Wednesday, November 14, 2018

Gajeren Labari: SANADIN BARA




SANADIN BARA
(C)Deejah Sharubutu


Na kasance mara wadatar zuci duk da dai maigidan yana kokarin ya ga ya fidda hakkin dake kansa, sai dai duk bana gani burina hangen abinda yake gaba da ni.
Watarana na fita da safe zan je asibiti, sai na ga mata suna ta shiga wani layi daidai lokacin da na sauka daga adaidaita sahu na tsaya ina kallon su, can na hango su kofar wani gida dankar ya sa na nufi wurin don ganin me ke faruwa. 



Daga baya-baya na tsaya ina nazari, sai na fahimci ai karbar sadaka ne da ake badawa, ina ta kallon matan dake wurin duk masu lafiya ne, babu nakasassu hakan ya ba ni karfin guiwar mantawa da abinda zan je yi, na bi layi ashe daman ba sai nakasasshe yake zuwa bara ba, na ga yaran mata ne yawancin su ma da kwalliyarsu a tare da su. 


Mun jima anan kafin a fito a fara raba mana 'yan dubu-dubu, duk da kokawar da ake yi na yi nasarar samun tawa, farin ciki ya dabaibaye ni - ba sana'a, ba komai na samu dubu. Ai da ka lokacin na samu abin yi, da garin Allah ya waye na tura yara makaranta, maigida yana fita ni ma nake fita maulata.
Yanzu duk wani guri da ake bada sadaka na sani, unguwa-unguwa, haka nake yawo saboda rashin wadatar zuci, ga dan karen wulakanci da muke sha, ga zagi, ga hantara, ga fada, duk jure su nake yi, saboda zuciyar ta riga ta mutu, wani zubin sai ka gama bin layin har rana ta yi sai ka ga masu kudin sun zo, sun wuce ka, bayan sun zuge gilashin motarsu haka zamu watse, mu tafi wani gurin.
Ba laifi, ina dan samun kudi amman saboda babu wadatar zuci a cikin zuciyar ya sa watarana sai in rasa ko sisi wani yawan zuwa maular a kafa, wani kuma sai na hau abin hawa.
Kamar kodayaushe yau ma na ji labarin inda ake bada sadakar dubu biyar-biyar, ina cike da zumudin safiya ta yi don in fice. Ai kuwa tana yi, na tura yara makaranta amman maigidan ya ki fita da wuri. Ganin ba shi da niyyar fita na yi masa karyar asibiti zan je. Ya dube ni, ya ce "Na ganki kalau, me zaki je ki yi?"
"Ai likita ya ce in koma."
"To tun jiya baki gaya min ba sai yau?"
"Na sha'afa ne, ka yi hakuri yanzu in je."
Bai yi magana ba, ya yi shiru ni ko tuni na sa hijabi, na dau nikaf ina daurawa, daman idan za ni yawon maula nikabi nake sawa don gudun haduwa da idon sani.
"Nikaf kuma yaushe ki ka fara sawa ban da labari?"
"Kai ko da maigida salon jan zance gare ka."
"Ai na ga sabon abu ne da ban taba gani ba."
"Ina sawa ai, daman tunda addini ya yi umarnin mu suturce jikin mu ko mu rufe fuskar mu saboda kallon mazajen da ba namu ba."
"Haka ne fa amman ga wanda kyau ya yiwa yawa ko? Wadda zata dinga haddasa fitina ga maza ba."
"Hmm maigida, kai dai sai na dawo." Na sabi jakata, har na kai soro saboda zumudi na ji ya ce "Kudin motar fa?"
Na dawo "Au na manta ne ina gudun kar in makara." Na karba ba godiya, na yi gaba, sauri-sauri.
Abin hawa na hau, na nufi inda na ji labarin ana ba da wadannan makudan kudade. Kudin mota ma dari uku na kashe, da na je gurin ya cika makil da mata kala-kala yawanci da karfinsu, shigar tasu ma mai kyau ce amman babu kyan zuciya. Na jima da zuwa, sannan na ga duk an tashi ana gudu, ashe yaron gidan mai bada sadakar ne ya fito, gefensa kuma ga wani a tsaye da bulala.
Can guri ya kaure da hayaniya, duk da dukan da mutumin nan yake yi da bulala bai sa gun ya nutsu ba, ai ko sai aka yi kan mai bada kudin da kokawa, ni ma na kutsa ciki ina kokarin samun nawa, ai ko wata kakkarfa dake kusa da ni, ta ingije ni, sai gani kasa wanwar, ana bi ana take ni, ihu nake amma babu wanda ya kula dani, kowa yana kokarin ya samu abinda zai samu. Ni dai, na ji azaba, ashe suma na yi, zuwa wani lokaci na ji jikina da lema, na bude ido na ganni a inuwa, duk matan nan sun tafi sai wasu maza biyu da suka taimake ni, suka janyo ni inuwa, suka yayyafa min ruwa, na dawo daga suman da na yi.
Nayi yunkurin in gyara, na ji wata irin azaba da radadi a cinya ta, na kwalla kara mutanen da ke gefe na, suka ce "Ai ba za ki iya tashi ba, karyewa kika yi a cinya, ga ciwuka nan a jikinki birjik!"
Ihu na saka da salati hawaye na zuba a idona.
Dayan ya mike ya ce "Da karfinki na neman halak da lafiyarki kika fito maula, ai yanzu kin samu jarin maular tunda ga shi nan za ki yawo da kafa daya."
Wani kuka ya subuce min tare da dana-sani. To yanzu ni me zan cewa maigidana? Wa zai mayar da ni gida?
Shi ke nan na rasa kafata, ga raunuka jikina!

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...