Alƙalancin Gasar Rubutu
Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkayi akwai abubuwan da za su amfani marubuta masu sha’awar shiga gasa don yin nasara.
Ɗabi’ar Karatu
Wannan a bayyane yake cewa, yanzu al’umma sun fi son su kalla ko su saurara fiye da karantawa. Idan haka ne, to kai marubuci kana da gagarumin ƙalubale rubuta labarin da zai sa alƙalan gasa ko suna so ko ba sa so za su karanta, wato ko ba don aikin da aka ba su na karanta labarin su yi alƙalanci ba, ko don salo da gwaɗare na labarun sai sun karanta.
Duk da yake akwai waɗanda daman aikinsu kenan su karanta labari su yi masa alƙalanci, amma duk da haka idan kai marubuci ka saɓa lamba, to za ka hayayyaƙa su.
Lokaci
Masu sanya gasa sukan sa lokacin fara karɓar labaran shiga gasa da kuma lokacin rufewa, kamar yadda muka sani wasu suna sa wata ɗaya, wasu biyu, wasu uku har zuwa watanni uku ko fi. Misali, za a fara karɓar labari daga ranar 1 ga watan Janairu 2026 zuwa 1 ga watan Fabarairu 2026, wannan yana nuna wata 1 cur kenan.
To kai marubuci ka lura da wani abu guda, mafi akasarin kintacen lokaci na rana da muke amfani da shi, shi ne daga ƙarfe goma sha biyu da minti ɗaya na dare shi ne wata sabuwar ranar ta shiga, misali ko ba a sa lokaci ba, idan masu gasa suka ce ranar 1 ga watan Janairu, 2026, za a fara karɓar labarai to wannan ranar za ta fara ne a Alhamis 1-1-2026, kuma za ta fara ne daga kan 12:01 na dare. Sannan ranar Lahadi 1-2-2026 da misalin ƙarfe 12:01 za a daina karɓa. Wasu masu sanya gasar suna sa alama (alert) na ƙin shigar saƙon da ya wuce wannan lokacin, wasu kuma suna duba lokacin da saƙon da marubuci ya aiko ya shigo, da sun ga ya wuce da minti 1, to duk kyan labarinka, ya fita daga tsari, babu shi, kuma za su jefa shi gefe ko kuma kwandon shara.
Mu kuma ‘yan Najeriya saboda rashin sanin darajar lokaci, sai mu ga cewar ai ba wani abu ba ne don mun tura da dare ko ya wuce sha biyun daren, ko ya kai karfe 4 na asuba muna ganin duk ɗaya ne, to wannan kuskure ne.
A shawarce ya kamata marubuci ya tsara labarinsa cikin isasshen lokaci, ya bibiye shi, ya yi gyara, ya bayar a duba masa duk a cikin lokacin da bai ƙure ba, sannan ya tabbatar bai karya duk wata ƙa’ida ta gasar ba, bayan ya tura kuma ya bi da addu’a. Wannan kenan.
Wani abu da yake ƙara kawo matsala ga masu shiga gasa a ƙurarren lokacin ba wai ga masu gasar ba ne, ga shi marubucin ne ma. Idan marubuci ya ƙure lokaci, yana hana shi bibiyar labarinsa ya gano wasu kurakurai da sukan iya hana labarin nasa ya kai bantensa, ƙure lokacin yakan sa ya tafka kuskure wajen gaza gyara wani abu da zai taimaka masa wajen samun nasara.
Wasu marubutan masu wayo sun rubuta labarai da yawa, sun ajiye su, ana sa gasa kaza, kawai za su ɗauko, su kakkaɓe su, su gyara, su sauya abin da za su sauya, su tura a kan lokaci.
Adadin Kalmomi
Sau tari a gasanni musamman na gajerun labarai akan ce ana so kalmomin labaran kar su gaza adadi kaza kuma kar su wuce adadi kaza, ko kuma kawai kalmomi kaza ake buƙata. Misali a ce kada kalmomin su yi ƙasa da dubu 1000 kuma kar su wuce 1500.
