Rubutunka Tunaninka
MARUBUCI SHI NE UBANGIJIN LABARINSA
Gabatarwa
Muna farawa da sunan maqagin baiwa da hikima, wanda
ya saukar da Alkur'ani da ya labarta mana labaran al'ummun da suka gabata don
izina da misali. Yabo ga mafi girman darajar halittun duniya da na lahira,
(S.A.W.)
Da farko an samar ko in ce an sabunta wannan fili ne
a wannan zaure domin darasi a kan DABARUN RUBUTA LABARI (littafi ko gajeren
labari); DA SAURAN MATAKAN YIN RUBUTU MAI ARMASHI, a lokaci guda za a rinqa
tattaunawa don faxaxa ilimi a harkar rubuce-rubucen labaru na Hausa.
Rubutunka Tunaninka;- Duk marubuci kafin ya yi
rubutu sai ya yi tunani akan abin da zai rubuta, don haka kenan rubutun da
marubuci ya yi tunaninsa ne, (hakan ya zama rubutunka tunaninka) akasi daya da
ake samu shi ne tunanin ya zama ingantacce ko karvavve ko kuma akasin hakan.