‘YA’YA BIYU
(Family Planning
Saga)
Muna zaune ni da
budurwata Nabila, muna hira. Ta dube ni, tare da tambaya ta.
“Yau babu wani
sharaɗi ko shawarar na ji ka yi shiru?”
Na bi ta da
murmushi.
“Kamar kin shiga
raina, yunƙurin nan da kika ga na yi, zan gaya miki ne, sai kika tambaya.”
“To ina
sauraronka.” Tana murmushi take maganar.
“Nabila, a
rayuwata ina son ‘ya’ya, amma
maganar gaskiya ina son shekaru goma sha biyar ɗin farkon aurenmu mu haifi
‘ya’ya biyu kawai.”
Ta kalle ni da mamaki a idonta.
“Na san kana da
hujja, amma ko za ka iya gaya min tare da ƙarin bayani. Iya sani na, Allah ne
mai yi ga rayuwar halittunsa, amma ta ya za mu yi haka?”
“Good, Nabila
kaso tamanin na rayuwar ɗan’adam tana hannunsa, tun da Allah ya yi mu mutanen
ya ba mu hankali da tunani da ilimi, don haka tsara haifar ‘ya’ya biyu a cikin
shekaru goma sha biyar zuwa ashirin abu ne mai sauƙi.”
“Na ji wannan, saura dalili.” Ta ce da ni.
“Lafiyar ki, da
tarbiyantar da ‘ya’yan da ɗora su a kan kyakkyawar rayuwa gwargwadon iyawarmu
da biyan haƙƙoƙinsu har su hau kan gwadaben rayuwa mai inganci. Sannan sai a
nemi wani ko wasu, su ne
dalilaina.”
Ta yi shiru,
kafin ta numfasa.
“Na ɗauka Allah
ne mai shiryarwa da bai wa ɗan’adam abinci da arziƙinsa tun daga lokacin da
yake halittarsa?” Ta tuhuma.
“Allah shi ne mai
shiriya, amma bisa mataki-mataki ciki har da wanda ya ɗora wa iyaye na haƙƙoƙin
ci da sha da tarbiyya.” Na numfasa, “Nabila komai da kika sani Allah ya yi shi
bisa sanadi, sanadin shi ne iyaye su kula da abubuwan da na lissafa miki, idan
suka gaza da gangan sai Allah ya kama su. Ai Allah shi ne mai halitta, me ya sa
bai ce idan aka Haifa, a watsar da su za su tashi da tarbiyya, za su ci, su sha
su tufatu daga sama ba, ya bai wa iyaye alhakin tarbiyyar? Saboda haka tsarinsa
yake.”
Yayin da na yi
shiru, ta dube ni tana son yin tambaya, ta kasa, na ɗora da cewa.
“Don haka, Nabila
muna buƙatar mu yi wannan aikin idan mun yi aure, Allah ya ba mu haihuwa, mu
sami ‘ya’ya biyun mu yi namu aikin, Allah ya yi na shi.”
Ta yi ajiyar
zuciya.
“Na gamsu da
bayaninka Habib.”
Bayan aurenmu, a
cikin shekaru uku Allah ya ba mu ‘ya’ya biyu mace; Fatima da namiji Muhammad
(Al’amin)
Muna cikin
shekara ta huɗu da aurenmu, da ‘ya’yanmu guda biyu cikin farin ciki da kula da
soyayya da nutsuwa, a gidan kaina nake, madaidaici ne mai ɗakunan Nabila da
falonta, ni ma nawa ɗakin da falo, da ɗakin saukar baƙi, haka su ma yara kowa da
nashi ɗakin da banɗakuna daban-daban. Motata ta kai miliyan biyu da rabi.
Harkar siyar da
shaddodi da yaduka su ne kasuwancina. Ina kula da ‘yan’uwana da na Nabila
gwargwadon iyawa ta.
A wannan shekarar
ne ‘yan’uwan Nabila da iyayenta mata suka fuskanci ta tsallake shekaru biyu ba ɓatan
wata, ba ɓari ba ciki. Take suka sa ƙahon zuƙa sai da suka gano jinkirin
haihuwa muke yi.
Watarana ina ɗakina
a zaune, Maman Nabila; Baba
Gambo da yayarta mai suna Atuwa suka zo gidan, ban yi tsammanin sun san ina nan
ba, na ji suna hira, suna ɗaga murya.
“Ke muke saurare,
gaya mana abin da ya sa kuke yin family planning?” cewar Baba Gambo.
“Gaskiya tun
kafin aure mun yi wannan yarjejeniyar da shi. Kuma ni ina ganin ba wani abu ba
ne...”
Atuwa ta katse
ta, “Ke sakarya, kya ce ba wani abu ba ne mana, tun da an ninke ki baibai. To
tsaya ki ji in gaya miki gaula ya mayar da ke. Kina nan zaune da ‘ya’ya biyu
zai ƙaro aure har biyu, ke har uku ma, ai haka mazan yanzu suke, su mayar da
mace shashasha, su banka miki maganin rashin haihuwa, ki zauna da ‘ya’ya biyu
ko uku, shi kuma ya je, ya yi ta aure, ya more rayuwarsa, tun da ba ‘ya’ya da
yawa a gabansa.”
Baba Gambo ta karɓa,
“To bari in gaya miki, mazan yanzu ‘ya’ya ake juye musu, kamata ya yi, shekaru
biyar kina da ‘ya’ya shida, a lokacin da kuke shekaru goma da aure kina da
‘ya’ya goma ko sha ɗaya, idan ya ga yawan ‘ya’yan ba zai iya tunkarar wata
shegiyar ‘yar da neman aure ba, ke ko ita yarinyar duk tsiyarta idan ta san
yana da ‘ya’ya da yawa ba za ta shigo miki gida a matsayin kishiya ba, don za
ta ce rainon ‘ya’ya za ta zo yi masa a banza...”
