Monday, August 18, 2025

HAMZA DAWAKI: GWARZON GASAR BASHIR TOFA 2025



 

HAMZA DAWAKI: GWARZON GASAR BASHIR TOFA 2025


Daga Kabiru Yusuf 

Kamar yadda ya gudana, an bayyana labarin "Ilimi Kogi" na Hamza Sadiq Adam a matsayin gwarzon gasar Bashir Tofa tare da bayar da kyaututtukan a gasar. Shin wane ne Hamza Dawaki?


An haifi Hamza Sadiq Adam, wanda aka fi sani da Hamza Dawaki, a fagen rubutu, a unguwar Dawakin Dakata, Ƙaramar Hukumar Nasarawa, a 22/02/1980. Kuma yanzu yana zaune da iyalinsa a unguwar Rangaza. 

Ya yi karatun allo a makarantun Malam Abdullahi da Malam Bahari da Malam Umar Basakkwace. Ya kuma yi yawon almajirci a ƙauyukan Daɗin Duniya da Tsalle da Ancau. Sannan ya yi karatun fiƙihu da hadisi da tafsiri da dangoginsu a wurin malamai irin su Malam Alfa Ma'aruf da Malam Zubairu Muhammad da Sheikh Aliyu Umar Chiromawa da sauransu. Tare da haka, Hamza ya ƙoƙarta ya riƙa zuwa makarantar boko. Har ya samu shaidar difiloma a Harsunan Hausa da na Turanci, a makarantar CAS, da ke titin zuwa filin tashin jirgin sama, a nan Kano. 

Hamza ya fara gwada rubuce-rubuce tun yana yaro ƙarami. Kuma a 2004 ya samu nasarar buga littafi mai suna Tubali, a lokacin yana aji biyar a makarantar sakandare ta Kawaji. 

Hamza ya halartar bitoci da tarukan ƙara wa juna sani a kan rubutu da dama, ciki har da Ibedi International Writers Residency, a Ibadan. 

Sannan ya samu nasarori a gasar rubutu da kyautuka da dama; kamar a gasar Gagara Gwari (ta waƙa) ta Taskar ALA 2012 sai gasar gajerun labarai ta Makarantar Malam Bambaɗiya, Jihar Kaduna 2014. Da gasar Labarun Yaƙi da Fatara, ta Pleasant Library Katsina, a shekarar 2017 da gasar Waƙoƙin Rashin Tsaro, ta Jami'ar Ɗanfodiyo, Sakkwato, 2021. Da sauransu.


Me labarin "Ilimi Kogi" ya ƙunsa?

Labarin wata jarumar mace ce, wadda suka rabu da mijinta, bayan sun haifi yaro ɗaya. Suka ɗauki shekaru suna zuwa kotu da mijin, a kan ta ba shi ɗan, ta hana. Alhali ita ba ta da ƙarfin samar wa yaron ingantaccen ilimin zamani. 

Don cike wannan giɓin, ta kasance takan fita da yaron, su bar unguwarsu. Wani lokacin su shiga gonaki, ta yi masa nuni da rayuwar tsirrai da ta dabbobi. Cikin hikima ta koya masa wani darasi. Misali, ta kwatanta masa yadda bishiyar giginya ta janye 'ya'yanta, can sama. Ba ta ba wa kowa, kuma kullum cikin jifan ta ake. Sai kuma bishiyar mangwaro, wadda ta bar 'ya'yanta a ƙasa-ƙasa, kusa da mutane. Suna tsinka ba tare da wahala ba. Sannan ta nusar da shi cewa, haka mutum mai rowa yake shan wahala da baƙin jini a cikin mutane. Kuma abin sa ba ya albarka.  Yayin da mai yawan kyauta ke samun farin jini, kuma kayansa ya yi albarka fiye da na mai rowar. 

Haka dai da sigogin darussa makamantan waɗannan ta ci gaba da koyar da shi, har zuwa lokacin da ta yi tsammanin yaro ya yi wa zaman duniya  kyakkyawar fahimta. Sai ta umarce shi cewa, duk ranar da suka koma kotu, ya ce shi babansa zai bi. 

Yayin da suka koma kotun ne, yaron ya amince da bin uban. Ya kuma  bayyana irin sigar da take bi don koyar da shi. Sai duk mutanen kotun suka cika da mamaki da irin hikima da jajircewar da ta nuna wurin koyar da shi! Har dai daga ƙarshe alƙalin da kansa ya nemar wa mijin biko. Ita kuma ta amince, aka mayar da auren nan take!

No comments:

Post a Comment

JAM'I A HAUSA (ADADI)

  Adadi (Jam'i) Kabiru Yusuf Fagge (anka) Adadi shi ne hanyar fayyace yawan abu, wato ɗaya ne ko kuma fiye da daya (jam’i) A harshen Hau...