FASSARA A HARSHEN HAUSA
Kabiru Yusuf
MA’ANAR FASSARA
Fassara asalinta kalmar Larabci, wato aikatau. Ma’anar kalmar a Larabci, ita ce bayanin wani sashe na littafi ko juyar magana daga wani harshe (yare) zuwa wani; wato “tarjamatun”. A taƙaice tafinta ko bayyana ma’anar magana shi ake kira da Larabci “Tarjamah/Tafsir”. Tafsir kuwa, ainihin ma’anarta ita ce bayanin ayoyin Alƙur’ani. Saboda haka ma iya cewa Hausawa sun ari wannan kalma ta fassara ne daga “fassar” ko “Tafsir.”
Bisa wannan za mu iya bayyana man’anar fassara da cewa, hanya ce ta mai da wata magana ko salo ko zance na wani harshe (yare) zuwa wani harshe (yare) ba tare da an sami bambancin ma’ana ba.
Idan ana fassara, ana amfani da wasu ƙa’idoji ne don bayyana ma’ana mafi kusa ko dacewa daga harshe na farko da harshe na biyu ta fuskar ma’ana da salo a maganance, ko kuma a rubuce. Saboda haka, ashe ke nan fassara ba ta samuwa sai da harasa guda biyu (harshen zance) da kuma harshe na biyu (harshen fassara). Haka kuma mafassari dole ne ya kasance mai iya yaruka biyu zuwa sama. Wato, dole mafassari ya zama kanari ko coli wajen iya magana da harasa. Dalili shi ne, mai iya magana da harshe (yare) ɗya ba ya iya fassara, sai dai ya yi ƙarin bayani.
Misali, a cikin harshe guda, ana iya samun wata magana dunƙulalliyaa cikin salo na hikima kamar karin magana ko zaurance ko azanci, waɗanda suke buƙatar ƙarin bayani domin a fahince su.
Fassara tana da manyan rabe-rabe guda biyu waɗanda suka haɗa da; fassarar ilimi da fassarar adabi
1. Fassarar ilimi: ita ce wadda ta shafi kimiyya ko kuma addini. A nan duk abin da aka rubuta ta sha’anin ilimi, ƙoƙari za a yi a zuba mata ƙa’idoji ko a ba ka labarin wani abu kai tsaye kawai ba wani sanabe ko ado ko ƙaƙale. Wato dai a faɗi gundarin gaskiya abu yadda yake. Haka kuma, ana amfani da kalmomi tare da zaƙin murya na baliganci ko tsoratarwa ga abubuwan da suka shafi harkokin addinin domin jama’a su tsorata ko himmata wajen abin da ake son su yi ko su bari.
2. Fassarar adabi: ita wannan fassarar ta adabi kuwa, ita ce wadda ake so a faɗi wani abu da aka rubuta ko aka faɗa da salo na sanabe ko ƙaƙale, wani lokaci ma akan so a faɗi abu ɗaya da ma’anoni biyu ko fiye, yadda in an tashi takura mai faɗa ta nan sai ya ɓullo ta can ya ce, ai ga abin da yake nufi in an zo fassara irin wannan, dole ne a yi ƙoƙari a ƙaƙale da salo na kurɗa-kurɗa da za a iya, har ma inda dama a yi wa fassarar baki biyu in ana iyawa.
NAU’O’IN FASSARA
Babban abin da ake nema a fassara, shi ne fahintar abin da harshe na biyu ke magana kamar yadda ma’anarsa take a harshe na farko. Abin nufi a nan dole sai an fassara komai daidai sannan za a sami fahintar abu sosai. Saboda haka ashe ya zama wajibi mai fassara ya fahinci abin da yake fassarawa, don in bai fahinta ba, ba zai yiwu ya yi fassara ingantacciya yadda abin yake ba, wanda yin hakan shi ke sa ma’ana ta canza a kuma haddasa rashin fahinta ga masu karanta fassara ko saurare saboda ganin irin wannan ne a wani ra’ayi aka rarraba fassara zuwa kashi-kashi kamar haka:
(1) Fassarar Kalma Da Kalma/ Jimla Da Jimla
Ana yin fassarar kalma da kalma ko jimla da jimla kamar yadda yake a cikin harshen farko zuwa harshe na biyu ko da babu ma’ana.