To wannan yana bai wa marubuta da yawa matsala wajen ƙidayawa, kuma yana da sauƙi kamar yadda zan kawo misalai na hanyoyi uku da ake rubutun da su a yanzu, wato (1) rubutawa da biro da takarda (2) rubutawa da kwamfiyuta (computer) (3) sai kuma rubutu da waya (hand set)
Kafin na kawo su, akwai abu na farko da ya sa marubuta suke samun matsala da adadin kalmomi, wannan abu kuwa shi ne; marubuci yana ji a ransa ta yaya ana son ya isar da saƙo amma za a ƙayyade masa adadin kalmomi? To ina shawartar marubuta in har kana son yin nasara ka cire wannan tunani daga ranka, domin baiwar da kake da ita, ita ke sa ka tattara labaran shekaru hamsin ka rubuta a rabin shafin littafi, idan haka ne don an ce ka yi labari a adadin kalmomi 100 kawai ka ɗauki hakan a matsayin shan ruwa ya fi shi sauƙi, wannan kenan.
Yanzu ga hanyoyin ƙidaya kalmomi a rubutun.
(1) Rubutun biro ko fensir ko alƙalami a kan takarda
Da farko, ai a matsayinka na marubuci, ka san mene ne kalma ko? Kalma ita ce haɗakar sauti ko haruffa waɗanda suke ba da ma’ana, kuma ake magana ko rubutu da su. A kalmomin nan akwai na suna (misali: Ali, littafi, rago, saniya, labule, keke dss), sannan akwai aikatau (misali: tafi, ci, sha, tsalle, dara dss), akwai sifa (misali: baƙi, dogo, ƙarami, sabo, mai kyau dss) akwai wakilin suna (misali: ni, mu, ku, su, shi, ita), akwai bayanau (misali: a guje, da sauri, jiya, sosai dss) akwai mahaɗi (misali: da, kuma, amma, ko dss) akwai alamar motsin rai (misali: kash! Wash! dss) da sauransu. To idan ka san cewa waɗannan kalmomi ne, don haka lokacin da ka rubuta labarinka za ka bi ka ƙirga su ɗaya bayan ɗaya ka san adadin su. Misali, sai ka rubuta labari a layin farko kamar haka:
“Bayan da Musa ya shiga ɗakin, ya tarar da Hindu da wata yarinya a zaune suna kuka...” Idan ka zo ƙidayawa za ka yi su kamar haka:
(1) bayan (2) da (3) Musa (4) ya (5) shiga (6) ɗakin (7) ya (8) tarar (9) da (10) Hindu (11) da (12) wata (13) yarinya (14) a (15) zaune (16) suna (17) kuka...
Ka ga a nan kana da kalmomi guda (17) ka yi lissafinka daidai.
Wasu suna tafka kuskure wajen tunanin wasu ba kalmomi ba ne masu zaman kansu kamar dirka “ne” da “ce” ko “a” da “e” duk sai su haɗe su, ko su tsallake su.
Wasu kuma rashin bin ƙa’idojin rubutu ne yake haifar musu da matsalar rashin daidaita adadin kalmomin. Wani sai ka ga ya rubuta:
“Za’a” ko “shine” ko “mune” ko “gaka” “emana” kuma duk a harhaɗe maimakon a rarrabe, kalmomi bibiyu ya mayar da su ɗai-ɗai a lissafe.
Ko kuma kalmomi ɗai-ɗai ya mayar da su bibiyu, kamar “ya na” ko “dai dai” ko “mana” da sauransu.
To idan ka kiyaye waɗannan abubuwa kuma ka bi wancan tsarin da na kawo, za ka ƙirga adadin kalmominka cikin sauƙi.
(2) Kwamfiyuta
Kwamfiyuta tana da tsarin ƙidaya duk adadin kalmomin da marubuci ya shigar cikinta, akwai a farfajiyar wajen tafin (typing) ɗin MS Word, wajen da ake kira “Status Bar” ko kuma kai tsaye ka shiga wajen “Review” za ka ga wajen “Word Count” kana shiga za ka ga adadin kalmomin ka, kai har da adadin shafuka da adadin sakin layi da adadin layukan jimloli da adadin sarari (space) da ka bayar.
