FASSARA A HARSHEN HAUSA
Kabiru Yusuf
MA’ANAR FASSARA
Fassara asalinta kalmar Larabci, wato aikatau. Ma’anar
kalmar a Larabci, ita ce bayanin wani sashe na littafi ko juyar magana daga
wani harshe (yare) zuwa wani; wato “tarjamatun”. A taƙaice tafinta ko bayyana
ma’anar magana shi ake kira da Larabci “Tarjamah/Tafsir”. Tafsir kuwa, ainihin
ma’anarta ita ce bayanin ayoyin Alƙur’ani. Saboda haka ma iya cewa Hausawa sun
ari wannan kalma ta fassara ne daga “fassar” ko “Tafsir.”
Bisa wannan za mu iya bayyana man’anar
fassara da cewa, hanya ce ta mai da wata magana ko salo ko zance na wani harshe
(yare) zuwa wani harshe (yare) ba tare da an sami bambancin ma’ana ba.
Idan ana fassara, ana amfani da wasu ƙa’idoji ne
don bayyana ma’ana mafi kusa ko dacewa daga harshe na farko da harshe na biyu
ta fuskar ma’ana da salo a maganance, ko kuma a rubuce. Saboda haka, ashe ke
nan fassara ba ta samuwa sai da harasa guda biyu (harshen zance) da kuma harshe
na biyu (harshen fassara). Haka kuma mafassari dole ne ya kasance mai iya
yaruka biyu zuwa sama. Wato, dole mafassari ya zama kanari ko coli wajen iya
magana da harasa. Dalili shi ne, mai iya magana da harshe (yare) ɗya ba ya iya
fassara, sai dai ya yi ƙarin bayani.
Misali, a cikin harshe guda, ana iya samun wata magana
dunƙulalliyaa cikin salo na hikima kamar
karin magana ko zaurance ko azanci, waɗanda suke buƙatar ƙarin bayani domin a
fahince su.
Fassara tana da manyan rabe-rabe guda biyu waɗanda suka
haɗa da; fassarar ilimi da fassarar adabi
1. Fassarar ilimi: ita ce wadda ta shafi
kimiyya ko kuma addini. A nan duk abin da aka rubuta ta sha’anin ilimi, ƙoƙari za a yi a zuba mata ƙa’idoji ko a ba ka labarin
wani abu kai tsaye kawai ba wani sanabe ko ado ko ƙaƙale. Wato dai a faɗi
gundarin gaskiya abu yadda yake. Haka kuma, ana amfani da kalmomi tare da zaƙin
murya na baliganci ko tsoratarwa ga abubuwan da suka shafi harkokin addinin
domin jama’a su tsorata ko himmata wajen abin da ake son su yi ko su bari.
2. Fassarar adabi: ita wannan fassarar ta adabi kuwa,
ita ce wadda ake so a faɗi wani abu da aka rubuta ko aka faɗa da salo na sanabe
ko ƙaƙale, wani lokaci ma akan so a faɗi abu ɗaya da ma’anoni biyu ko fiye,
yadda in an tashi takura mai faɗa ta nan sai ya ɓullo ta can ya ce, ai ga abin
da yake nufi in an zo fassara irin wannan, dole ne a yi ƙoƙari a ƙaƙale da salo
na kurɗa-kurɗa da za a iya, har ma inda dama a yi wa fassarar baki biyu in ana
iyawa.
NAU’O’IN FASSARA
Babban abin da ake nema a fassara, shi ne fahintar abin da harshe na biyu
ke magana kamar yadda ma’anarsa take a harshe na farko. Abin nufi a nan dole
sai an fassara komai daidai sannan za a sami fahintar abu sosai. Saboda haka
ashe ya zama wajibi mai fassara ya fahinci abin da yake fassarawa, don in bai
fahinta ba, ba zai yiwu ya yi fassara ingantacciya yadda abin yake ba, wanda
yin hakan shi ke sa ma’ana ta canza a kuma haddasa rashin fahinta ga masu
karanta fassara ko saurare saboda ganin irin wannan ne a wani ra’ayi aka
rarraba fassara zuwa kashi-kashi kamar haka:
(1) Fassarar Kalma Da Kalma/ Jimla Da Jimla
Ana yin fassarar kalma da kalma ko jimla da jimla kamar yadda yake a cikin
harshen farko zuwa harshe na biyu ko da babu ma’ana.
