JAM'I A HAUSA
Tattarawa Kabiru Yusuf Fagge (anka)
A Hausa akwai hanyoyi da dama na yin jam'i. Bari mu duba wasu daga ciki kamar haka:
Mota -Motoci
Buta -Butoci
Ƙofa -Ƙofofi
Hanya -Hanyoyi
Tsutsa -Tsutsotsi
*
Riga -Riguna
Wando -Wanduna
Hula -Huluna
Jaka -Jakuna/Jakunkuna
Sanda -Sanduna
*
Kujera -Kujeru
Ƙadangare -Ƙadangaru
Fitila -Fitilu
Tattabara -Tattabaru
Aljani -Aljanu
*
Surutu -Surutai
Masallaci -Masallatai
Wanzami -Wanzamai
Alhaji -Alhazai
Shashasha -Shashashai
*
Kunne -Kunnuwa
Zane -Zannuwa
Ƙafa -Ƙafafuwa
Ido -Idanuwa
Ƙirare -Ƙiraruwa
*
Gida -Gidaje
Wuƙa -Wuƙaƙe
Jirgi -Jirage
Kurma -Kurame
Bisa -Bisashe
*
Wata -Watanni
Manzo -Manzanni
Fure -Furanni
Wasa -Wasanni
Kaka -Kakanni
*
Gari -Garuruwa
Buki -Bukukuwa
Ɗari -Ɗaruruwa
Abu -Abubuwa
Ƙashi -Ƙasusuwa
*
Gwaji -Gwaje-gwaje
Yanka -Yanke-yanke
Rubutu -Rubuce-rubuce
Tafiya -Tafiye-tafiye
Shiri -Shirye-shirye
*
Fartanya -Faretani
Garma -Garemani/garmuna
Garwa -Garewani
Marmara -Maremari
Kwalba -Kwalabe/Kwalebani