Wani lokacin kuma ana ɗaukar kowanne sakin layi ne abin da ake so a fassara ba ta kalma da kalma ba, wato akan yi ne gwargwadon abin da sakin layi ya ƙunsa.
Misali: Good morning =Kyakkyawar safiya
A Hausa an ce: “Naira bibiyu ne kowanne”
“Two-two naira each”, maimakon “two naira each.”
Saboda haka irin wannan fassara a wani lokaci ba ta da daɗin karatu a wajen mai karantawa, kuma fahintar ma’anarta kan jirkita.
(2) Fassara Mai ‘Yanci
Fassara mai ‘yanci ita ce wadda za a yi bisa fahintar abin da aka karanta na cikin harshe na farko. Wato wannan fassarar, harshen da mai fassara ya karanta kuma ya fahinci abin da ake nufi, sai shi kuma ya rubuta cikin harshen da yake fassara mafi sauƙi yadda za a fahinta. Wato mai fassara na da ‘yancin faɗin abin da ya ga dama muddin dai ya bayar da ma’ana kamar yadda yake a harshe na farko.
Ita wannan fassara tana buƙatar lura ainun don gudun kada a yi ƙari ko ragi wanda bai dace ba a cikinta, kodayake dai ana iya taƙaita ta ko a tsawaita ta, amma dai fassara ce mai tara dukkan ma’anar abin da ake fassarawa.
(3) Fassarar Harshe Da Wani Harshe
Wato ita wannan fassarar, a wani lokaci akan sami mutum yana magana da wani harshe sannan kuma wani ya fassara maganar mutumin nan da wani harshe. Wannan irin fassarar na samu ne wajen magana a taro, inda wasu ba sa jin harshen wasu kamar yadda ake yi a majalisar ɗinkin duniya ko shugabannin ƙasashe ko kuma manyan jami’an diflomasiyya. Irin wannan fassara ita ake kira “Tafinta.”
MUHIMMANCIN FASSARA
(a) Ana fassara don kyautata danganatakar al’ummomi daban-daban
(b) Ana fassara littattafai don a haɓaka harkokin ilimi
(c) Ana fassara don wayar da kan al’umma
(d) Ana fassara don yaɗa manufofin gwamnati ko hukuma
(e) Ana fassara don haɓaka arziƙin ƙasa ta sanin wasu asiran ƙere-ƙere da hanyoyin kasuwanci
(f) Ba wa ɗan’adam damar laƙantar harasa da dama
ƘA’IDOJIN FASSARA
Akwai hanyoyi da ƙa’idoji da ya zama wajibi mai fassara ya bi su domin a fahinci saƙon da yake son isarwa ga jama’a. Waɗannan ƙa’idojin sun haɗa da:
(1) Mai fassara ya san manufar batu. Shin ya shafi kimiyya ne ko fasaha ko kuma kasuwanci?
(2) Mai fassara ya laƙanci harasan da zai yi fassara da su.
(3) Mai fassara ya san kalmomi da ma’anoninsu, musamman gama-garin kalmomi, irin su hannu, baki, ƙafasa, kai da sauransu.
(4) Sanin bambancin al’adu, domin harshe da al’adu Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Misali ƙanƙara da dusar ƙanƙara.
(5) Sanin kalmomi masu harshen damo, misali kamar a ce “jirgi” a nan jirgin na iya zama “jirgin sama” ko “na ruwa” ko na “ƙasa.” Da sauransu
(6) Mai fassara ya daidaita harshe, kuma ya san irin karin da zai yi amfani da shi domin a fahince shi da zarar ya ambaci kowacce irin kalma.
(7) La’akari da fifikon ma’ana a fassara wajibi ne, misali:
Good morning:
Kyakkyawar safiya Barka da asuba Ina kwana
(8) La’akari da mutanen da ake yi wa fassara shi ma wajibi ne. Ana so mafassari ya yi la’akari da basira da ilimi da shekaru na mutanen da yake yi wa fassara.
(9) Mai fassara ya yi fassara cikin daidaitacciyar Hausa ba cikin furucin Kananci ko Zazzaganci ko Katsinanci ko Dauranci ko Sakkwatanci ba. Haka kuma kada ya yi fassara cikin Ingausa.