Wani lokacin kuma ana ɗaukar
kowanne sakin layi ne abin da ake so a fassara ba ta kalma da kalma ba, wato
akan yi ne gwargwadon abin da sakin layi ya ƙunsa.
Misali: Good morning =Kyakkyawar
safiya
A Hausa an ce: “Naira
bibiyu ne kowanne”
“Two-two naira each”, maimakon “two naira each.”
Saboda haka irin wannan fassara a wani lokaci ba ta da
daɗin karatu a wajen mai karantawa, kuma fahintar ma’anarta kan jirkita.
(2) Fassara Mai ‘Yanci
Fassara mai ‘yanci ita ce wadda za a yi bisa fahintar
abin da aka karanta na cikin harshe na farko. Wato wannan fassarar, harshen da
mai fassara ya karanta kuma ya fahinci abin da ake nufi, sai shi kuma ya rubuta
cikin harshen da yake fassara mafi sauƙi yadda za a fahinta. Wato mai fassara
na da ‘yancin faɗin abin da ya ga dama muddin dai ya bayar da ma’ana kamar
yadda yake a harshe na farko.
Ita wannan fassara tana buƙatar lura ainun don gudun
kada a yi ƙari ko ragi wanda bai dace ba a cikinta, kodayake dai ana iya
taƙaita ta ko a tsawaita ta, amma dai fassara ce mai tara dukkan ma’anar abin
da ake fassarawa.
(3) Fassarar Harshe Da Wani Harshe
Wato ita wannan fassarar, a wani lokaci akan sami mutum
yana magana da wani harshe sannan kuma wani ya fassara maganar mutumin nan da
wani harshe. Wannan irin fassarar na samu ne wajen magana a taro, inda wasu ba
sa jin harshen wasu kamar yadda ake yi a majalisar ɗinkin duniya ko shugabannin
ƙasashe ko kuma manyan jami’an diflomasiyya. Irin wannan fassara ita ake kira
“Tafinta.”
MUHIMMANCIN FASSARA
(a) Ana fassara don kyautata danganatakar al’ummomi
daban-daban
(b) Ana fassara littattafai don a haɓaka harkokin ilimi
(c) Ana fassara don wayar da kan al’umma
(d) Ana fassara don yaɗa manufofin gwamnati ko hukuma
(e) Ana fassara don haɓaka arziƙin ƙasa ta sanin wasu
asiran ƙere-ƙere da hanyoyin kasuwanci
(f) Ba wa ɗan’adam damar laƙantar harasa da dama
ƘA’IDOJIN FASSARA
Akwai hanyoyi da ƙa’idoji da ya zama wajibi mai fassara
ya bi su domin a fahinci saƙon da yake son isarwa ga jama’a. Waɗannan ƙa’idojin
sun haɗa da:
(1) Mai fassara ya san manufar batu. Shin ya shafi
kimiyya ne ko fasaha ko kuma kasuwanci?
(2) Mai fassara ya laƙanci harasan da zai yi fassara da
su.
(3) Mai fassara ya san kalmomi da ma’anoninsu, musamman
gama-garin kalmomi, irin su hannu, baki, ƙafasa, kai da sauransu.
(4) Sanin bambancin al’adu, domin harshe da al’adu
Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Misali ƙanƙara da dusar ƙanƙara.
(5) Sanin kalmomi masu harshen damo, misali kamar a ce
“jirgi” a nan jirgin na iya zama “jirgin sama” ko “na ruwa” ko na “ƙasa.” Da
sauransu
(6) Mai fassara ya daidaita harshe, kuma ya san irin
karin da zai yi amfani da shi domin a fahince shi da zarar ya ambaci kowacce
irin kalma.
(7) La’akari da fifikon ma’ana a fassara wajibi ne,
misali:
Good morning:
Kyakkyawar safiya Barka
da asuba Ina kwana
(8) La’akari da mutanen da ake yi wa fassara shi ma
wajibi ne. Ana so mafassari ya yi la’akari da basira da ilimi da shekaru na
mutanen da yake yi wa fassara.
(9) Mai fassara ya yi fassara cikin daidaitacciyar Hausa
ba cikin furucin Kananci ko Zazzaganci ko Katsinanci ko Dauranci ko Sakkwatanci
ba. Haka kuma kada ya yi fassara cikin Ingausa.
(10) A yi la’akari da canza sigar jimloli domin su dace
da harshen fassara. Kowane harshe da tsarin jimlolinsa. Misali a Hausa ana iya
amfani da suna ko wakilin suna a jimla ɗaya, amma a Turanci haka ba ta faruwa.
