Thursday, January 7, 2021

COVID-19: KARO NA BIYU

 

COVID-19: KARO NA BIYU
Kabiru Yusuf Fagge (anka)
 
A karo na farkon bayyanar Covid-19 an yayata yadda ya kamata, don haka wasu suka tsorata suka bi matakan kiyayewa kamar yadda hukumar lafiya ta sanar gwargadon yinsu.
 
Sai dai daman tun da farko, da yawa kuma ba su yarda da cutar ba bare su tsorata. Allah dai ya takaita cutar ba ta yi illa yadda aka zata ba ga al'ummar Afirka, wannan ya sa wadanda ba su yarda din ba suka rinka cewa daman sun fada bogi ce, wasu daga wadanda suka yarda suka dawo daga rakiyar ta.
Sai dai wasu suna ganin yanayin zafi da ake ciki ne ya hana cutar illa ga Afirikawa.
A wani bangaren wasu masana suna mamakin yadda cutar ba ta yi raga-raga ga al'ummun Afirka ba, har suke saduda cewar wannan daga Allah ne.
 
To sai dai a karo na biyu na yanzu da ake hasashen cutar na shirin dawowa bakatatan, akwai matsaloli abubuwan dubawa.
(1) Yanzu lokacin sanyi ne ba zafi ba, idan a da cutar ba ta yi illa a lokacin zafi ba, to tana da damar keta rashin mutuncinta a wannan lokaci na sanyi.
(2) Ana ganin tana da alaka da mura, to kuma a wannan lokacin na sanyi mura tana da karfi ga al'umma musamman nan Nijeriya, don haka cutar na iya samun abokiyar burminta.
(3) Mutane sun watsar da duk wasu hanyoyi na kariya, kamar sa takunkumi, ba da tazara, hana cunkuso, wanke hannu, zuwa ga hukumar lafiay da zarar an ji ba daidai ba da sauransu.
(4) Hukumomi da jami'an gwamnati da suke da jagorancin fadakarwa da samar da abubuwan kariya ga al'umma sun kasuwantar da harkar, sun karkartar da tallafi da kayyakin da aka samar don kariya ga cutar.
_
Sannan kuma a zahiri yanzu ana samun mace-mace da suke da alamu da cutar. Ya ya kenan?
Lallai ya kamata al'umma su farga, kar su yi sakaci wannan cuta ta illata su ta bangaren lafiya da rayukansu, tun da ta gama da tattalin arzikinsu.
Ya kamata a dage da bin dokokin da hukumar lafiya ta kasa take sanarwa a kullum, domin kowa ya kwana lafiya shi ya so. Kuma gyara kayanka bai zama sauke mu raba, rigakafi ya fi magani.
Allah ya maganta mana.
Kabiru Yusuf Fagge

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...