa wajen samuwar ci gaba da bunkasa da kafuwar wasu kamfanoni
a wannan masana’anta ta Kannywood.
Kuma marubutan nan har yanzu wasu
daga ciki suna wannan masana’antar ba su gudu ba, ko da sun gudu ma suna dawowa
Ina ga idan aka ce kashi 50 cikin
dari na ci gaba da bunkasar da kuma kafuwar wannan masana’anta marubuta ne suka
kawo su, ina ga ba a yi kuskure ba. Allah ne masani. Na gode.
MANAZARTA
Gidan Dabino, A.A, (1995)
Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma,
Takardar da Aka Gabatar a Bikin
Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci. Koko, Jihar Kebbi: Makarantar
Sakandare.
Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar
Adabin Hausa da Addinin Musulunci, Takardar da Aka Gabatar a Taron Kara wa Juna
Sani na Dalibai Musulmi na Babbar Makarantar Sakandaren Dawakin Tofa.
Gidan Dabino, A.A, (1992) Tasirin
Labaran Soyayya ga Al’umma, Musamman ta Hausawa, An Gabatar da Wannan Takarda a
Taron Kara wa Juna Ilimi Mai Taken “Rubutu Don Al’umma’’ Wanda Kungiyar
“Writers Forum” ta Gudanar, a Majalisar Matasa ta Fagge, Kano.
Buba, Malami, Gidan Dabino, A.A,
(2004) Adabi Mai Tafiya: Waiwaye A Kan Fasahar Mai Da Littafi Zuwa Fim. Kano:
Gidan Dabino Publishers.
Yakasai, B.M., Gidan Dabino, A.A,
(2004) Matsaloli Da Nasarorin Masu Shirya Finafinan Hausa Musamman Na Kano.
Kano: Gidan Dabino Publishers.
Hira da Marubuci Bala Anas
Babinlata, 07/06/2020, karfe 7:49 na safe
Hira da Marubuci Almustapha Adam
Muhammad, 07/06/2020, karfe 9:35 na safe