(10) A yi la’akari da canza sigar jimloli domin su dace da harshen fassara. Kowane harshe da tsarin jimlolinsa. Misali a Hausa ana iya amfani da suna ko wakilin suna a jimla ɗaya, amma a Turanci haka ba ta faruwa. Misali: (a) Ado went to Kaduna. =Ado ya tafi Kaduna. (ba; Ado tafi Kaduna ba)
(b) He bought twelve cars. =Ya sayo motoci sha-biyu. (ba; Ya sayo sha-biyu motoci ba.)
(11) Ya zama mai bincike da neman cikakken bayanai game da ma’anar kalmomi tsofaffi da kuma sababbi.
(12) Mai fassara ya zama mai bin ƙa’idojin rubutu kamar yadda ƙa’idar harshe yake fassarata a ajiye. Misali: shi ne ba shine ba, ita ce ba itace ba, kowane ba ko wane ba, za a ba za’a ba da sauransu.
MATSALOLIN FASSARA A HARSHEN HAUSA
Harasa suna da hanyoyi da ba ƙayyadaddu ba, kuma rashin ƙayyadewa bisa abin da ya kamata a ce kaza a wannan harshe shi ne kaza a wancan harshen, shi ya kawo akasarin bambance-bambance a tsakanin harsuna. Taƙaitar wannan bambancin kuwa shi ne samuwar tsatso da asali da kuma cuɗanya tsakanin harasa.
Ire-iren wannan shi kan sa mutum ya iya yin kuskure, wato cewa ba ya yiwuwa a fassara zance daidai-wa-daida, wato ba ragi ba ƙari, haka kuma gwargwadon nisantar harasa gwargwadon salwatar manufa da ma’ana, amma duk da haka za a iya fassara zance ta hanyar tsantsar kalmomi ba damuwa da dangantakarsu ba.
Idan aka duba ‘yan shekarun baya, duk wanda ya liƙewa harshen Hausa, alhali ga ‘yan birni da ma’aikata tare da ‘yan makaranta kowa sai hanƙoro yake ya ji ana “yes, yes, no, no” to zai sha wuya, domin kuwa kallon biyu-ahu zai yi masa. Amma Allah da ikonsa, harshen Hausa ya sami wani matsayi na gogayya da wasu manyan harasa. Wannan shi ya sa ake ƙoƙarin gwada kalmominsa da nasu. Saboda haka wannan ya nuna ba wai a yanzu ne matsalar fassara ta fara ba, a’a tun lokacin da mutanen wata ƙasa suka fara kutso mana ne muka fara cin karo da waɗannan matsaloli:
1- Rashin Damuwa da kiyaye dangantakar da baƙuwar kalma take da ta Hausa;
2- Rashin sanin ita kanta baƙuwar kalma, balle a san ‘yar’uwarta a Hausa.
3- Rashin sanin kalmomin Hausa yadda za a ce ga ‘yan’uwansu a cikin baƙin kalmomi.
Waɗannan su suka sada arar wata kalma ta zo sai kawai mutane su bar harshen ya haɗiye ta don zafin da yake da shi, sai ka ga Hausar ta ainihi ta ɓace. A wannan magana da muke yi, akwai alamomi da yawa da muka ara waɗanda idan aka tsaya aka bincika za a iya gano ainihin takwarorinsu na Hausa domin kuwa akwai irin waɗannan kalmomi birjik a cikin adabin zamani, sai dai kula da rashin saninsu suka haddasa wannan. Wato, sai ka ga mutum wanda ya kamata ya fassara wata kalma, amma ƙuiya da rashin sani ya sa ya tsallake ta, kuma ya rafkana wajen fassarar ta, haka kuma za ta zauna har ‘ya’ya da jikoki.
Harshen Hausa ya fara cuɗanya da baƙin harasa. Cuɗanyar da ya yi a nan gida ita ce wadda ya yi da dukkan harsunan Najeriya. Amma waɗanda aka kawo tsaraba su ne Turanci da Larabci da kuma Faransanci da sauransu.
