Friday, November 20, 2020
DR. BASHIR ABU SABE YA ZAMA SABON SHUGABAN NORTHERN NIGERIA WRITERS SUMMIT)
DR. BASHIR ABU SABE YA ZAMA SABON SHUGABAN KUNGIYAR TUNTUBA TA MARUBUTAN AREWACIN NIJERIYA (NORTHERN NIGERIA WRITERS SUMMIT)
Daga Kabiru Yusuf
Kwamitin zabe na kungiyar Northern Nigeria Writers' Summit karkashin jagoranci Odoh Diego Okenyodo ya bayyana Dr. Bashir Abu Sabe a matsayin sabon shugaban kungiyar Northern Nigeria Writers' Summit.
A ranar Litinin 16-11-2020 kwamitin mai dauke da mutum uku, ya bayyana Dr. Abu Sabe a matsayin wanda ya yi nasarar lashen zaben da sauran mukaman da aka yi takarar a kansu.
Dr. Bashir Abu Sabe Babban Malami (Senior Lecturer) ne a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua da ke Katsina. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, ya samu digirinsa na uku a Jami'ar Alkhahira da ke Masar.
Ya yi rubuce-rubucensa kan abin da ya shafi adabin kasuwar Kano da kuma kamanci da bambancin da ke akwai tsakanin marubuta mata a kasar Masar da Nijeriya.
Masani ne kan nazarin adabin Hausa a fannoni da dama. Shi ne shugaban kungiyar Marubuta ta kasa reshen jihar Katsina. Ya taba zama dan kwamiti na taron NNWS a 2017 da aka yi a Katsina.
Dr. Abu Sabe yana da kishi da son rubutu da marubuta da adabi gabadaya, ya bayar da gudunmawarsa sosai wajen ci gaban rubuce-rubuce ta fuskoki daban-daban.
KUNGIYAR TUNTUBA TA MARUBUTAN AREWACIN NIJERIYA (NORTHERN NIGERIA WRITERS' SUMMIT)
An kafa wannan kungiya a Minna da ke jihar Niger a 2008 wadda ta zama inwar marubutan Arewacin Nijeriya na jihohi 19 da ke Arewa, da nufin tsare-tsaren cigaban marubutan yankin. A shekara ta 2018 a Maiduguri, jihar Borno aka kafa shugabancin riko karkashin shugabanta Malam Baba M. Dzukogi, da suka tafiyar da kungiyar.
JADAWALIN SHUGABANNIN DA AKA ZABA
Dr. Bashir Abu Sabe -Chairman
Omale Allen Abduljabbar -Vice Chairman
Safiya Isma'il Yero -Secretary
Isma'il Bala Garba -Asst. Secretary
Hussaini Kado -Treasurer
Awaal Gata -PRO (North Central)
Haruna Adamu HAdejia -PRO (North West)
Yusuf Garba Yusuf -PRO (North East)
Maryam Gatawa -Auditor
Ogbe Benson Aduojo Esq -Legal Adviser
Tee Jay Dan -Ex-Officio 1
Dr. Bashir Abu Sabe ya cancanci rikon wannan kungiya, muna yi masa fatan alheri, tare da addu'ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa, amin.
Wednesday, October 28, 2020
Sunday, October 18, 2020
GIDAUNIYAR MARUBUCI BADAMASI BURJI
Gidauniyar Marubuci Badamasi Burji Ta Gwangwaje Yara
A lokacin da ɗalibai ke komawa makaranta, gidauniyar Badamasi S. Burji ta gwangwaje yara da littattafai da alƙaluman rubutu.
A shekarar da ta gabata ne Alhaji Badamasi S. Burji da gidauniyarsa suka samar da yunifom ga ɗalibai 5,200, a makarantar firamare da ya samar a mahaifarsa ta Burji dake ƙaramar hukumar Doguwa, a jihar Kano.
Yanzu haka an raba littattafan rubutu da alƙaluman rubutu, sai kuma abinci da ake samarwa ga kowanne ɗalibi kyauta.
Allah ya ƙarfafi wannan yunƙuri da wannan bawan Allah.
Friday, October 16, 2020
Monday, September 14, 2020
Subscribe to:
Posts (Atom)
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...