Saturday, April 11, 2020

GASAR GUSAU INSTITUTE KADUNA, KARIN LOKACI

*KARIN LOKACIN TURO DA TSAKUREN LABARI NA GASAR MARUBUTA HAUSA NA ALIYU MOHAMMED RESEARCH LIBRARY, GUSAU INSTITUTE (GI) KADUNA*
Biyo bayan bullar cutar Covid-19 watau corona virus a fadin duniya. Hukumar Gusau Institute sun kara lokacin turo da tsakuren labaran masu sha’awar shiga wannan gasa, zuwa 31 ga watan mayu na 2020 (31 May 2020), domin bama sauran marubuta daman turo da tsakuren labarin su.
Cibiyar Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute (GI) Kaduna ke shirya wannan gasa, da kuma ba da kyaututtukan kudade domin tallafawa marubutan adabin Hausa.
Gasar da ake yin ta a kowace shekara, tana daukar siffa da tsari na kagaggun labarai ko wasu irin labaran adabin Hausa.

Friday, April 10, 2020

MISALAI DA BAMBANCEN-BAMBANCEN KARE-KAREN HARSHEN HAUSA




Rubutunka Tunaninka
MISALAI DA BAMBANCEN-BAMBANCEN KARE-KAREN HARSHEN HAUSA

Kabiru Yusuf
 
Da farko, bari in kara tuna mana tsarin yadda Hausar take ta haka za mu iya bambance yadda Hausar kowanne bangare;
(1) HAUSAR GABAS: su ne; Kananci, Bausanci, Zazzaganci, Kudduranci/Gudduranci, Hadejanci
(2) HAUSAR YAMMA: su ne; Sakkwatanci, Kabanci, Gobiranci, Zamfaranci
(3) HAUSAR AREWA; wadda ta hada da: Dauranci, Gumalanci, Katsinanci, Damagaranci Da sauransu.

KARIN HARSHE DA DAIDAITACCIYAR HAUSA
Yanzu bari mu dubi misalan yadda wasu kare-karen harshe suke da kuma yadda suke a daidaitacciyar Hausa:
"TS"
Kare-karen Yamma                 D/H
Tcimi                                       tsimi
Hatci                                       hatsi
Tcere                                       tsere
Watce                                      watse
Rantcatce                                rantsattse
(a lura wajen furta "ts" sai su furta "tc")

MUSAYAR KWAYOYIN SAUTI
A nan ana nufin yadda wasu suke amfani da wata kwayar sauti madadin wata.
Sautin "h" maimakon "f"
Yamma                        D/H
Hwata                         fata
Kahwa                         kafa
Sassahe                        sassafe
Hili                              fili
Laihi                            laifi

A dangin Dauranci kuwa "sh" mai wasalin "i" ko "e" ita ke zama "h". Mai wasalin "a" kuwa tana zama "hy" ne, kamar haka:
Dangin Dauranci                     D/H
Hirwa                                      shirwa
Farahi                                      farashi
Hekara                                     shekara
Tahe                                        tashe

Hyakka                                    shakka
Hyayi                                      shayi
Hya'ani                                    sha'ani
Hyahyanci                               shashanci

Bayan haka, dangin Dauranci, wani lokaci ma har da wasu kare-karenn yamma, sukan dauri "I" maimakon "r", kamar haka:
Dangin Dauranci                     D/H
Galgadi                                   gargadi
Halbi                                       harbi
Kalkashi                                  karkashi
Malka                                      marka
Walwala                                  warwara
Zalbe                                       zarbe

*A Bausanci, "c" mai wasalin "i" tana zama "sh", kamar haka:
Bausanci                      D/H
Shiki                            ciki
Shitta                           citta
Shigiya                        cigiya
Binshike                      bincike
Dagashi                       dagaci
Takaishi                       takaici

Idan muka dan bi wadannan misalan za mu ga yadda wasu suke furta wasu kalmomi, ke nan idan marubuci yana son ya bambace wa mai karatu, tauraro Basakkwace ko Bakano ko Bakatsine ko Badamagare ko Bagumule ko Badauri ne yana bukatar furucin da ya shafi karin harshensa, ba kawai ya ce tauraro kaza Basakkwace ne amma Hausarsa ta Gumel ko ta Katsina da sauransu.

KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA
Ci gaba/Cigaba
Ta farko ta zo ne a matsayin aiki, wato don haka a rabe take zuwa. Misali:
*Zo ka 'ci gaba' da yin wannan aikin.*
Ta biyu kuma a matsayin suna take, don haka a rabe take zuwa, misali:
*Lallai na yarda an samu 'cigaba' a darasin nan."

Farinciki/farin ciki
*Farinciki* a nan suna ne, misali:
*Kodayaushe yana cikin farinciki da annashuwa.*
*Farin ciki* wannan kuwa, sifa ce ko aiki
*Za ka yi farin ciki idan ka samu.*
*Daliban suna ta farin ciki da samun nasarar.*

Bakinciki/Bakin ciki
 Hukuncinsu daya ne da farinciki/farin ciki


Shikenan
Shikenan; na nufin an kammala abu, ko abu ya kammata. Misali:
1- *Ai shikenan tun da ka siyar.*
2- *Shikenan je kawai.*
3- *Ai shikenan, sai mu tafi ko."
4- *Kurunkus, shikenan.*

Shi kenan
Kalmar *shi* wakilin suna ne na mutum namiji, misali:
*Shi kenan kullum cikin ciye-ciye.*
*Wai har yanzu rigima yake?" "E mana, shi kenan cikin rigima a kullum."

Manazarta:
Bunza, A.M. (2002) "Rubutun Hausa: Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa. Don Masu Koyo Da Koyarwa." Ibrash Islamic Publications Centre LTD., Surulere, Lagos.
Indabawa, I.M da Fagge, K.Y (2000) Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai." Gimbiya Publishers, Fagge, Kano.
Zarruk, R.M. da wasu (2010) "Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Don Kananun Makarantun Sakandire." Ibadan Press Plc, Ibadan Nigeria.
Yahaya, I.Y. () "Darussan Hausa: Don Manyan Makarantun Sakandare." University Press, Plc.

MOWAR MATA & SIRRIN MALLAKAR MAIGIDA COVERS



RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...