(3) Wayar Hannu
Haka a wayoyin hannu a kan WPS, kana shiga wajen “tools” sai ka je “view” za ka ga “word count” kana taɓawa zai kai ka wurin da za ka ga yawan kalmominka har da sararin da aka bayar (spaces) da wanda ba a bayar ba. Idan adadin ya yi yawa ko kaɗan sai ka daidaita.
Jigo
Masana sun sha yin bayani a kan jigo a mabambantan rubuce-rubucen ƙagaggun labarai daga gajeru zuwa cikakken littafi. Shi dai jigo, shi ne manufa ko saƙo na labari.
Sau tari masu sanya gasa musammman ta gajerun labarai sukan bayar da jigon da suke so a yi rubutu a kansa, kamar gasar Ɗangiwa, duk shekara suna bayar da jigon da suke so a yi rubutu a kai, kamar gasar Jigawa da aka fara ta shekarar 2025 ta kasance da manufar ayyukan gwamnan jihar Jigawa, wato Malam Umar Namadi. Amma wasu ba sa bayar da tsayayyen jigo guda ɗaya, kamar gasar Hikayata ta BBC Hausa da Gusau Institute.
To ko ma dai mene ne akwai abin da nake son marubuta su gane a kan jigo a gajeren labari, kuma shi ma yana bai wa wasu matsalar samun nasara. Saboda rashin tantance jigo ko matsayinsa a yayin rubuta gajeren labari wasu sukan cunkusa manyan jigogi sama da ɗaya ko biyu ko ma uku har huɗu, su lafta a rubutunsu.
A zahiri jigo ɗaya ake buƙata a gajeren labari, wanda wasu ‘yan ƙananan saƙonni marasa yawa suke tallafarsa.
Gajeren labari ba kamar dogon labari ba ne bare marubuci ya cunkusa masa manyan saƙonnin da ake gaza tantance wanne ne jigon labarin. Wasu marubuta sukan sami kuskure, su yi ta sako saƙonni ba adadi, waɗanda ba za su iya warware su a cikin ɗan labarin da suka rubuta na gajeren labari ba, kuma wannan sai ya sa a yi haihuwar guzuma, wato labarin ya gaza kai bantensa, wannan yana faruwa ne har a gasannin da ake sakar wa marubuta mara su yi rubutu a kan jigon da suke so.
Misali an ce a yi rubutu a kan jigon ƙazanta, sai marubuci ya kawo kishi da tarbiyya da mugunta da bara duk ya ba su ƙarfi a labarin, to masu alƙalanci za su rasa gane wanne ne jigon naka.
Yawan Taurari
Haka, su ma wasu marubutan sukan sami matsala wajen saka taurari da yawa a labarinsu. A zahiri shi gajeren labari ba ya buƙatar yawan taurari, domin yawansu yana nuna zaren labarin yana da tsayi kuma ya wuce a iya ɗinke shi a gajeren labari.
Shi gajeren labari ana buƙatarsa kaɗan, kuma a fahimce shi cikin sauƙi amma idan ka zuba taurari da yawa, to ana buƙatar a fahimci manyansu, kuma za su rikitar da labarin.
- Ba za ka iya gamsar da rawar da taurari da yawa za su taka a gajeren labari ba.
- Sannan ana sa tauraro wanda labarin ya fi karkata gare shi.
- Sai kuma tauraron da yake taimaka wa tauraron (jarumi) labarin naka ko kuma mai ƙalubalantar sa.
- Sai kuma wani tauraron mai ƙara armashi a labarin ko ya kunno wata rigimar a labari.
Ƙa’idojin Rubutu
Alƙalan gasa sun zubar da labarai da yawa saboda dalilan rashin bin ƙa’idojin rubutu.
