UBANKI YANA GIDA YARINYA
(Gajeren Labari)
Kabiru Yusuf Fagge
Ina zaune a cikin Keke Napep muna tafe, don kai ziyara wajen
abokina Hakimin Wajila, mai suna Iro Mamman, kida ne kawai yake tashi a Napep
din, a wakar Lalakukulala, mai jan Napep din dattijo ne da ya doshi shekaru
hamsin zuwa hamsin da biyar, don ga furfura da gemu nan a tare da shi.
Sai gyada kai yake kamar kadangare, wani lokacin har wani
zabura yake ya kwaso Shoki a waje, sannan ya hankado shi cikin motar, ni kam
kallonsa kawai nake.
A daidai kwanar shiga unguwar Wajilar, wata kyakkyawar
yarinya 'yar birni, mai dauke da shekaru 15 zuwa 16 ta tsayar da mu.













