KAWALCI A ƘASAR HAUSA
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
Kawalci yana ɗaya daga cikin munana ɗabi’u da suka zama
ruwan dare ba kawai a ƙasar Hausa ba har ma a duniya bakiɗaya.
Kawalci shi ne ɗabi’ar haɗa namiji da mace ko namiji da namiji
ko ma mace da mace don su yi aikin assha, inda yawanci mai haɗawar wato “Kawali”
yakan sami wani abin masarufi.
A taƙaice za a iya kasa kawalci zuwa manyan kaso guda uku
da suka haɗa da:
(1) Kawalcin Mata
Shi wannan nau’i na kawalci wasu mutane ne da suka ɗauki
wannan ɗabi’a a matsayin hanyar neman abin masarufi suke nama wa wasu mutane
mata suna kai musu da niyyar a aikata lalata, su kuma a biya su.
Suna gudanar da wannan ɗabi’a ne ta hanyar yarjejeniya ko
kuma yanke farashi. Ma’ana tun kafin su kawo wa mutum mace sai an ƙayyade abin
da za a biya su. Su waɗannan mutane suna nema wa mutum duk irin macen da yake
so, sannan kuma kowacce mace tana da farashi, ya danganta da ƙirarta.
(2) Kawalcin Maza
Nau’i na biyu wanda ya fi kowanne muni shi ne masu yin sa
sun mayar da hankali ne a kan nema wa mutane maza maimakon mata.
Su kawalan maza su ma mutane lalatattu, wasu ma suna
aikata irin wannan lalatar da maza, sukan yi haka ne ta hanyar yaudarar mutane
da wasu abubuwa. Sukan samu yara masu kwaɗayi su rinƙa ba su abubuwa na jin daɗin
rayuwa da yi musu alƙawari na cewa za su saya musu mota ko babur ko kuma su ce
za a kai su aikin Hajji idan suka amince aka aikata lalata da su.
Abin takaici a yanzu wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a
cikin al’ummar Hausawa da ma duniya bakiɗaya.
(3) Kawalcin Mata Da Maza
Wannan nau’i na kawalci ya fi sauran nau’o’in shahara da ɗaukaka.
Masu aikata wannan ɗabi’a sukan nemawa mata ko maza waɗanda za a yi aikin assha
da su.
Zaurancen Kawalai
Kawalai suna da zaurance na musamman da suke amfani da su
a lokacin da su a lokacin da suke aiwatar
da wannan ɗabi’ar. Misali a lokacin da suke zaune a majalisarsu ko
dandali duk mutumin da ya tunkaro su, idan suka ga ya yi kama da irin mutanen
da suke hulɗa da su, bayan sun gama gaisawa abu na farko da za su ce masa shi
ne.
“Alhaji me ake buƙata, kaza ko zakara?”
Shi kuwa idan abin da ya kawo shi kenan, sai ya zaɓa ya
ce; “Kaza” ko ya ce, “Zakara”
A zaurancen nasu abin da wai suke nufi da “kaza” shi ne “mace”
haka kuma abin da suke nufi da “zakara” shi ne “namiji.”
A mafi yawancin lokuta kawalai suna gane abokan harkar su
wato waɗanda za a nema a kai wa mutane ta hanyar wasu alamomi.
A ƙasashen da suka ci gaba kuwa sukan gane mata lalatattu
ta hanyar saka wata irin sarƙa a ƙafarsu ta hagu ko ta dama, ko kuma yin wani
ƙunshi na musamman a ƙafafuwansu ko kuma saka zobe a yatsan ƙafa.
Haka kuma sukan gane maza ta hanyar yin wani irin aski ko
kuma gyaran gashi na musamman. Ta haka ne su kawalan suna ganin su ko da kuwa
ba su taɓa ganin su ba, za su gane su, ta irin waɗannan alamomi.
Waɗannan alamomi sun yi nisa da zuwa ƙasar Hausa da
kewayenta.
Ba kowa ake yi wa kawalci ba, sai wasu keɓaɓɓun mutane waɗanda
ba sa so a gan su suna aikata irin wannan ɗabiu’ar. Snanan kuma yawanci shugabanni
ne a cikin al’umma, akan haka ne suke neman waɗanda za su riƙa yi musu kawalci,
suna biyan su.
Waɗansu daga cikin waɗanda ake yi wa kawalci akwai
attajirai da masu mulki da kuma wasu manyan mutane.
A mafi yawan lokaci kuwa su ne suke riƙe da ragamar
tafiyar da jagoranci na al’umma.
(A sani: Akwai wasu alamomi da alamtattuka da na ɓoye don
kar su zama abin koyi ga gurɓatattu)