Sunday, December 14, 2025

AN HORAR DA MARUBUTAN KANNYWOOD









MARUBUTAN KANNYWOOD 


Ranar Asabar 13-12-2025 aka gudanar da horo (training/workshop) ga marubuta 53 na masana'antar Kannywood wadda ta guda a ƙarƙashin Nigeria Film Corporation wadda Dr. Ali Nuhu yake jagoranta.


Horon ya gudana ne domin ƙara ƙwarewar wasu marubutan tare ƙyanƙyashe sababbin marubuta a masana'antar.


An gudanar da horon a ɗakin taro na Sarari Media and Telecommunications Hub da ke kan titin jami'ar Northwest Kano. 

Ƙwararrun malamai masana rubutun fim daga tashar Arewa 24 kamar Nazir Adam Salih da Fauziyya D. Sulaiman da Zuwairiyyah Girei da Nasir NID su ne, suka bayar da wannan horo.

Yayin da Kabiru Anka da Nura Nasimat suka kasance masu kula da gudanar da horon.

Bayan kammala horon, an bayar da gwaji don tantance marubutan tare da ba su shaidar kammala ɗaukar horo.

 

No comments:

Post a Comment

AN HORAR DA MARUBUTAN KANNYWOOD

MARUBUTAN KANNYWOOD  Ranar Asabar 13-12-2025 aka gudanar da horo (training/workshop) ga marubuta 53 na masana'antar Kannywood wadda ta g...