CAKIN FOYIN (Checking Point)
Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Malam Tukuro Cakin Foyin yana zaune kan tsohuwar kujerarsa da mutanen
unguwar suke kira da bugun Koje Masassaki saboda tsananin tsufanta, ban
da tsananin dauda da ta yi saboda zama har tankwarewa ta yi ta yadda
kullum idan Cakin Foyin zai zauna a kanta sai ya tokareta da dutse.
Wasu sun ce sama da shekaru arba'in da tara da aka sassaka kujerar nan
kullum sai Cakin Foyin ya yi zaman sama da awa bakwai zuwa takwas a
kanta, don haka dole ta jigata.
Tsananin zaman sa ido ne ya sa aka
sa wa Malam Tukuro suna 'Cakin Foyin' saboda duk wanda ya zo wucewa sai
Malam Tukuro ya lalube shi da idanu, musamman mata. An ce yakan iya
sanin adadin mata da maza, yara da manyan da ke wucewa ta hanyar a
kullum, kuma ya san iya adadin kayan da kowa yake sawa na yau da gobe,
don wasu matan ma hatta dan kamfan da suke sawa Cakin Foyin ya sani. Ya
haddace irin tafiyar kowa, ya san masu yi masa magana idan sun zo
wucewa, ya san masu yi masa kallon banza ko tsaki.
Haka nan ya san adadin ababen hawan da suke wucewa, kana yana gane baki da kuma masu wucewa yau da kullum ta hanyar.