Misali: (a) Ado went to Kaduna. =Ado ya tafi Kaduna. (ba; Ado tafi Kaduna ba)
(b) He bought twelve cars. =Ya sayo motoci sha-biyu.
(ba; Ya sayo sha-biyu motoci ba.)
(11) Ya zama mai bincike da neman cikakken bayanai game
da ma’anar kalmomi tsofaffi da kuma sababbi.
(12) Mai fassara ya zama mai bin ƙa’idojin rubutu kamar
yadda ƙa’idar harshe yake fassarata a ajiye. Misali: shi ne ba shine ba, ita ce
ba itace ba, kowane ba ko wane ba, za a ba za’a ba da sauransu.
MATSALOLIN FASSARA A HARSHEN HAUSA
Harasa suna da hanyoyi da ba ƙayyadaddu
ba, kuma rashin ƙayyadewa bisa abin da ya kamata a ce kaza a wannan harshe shi
ne kaza a wancan harshen, shi ya kawo akasarin bambance-bambance a tsakanin
harsuna. Taƙaitar wannan bambancin kuwa shi ne samuwar tsatso da asali da kuma
cuɗanya tsakanin harasa.
Ire-iren wannan shi kan sa mutum ya iya yin kuskure,
wato cewa ba ya yiwuwa a fassara zance daidai-wa-daida, wato ba ragi ba ƙari,
haka kuma gwargwadon nisantar harasa gwargwadon salwatar manufa da ma’ana, amma
duk da haka za a iya fassara zance ta hanyar tsantsar kalmomi ba damuwa da
dangantakarsu ba.
Idan aka duba ‘yan shekarun baya, duk wanda ya liƙewa
harshen Hausa, alhali ga ‘yan birni da ma’aikata tare da ‘yan makaranta kowa
sai hanƙoro yake ya ji ana “yes, yes, no, no” to zai sha wuya, domin kuwa
kallon biyu-ahu zai yi masa. Amma Allah da ikonsa, harshen Hausa ya sami wani
matsayi na gogayya da wasu manyan harasa. Wannan shi ya sa ake ƙoƙarin gwada
kalmominsa da nasu. Saboda haka wannan ya nuna ba wai a yanzu ne matsalar
fassara ta fara ba, a’a tun lokacin da mutanen wata ƙasa suka fara kutso mana
ne muka fara cin karo da waɗannan matsaloli:
1- Rashin Damuwa da kiyaye
dangantakar da baƙuwar kalma take da ta Hausa;
2- Rashin sanin ita kanta baƙuwar
kalma, balle a san ‘yar’uwarta a Hausa.
3- Rashin sanin kalmomin Hausa
yadda za a ce ga ‘yan’uwansu a cikin baƙin kalmomi.
Waɗannan su suka sada arar wata kalma ta zo sai kawai
mutane su bar harshen ya haɗiye ta don zafin da yake da shi, sai ka ga Hausar
ta ainihi ta ɓace. A wannan magana da muke yi, akwai alamomi da yawa da muka
ara waɗanda idan aka tsaya aka bincika za a iya gano ainihin takwarorinsu na
Hausa domin kuwa akwai irin waɗannan kalmomi birjik a cikin adabin zamani, sai
dai kula da rashin saninsu suka haddasa wannan. Wato, sai ka ga mutum wanda ya
kamata ya fassara wata kalma, amma ƙuiya da rashin sani ya sa ya tsallake ta,
kuma ya rafkana wajen fassarar ta, haka kuma za ta zauna har ‘ya’ya da jikoki.
Harshen Hausa ya fara cuɗanya da baƙin harasa. Cuɗanyar
da ya yi a nan gida ita ce wadda ya yi da dukkan harsunan Najeriya. Amma waɗanda
aka kawo tsaraba su ne Turanci da Larabci da kuma Faransanci da sauransu.
Saboda haka, idan har ana son gano yadda baƙuwar kalma
kan shiga cikin wannan harshen na Hausa, dole ne a ɗauki wani baƙon harshe a yi
amfani da shi. Alal misali; Larabci ya shigo ƙasar Hausa ta hanyoyi guda biyu,
wato dalilin kasuwanci zuwa ƙasashen Larabawa kamar irin su Libiya, Sudan,
Mali, Maroko da sauransu. Sannan kuma ta dalilin zuwan addinin Musulunci.