Saboda haka, idan har ana son gano yadda baƙuwar kalma kan shiga cikin wannan harshen na Hausa, dole ne a ɗauki wani baƙon harshe a yi amfani da shi. Alal misali; Larabci ya shigo ƙasar Hausa ta hanyoyi guda biyu, wato dalilin kasuwanci zuwa ƙasashen Larabawa kamar irin su Libiya, Sudan, Mali, Maroko da sauransu. Sannan kuma ta dalilin zuwan addinin Musulunci. Malamanmu na da, idan suna karatu sai su riƙa ƙyale wasu kalmomin Larabci suna tsunduma su cikin Hausa, maimakon su fassara su, amma saboda ƙuiya da rashin sani ya sa kalmomin ke yi wa harshen Hausa kane-kane, misali;
Larabci Hausa
Arziƙi maimakon wadata
Shagala maimakon mantuwa
Ilimi maimakon sani
Waɗannan kalmomi a koyaushe za ka ji malamai suna faɗarsu, kuma haka ake rubuta su. Haka abin yake faruwa da kalmomin Turanci waɗanda suka yi wa harshen Hausa kane-kane;
Turanci Hausa
Kwandem maimakon la’ana ko suka
Dameji maimakon lalacewa
Coci maimakon majami’a
Matsalar fili da lokaci ke haddasawa cikin jaridu. Abin nufi a nan shi ne, filin da za a sa Larabci da yawa kan jawo taƙaita fassara ko faɗaɗata. Matsalar lokaci kuwa ta shafi lokacin da aka ƙayyade wajen shirya jarida da lokacin da ake so a buga ta tafi don sayarwa ga jama’a.
Don haka ƙarancin lokaci da fili kan sa a yi wa labari yanka a yi aya a wurin da bai dace ba, ko kuma cire wani sashe da ba shi da muhimmanci.
SHAWARWARI GA MAI FASSARA CIKIN HARSHEN HAUSA
Duk mai fassara cikin harshen Hausa ta kowace irin hanyar sadarwa ga jama’a dole ne ya kasance ya yi la’akari da waɗannan shawarwari:
1. Dole ne ya kasance ya san harshen da yake so ya fassara da Hausa.
2. Dole ne ya san harshen Hausa, yadda zai iya gane kalmominta da kuma baƙin kalmomi.
Dangane da sigar Nahawu, kowace hanya aka bi sai an sami canji da ya shafi shigar Nahawu. Alal-misali; A Hausa za a iya haɗa suna da wakilin suna a cikin jimla guda, wanda Turanci bai yarda da wannan ba. Misali; Ado ya zo. Amma a Turanci sai dai “Ado come” ko “He came,” ba “Ado He came” ba.
Ta fuskar kalmomi da ma’anoninsu kuwa, ana la’akari da makusanciyarsu mafi dacewa, domin mutum zai haɗu da kalmomi gama-gari, misali; hannu, ƙafa, kai da sauransu da kuma kalmomi masu manufa ɗaya, amma suna da bambancin al’adu misali kamar “fari” da kuma “fat”. Sai kuma kalmomin da suke nuna zurfin ƙwarewa, misali;
Teargas =Barkonon tsohuwa
Senate =Majalisar Datijai
Salon zance da karin magana, kyawawan misalai ne da za mu iya amfani da su ta wajen irin juye-juyen da za mu iya yi wajen fassara. Idan mai fassara ya ci karo da salon ma’ana akwai abubuwa uku da zai iya yi;
(1) Salo zuwa salo
He is second to none;
Ba shi da na biyu.
(2) Juya ma’anar sarari zuwa salon zance.
Pride begets the turban of poverty;
=Girman kai rawanin tsiya
(3) Salon zance zuwa ma’ana sarari.
He was alarmed;
=Girmansa ya faɗi (ƙarin gishiri)
HANYOYIN MAGANCE MATSALOLIN FASSARA
Idan muka duba abubuwan da aka zayyana a baya dangane da matsalolin fassara, sai mu ga ita kanta matsalar fassara ba ta masu sadarwa ga jama’a ce kaɗai ba. Wannan matsala ce ta gwamnati wadda ya zama tilas a gare ta ta tashi tsaye wajen bai wa harsunan ƙasar nan wani matsayi da ya dace da su.
Hausawa sun ce, hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Saboda haka hanyoyin magance matsalolin fassara yanzu ta zama ta fassara da masu amfani da harshen.
(a) Masu fassara su san cewa fassara cikin harshen baka tana da fifiko kan fassara cikin rubutaccen zance.
(b) Masu fassara su san cewa maganar mutanen da ake yi wa fassara dangane da matsayinsu tana da fifiko kan fassara da ta fi yawan jama’a/mutane.
(c) Masu fassara su zama masu yawan gudanar da bincike akai-akai da kuma yawan halartar taron ƙarawa juna sani.
Manazarta
Tuntubi marubucin
No comments:
Post a Comment