Wednesday, January 25, 2023

'YAR NAJERIYA COVER - Sumayya Abdulkadir


 

'YAR SAKI BOOK COVER


 

KALAR KYAMARA CE

KALAR KYAMARA CE

Kabiru Yusuf Fagge

Alhaji Adamu, mahaifin Habule ya kira shi.

“Na kira ka ne don in sanar da kai na yi maka zabin mata. Na zaba maka Nafisa, ‘yar Alhaji Mukhtar, ka je ku gana.”

Habule ya girgiza kai.

“Gaskiya Dad ka yi shigar sauri. Ina da wadda nake so zan aura.”

“Wace ce wannan?”

“Zizi, ‘yar gidan Hon. Bala Gunduma.”

Alhaji Adamu ya girgiza kai.

“Haba Habule, ai kuwa Nafisa ta fi Zizi hankali da addini…”

Habule ya yi dariya.

“Dad ke nan! Dad ai Zizi ta fi Nafisa komai.”

“Me da me ta fi ta?”

“Good, Dad! Da farko Zizi kyakkyawa ce, ‘yar gayu, kalar gaban mota, kuma kalar kyamara.”

“Yaro dai yaro ne, wane ne ya gaya maka yanzu ana bibiyar wata mace kalar kyamara ko gaban mota, ai kalar hankali da addini ake bi.”

“Dad, ka yi hakuri, ni dai gaskiya kalar kyamara nake so.”

“Habule, ina nuna maka gefen wuka, kana kara kai hannu. Yanzu wadannan ‘yanmatan da kake kira da kalar kyamara, ku suke mayarwa ababen daukar hoto, ka ganka kamar wayayye, amma su mayar da kai gaula a gaban kyamara, ka saki baki su yi ta daukar ka.”

“Dad, ni wayayye ne dan birni, dole ina bukatar macen da zan keta a bi ni da kallo, wacce idan na sa ta a gaban lens za ta dauki ido. Amma na ga kamar ba za ka gane ba.”

“Shi ke nan, Allah ya kai mu lokacin da za mu gane wane ne bai gane din ba.”

*

Wata biyu da yin auren Habule da Zizi, Habule ya fahinci duk wani kyalkyal da sheki da Zizi ke yi ashe maya-mayai ne da hodoji, ya fuskanci duk harkar danfare (packaging) ce. Ba ma wannan ba ne ya fi damun shi ba, yadda ta zama ba ta da lokacinsa. Bugu da kari duk ta tsittsince masa ‘yan kudadensa, ta ja jarin kanta, ta fi shi muwalatin harkoki.

A yanzu kam sai dai ya hango ta a a social media. Haka take rangwada make-up ta yi radau da ita, ta dauki hotuna ta watsa, ana ta yi mata comments da liking.

Da abin ya ishe shi, ya je, ya sami mahaifinsa cikin damuwa. Yana magana da alamun jin kunya.

“Dad ya batun Nafisa?”

Alhaji Adamu ya sa halin da yake ciki, har zai yi dariya sai ya basar.

“Me kake nufi da batun Nafisa?”

“Ina nufin a nemar min aurenta.”

Yanzu dariya ta kwacewa Alhaji Adamu.

“Nafisa tana dakin mijinta cikin kwanciyar hankali. Ina matar taka?”

“Gaskiya Dad ba zan boye maka ba, wannan yarinya ba kala ta ba ce.”

“Don me, yarinya kalar kyamara, ka ce min ba kalar ka ba ce?”

“Lokaci da nake fadar haka ba na yin hangen nesa, amma yanzu ina tafe da hangenka Dad.”

“Ai kuwa Zizi kalar kyamara ce.”

Ya tsokane shi.

“Ni ma na san kalar kyamara ce Dad. Amma ba kala ta ba ce. A yi hakuri.”

Alhaji Adamu ya kyalkyale da dariya.

“Ai kuwa Zizi kalar kyamara ce.”

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...