Saturday, February 15, 2020

2020: GASAR MARUBUTA HAUSA NA ALIYU MOHAMMED RESEARCH LIBRARY, GUSAU INSTITUTE (GI) KADUNA, NIGERIA




GASAR MARUBUTA HAUSA NA ALIYU MOHAMMED RESEARCH LIBRARY, GUSAU INSTITUTE (GI) KADUNA, NIGERIA
Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute (GI) Kaduna, wata cibiya ce da General Aliyu Muhammed Gusau ya assasa, wannan cibiya tana shirya gasar marubuta cikin harsuna daban-daban musamman ma harshen hausa. Makasudin shirya irin wannan gasar shi ne, don habaka al’adu da kyawawan dabi’u na bahaushe.
 
Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute (GI) Kaduna ke shirya wannan gasa, da kuma ba da kyaututtuka don kara kaimi ga sababbin marubuta adabin hausa.
Gasar da ake yin ta a kowace shekara, tana daukar siffa da tsari na kagaggen labari ko wasu labaran.
Ga masu son shiga wannan gasar, ana bukatar marubuci ko marubuciya da su kiyaye da wadannan ka’idoji ko dokoki kamar haka:
1.      Ana bukatar marubuta su aiko da tsakuren labarinsu shafi goma, kada ya wuce shafi goma.
2.      Duk marubuci ko marubuciya da basu kai shekara sha takwas ba, ana bukatan izinin iyayensu.
3.      Ba a yarda wani ko wata daga cikin ma’aikatan Gusau Institute ko danginsu su shiga wannan gasa ba.
4.      Ba a karbar wani rubutun da aka bugawa ko kuma ya fita a matsayin littafi, ko aka taba karantawa a daya daga cikin kofofin watsa labarai.
5.      Ba a yarda da satar fasaha ba ta hayyan yin amfani da rubutun wani.
6.      Za a turo da tsakuren aikin ne daga farkon watan Janeru zuwa karshen watan mayu, sannan mutanen da aka zaba, za su turo da sauran gundarin aikin a karshen watan Yuly zuwa karshen watan satumba.
7.      Labarin da bai wuce kalmomi dubu arba'in (40,000) zuwa arba'in da biyar (45,000), kuma rubutun ya zamana na mutum daya ne ba hadaka ba.
8.      Alkalai za su yi la’akari da kyawun harshen, zube da kuma tsari da marubuta sukayi amfani da shi.
9.      Duk wanda ya shiga wannan gasar, to ya kwana da sanin cewa duk abinda alkalan gasar suka zartar shi ne daidai kuma babu daukaka kara.
10. Za a turo da tsakuren labara zuwa ga wadannan adireshi kamar haka:
            i.      Email: info@gusauinstitute.com,   gusau.institute@gmail.com
                 ii.      WhatsApp Number: +2347087808036
11. Za a turo da cikakken suna, kwanan wata, ID Card Mai dauke da hoto da kuma cikkakken adireshi.
12. Duk labarin da aka turo, an turo kenan, babu hurumin canza wani fasali ko tsari na littafin da aka tura
13. Ba’a turo da rubutun hannu.

Mungode.
https://ssl.gstatic.com/ui/v1/icons/mail/profile_mask2.png
Mohammed Isah Suleiman


1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...