Malamanmu na da, idan suna karatu sai su riƙa ƙyale wasu kalmomin Larabci suna
tsunduma su cikin Hausa, maimakon su fassara su, amma saboda ƙuiya da rashin
sani ya sa kalmomin ke yi wa harshen Hausa kane-kane, misali;
Larabci Hausa
Arziƙi maimakon wadata
Shagala maimakon mantuwa
Ilimi maimakon sani
Waɗannan kalmomi a koyaushe za ka ji malamai suna faɗarsu,
kuma haka ake rubuta su. Haka abin yake faruwa da kalmomin Turanci waɗanda suka
yi wa harshen Hausa kane-kane;
Turanci Hausa
Kwandem maimakon la’ana ko suka
Dameji maimakon lalacewa
Coci maimakon majami’a
Matsalar fili da lokaci ke haddasawa cikin jaridu. Abin
nufi a nan shi ne, filin da za a sa Larabci da yawa kan jawo taƙaita fassara ko
faɗaɗata. Matsalar lokaci kuwa ta shafi lokacin da aka ƙayyade wajen shirya
jarida da lokacin da ake so a buga ta tafi don sayarwa ga jama’a.
Don haka ƙarancin lokaci da fili kan sa a yi wa labari
yanka a yi aya a wurin da bai dace ba, ko kuma cire wani sashe da ba shi da muhimmanci.
SHAWARWARI GA MAI FASSARA CIKIN HARSHEN HAUSA
Duk mai fassara cikin harshen Hausa ta kowace irin
hanyar sadarwa ga jama’a dole ne ya kasance ya yi la’akari da waɗannan
shawarwari:
1. Dole ne ya kasance ya san
harshen da yake so ya fassara da Hausa.
2. Dole ne ya san harshen Hausa,
yadda zai iya gane kalmominta da kuma baƙin kalmomi.
Dangane da sigar Nahawu, kowace hanya aka bi sai an sami
canji da ya shafi shigar Nahawu. Alal-misali; A Hausa za a iya haɗa suna da
wakilin suna a cikin jimla guda, wanda Turanci bai yarda da wannan ba. Misali;
Ado ya zo. Amma a Turanci sai dai “Ado come” ko “He came,” ba “Ado He came” ba.
Ta fuskar kalmomi da ma’anoninsu kuwa, ana la’akari da
makusanciyarsu mafi dacewa, domin mutum zai haɗu da kalmomi gama-gari, misali;
hannu, ƙafa, kai da sauransu da kuma kalmomi masu manufa ɗaya, amma suna da
bambancin al’adu misali kamar “fari” da kuma “fat”. Sai kuma kalmomin da suke
nuna zurfin ƙwarewa, misali;
Teargas =Barkonon
tsohuwa
Senate =Majalisar
Datijai
Salon zance da karin magana, kyawawan misalai ne da za
mu iya amfani da su ta wajen irin juye-juyen da za mu iya yi wajen fassara.
Idan mai fassara ya ci karo da salon ma’ana akwai abubuwa uku da zai iya yi;
(1) Salo zuwa salo
He is second to none;
Ba shi da na biyu.
(2) Juya ma’anar sarari zuwa salon zance.
Pride begets the turban of poverty;
=Girman kai rawanin tsiya
(3) Salon zance zuwa ma’ana sarari.
He was alarmed;
=Girmansa ya faɗi (ƙarin gishiri)
HANYOYIN MAGANCE MATSALOLIN FASSARA
Idan muka duba abubuwan da aka zayyana a baya dangane da
matsalolin fassara, sai mu ga ita kanta matsalar fassara ba ta masu sadarwa ga
jama’a ce kaɗai ba. Wannan matsala ce ta gwamnati wadda ya zama tilas a gare ta
ta tashi tsaye wajen bai wa harsunan ƙasar nan wani matsayi da ya dace da su.
Hausawa sun ce, hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Saboda
haka hanyoyin magance matsalolin fassara yanzu ta zama ta fassara da masu
amfani da harshen.
(a) Masu fassara su san cewa fassara cikin harshen baka
tana da fifiko kan fassara cikin rubutaccen zance.
(b) Masu fassara su san cewa maganar mutanen da ake yi
wa fassara dangane da matsayinsu tana da fifiko kan fassara da ta fi yawan
jama’a/mutane.
(c) Masu fassara su zama masu yawan gudanar da bincike
akai-akai da kuma yawan halartar taron ƙarawa juna sani.
Manazarta
Tuntubi marubucin