(1) Wasu alƙalan suna ganin rubutun marubuci a hargitse za su ajiye shi gefe su ce marubucin bai san me yake yi ba, ko da kuwa labarinsa ya yi daɗi. (idan ya yi daɗin ma ba za a sani ba sai an iya karantawa)
(2) Rashin bin ƙa’idojin rubutu na sa adadin kalmomi a labari su ƙaru. Misali za ka rubuta “Muna sane da duk irin rigingimun da suke faruwa a cikin unguwar da kuma masu haifar da su.” Sai ka rubuta “Mu na sa ne da duk irin rigingimun da su ke faruwa a cikin unguwar da ku ma ma su haifar da su.”
Ko kuma ya rage adadin kalmomin cikin labari, misali za ka rubuta “Shi ne ya zo ɗazu amma na san ba a gan shi ba.” Sai a rubuta “Shine yazo ɗazu amma nasan ba’a ganshi ba.”
(3) Haka an samu marubutan da suka rinƙa rubuta “x” a matsayin “z” ko “s” su ma sun shiga tasku, domin an watsar da labarai masu yawa a kan waɗannan abubuwa. Marubuci zai rubuta “zama” sai ya rubuta “xama” da sauransu.
(4) Kuskure rubuta Hausar baka a wajen da ya kamata a rubuta rubutacciyar Hausa da sauransu.
Shawara a Dunƙule
Akwai abubuwan da marubuta ya kamata su kula da su a yayin rubuta gajeren labarin gasa, kafin rubutun ya je hannun alƙalai, waɗannan abubuwa su ne:
1. Jigo (saƙo)
-Marubuci ya tabbatar labarinsa yana da jigo bayyananne.
-Ya tabbatar saƙon yana da ma’ana.
-Ya tabbatar ya nuna jigon labarin ta hanyar labari, ba wai kai marubucin ka faɗa kai tsaye ba.
2. Tsarin Labari
-Marubuci ya buɗe labari da jan hankali.
-Marubuci ya tabbatar da rikici ko matsala a tsakiyar labari.
-Marubuci ya tababtar ƙarshen labarinsa ya zama mai gamsarwa.
-Sannan ya tabbatar tun daga farkon labarin ya tafi tiryan-tiryan har zuwa ƙarshe ba tare da zarmewa ba.
3. Taurari
-Marubuci ya tabbatar taurarin da ya sa a labarinsa, sun taka rawar da ya ba su yadda ya kamata.
-Marubuci ya tabbatar halayen taurarin sun bayyana a labarin.
-Ya tabbatar ayyukan da ya bai wa taurari sun tafi daidai da jigon labarin.
4. Salo/Sarrafa Harshe
-Marubuci ya tabbatar ya yi amfani da salo mai jan hankali (mai armashi)
-Ya tabbatar da ingantacciyar Hausa da zaɓin kalmomi.
-Marubuci ya guji maimaita wani abu ko tsawaita magana ko bayani (sai in dole ne)
5. Ƙirƙira
-Marubuci ya tabbatar shi ya ƙirƙiri labarinsa ba wanko shi ya yi ba, ko AI (ƙirƙirarriyar basira) ya bai wa, ya rubuta masa.
-Tunanin ya zama sabo ba gama-gari ba.
-Salon rubutun ya zama na daban.
6. Tsawon Labari
-Marubuci ya tabbatar ya bi ƙa’idar yawan kalmomin da aka buƙata.
7. Tasirin Labari
-Marubuci ya tabbatar labarin zai zama mai tasiri ga duk wanda ya karanta shi.
-Ya tabbatar ya zama mai kama zuciya.
8. Sunan Labari
-Marubuci ya tabbatar sunan labarinsa ya dace da abin da labarin ya ƙunsa.
-Ya zama mai jan hankali.
9. Tsari
-Marubuci ya tabbatar rubutunsa yana cikin tsari ba kura-kurai, cikin nau’in rubutu na Hausa.
-Kar marubuci ya cusa abubuwa da yawa marasa kan gado a labarin.
-Yana da kyau marubuci ya bar taurari su ba da labarin ta hanyar ayyukansu da maganganunsu. Kar marubuci ya shiga yana ta sharhi ko bayani.
-A ƙarshe, marubuci ya tabbatar ya yi gyara sosai a labarinsa.
Na gode
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
Ɗalibi