A daidai lokacin
na yi sallama, na shiga falon, suka yi tsuru-tsuru suna kallona, na gaishe da
Baba Gambo, ta amsa ciki-ciki. A sanyaye na fara magana.
“Baba wannan abin
da kuke magana a kai ba haka ba ne a raina, ban taɓa tunanin zan ƙara aure ba,
sai dai abin da Allah ya nufa, bare in sa Nabila ta yi tazara saboda wannan abu
da kuke tunani. Mun yi haka ne don lafiyarta da inganta rayuwarmu. Batun aure
kuwa, ya kamata ku sani idan na so ko ‘ya’ya ɗari gare ni, akwai ‘yanmata da
yawa da za su iya aure na a haka. Ni da Nabila muna son juna, muna son mu rayu
har abada a cikin kyakkyawar rayuwa, don haka babu wannan abu da kuke magana...”
Har na gama
maganganuna na fita ba su tanka min ba. Ashe dai baya na bari da ƙura don kuwa
maganganun da na faɗa musu ko a jikinsu, haka suka zuge Nabila tas!
Watarana ina zaune
a falo, ta shigo rai a ɓace.
“Ya aka yi abar
ƙaunar?” Na ce da ita. Ta kawar da kai.
“Habib ba zan
ƙara yin tazarar haihuwa ba, don yana sa ni rashin lafiya. Yana rikita min
al’ada ta.”
Na san ƙarya take
yi, na yi ta lallashinta, amma fafur ta ƙi. Da na ɗan nuna mata ɓacin rai sai
ta nuna kamar ta haƙura, ashe yaudara ta za ta yi, sun ƙulla mata abin da za ta
yi idan na matsa.
Wata na gaba sai
ga Nabila da ciki. Da na yi magana sai ta ce Allah ne ya yi ikonsa, ni kuma na
san ƙarya take, ƙin shan maganin ta yi. Lokaci na yi ta haifo ‘yar da muka sa
wa suna Zulaiha.
Muka ƙara hawa
teburin tattaunawa, na nemi ta yi allura, ta ce sai dai ta sha magani. Da na
nemi matsa mata a kan ta yi allurar, ta bijire min tare da yunƙurin yin yaji,
dole na haƙura, na yarda ta sha maganin.
Aka kuma
maimaitawa. Ta sake yaudara ta, ta ƙi shan maganin. Wannan karo namiji ta haifa,
sunan shi Shamsu. Cikin shekaru bakwai muna da ‘ya’ya huɗu.
Na sake nuna mata
ɓacin raina sosai, a kan lallai sai ta yi allura, ta yarda aka yi mata wadda za
ta yi wata uku. Bayan cikar wata ukun, na tuna mana lokacin sake yi ya yi, sai
ta tubure cewar waccan allurar ba ta sake ta ba, wai ta tabbatar ba za a sami
ciki ba, don haka ba za ta sake yin wata allurar ba.
Nan ma dai ciki
ya bayyana. Wata takwas ta haifo Naziru. Muka kai ruwa rana wajen a sa mata abin
tazarar na hannu, da ƙyar ta yarda aka sa. Ashe daga baya ta koma wani asibitin
sun cire mata.
A cikin
shekararmu ta goma sha biyu da aure muna da ‘ya’ya tara.
Sai wane babi,
dole na saduda, ba don Allah ba, sai don yadda rayuwa ta bida ni. Abubuwa suka
sakwarkwace, saboda:
Ban ninka samu
ba, amma buƙatu sun ninku sun ruɓanya har sau biyar ko fi a kaina. Abinci,
abubuwan buƙatun gida, harkar makarantun yara, babu abin da bai ninku ya ƙara
ba.
Kafin wani lokaci
jarina ya yi ƙasa sosai saboda tsadar kayan masarufi da na buƙatunmu. Na siyar
da motata, don biyan kuɗin makarantar yara da siyen kayan abinci. Da tafiya ta
ƙara nisa na siyar da gidan da muke ciki, muka koma gidan haya.
A yanzu, watanni
sun ƙaru, mun ƙara samun ‘ya’ya biyu sun zama su sha ɗaya, da ni da ita mu sha
uku ke nan. Rayuwarmu kacokam ta koma kan gwadaben ƙarma-ƙarma.
Na je ga Nabila
ina duban ta. Zan yi magana, ta fashe da kuka.
“Kukan me kike
yi?”
“Na san abin da
za ka faɗa. Kuma tabbas ni ce sila, na kauce wa gaskiya ga halin da muka faɗa.”
Na zauna.
“In ƙara maimaita
miki, kaso tamanin na rayuwar ɗan’adam tana hannunsa. Allah ya yi masa komai tun
da ya ba shi abubuwa guda uku; hankali da tunani da ilimi, sannan halak ne
tsarin iyali a Musulunci. Allah zai tambayi duk wasu iyaye a kan ‘ya’yan da
suka haifa, idan ka san akwai matsala, to kar ka haifa, hatta auren ma ba tilas
ba ne a kanka idan akwai matsala.”
“Ni ganau ce ba
jiyau ba Habib. Ko kana da damar ɗaukar ɗawainiyar wasu, idan suka yi yawa ba
za ka iya ba. Yanzu me ya kamata mu yi.” Tana hawaye.
Muka yi shiru,
muna duban juna.
Na gama
Kabiru Yusuf
Fagge (Anka)