Saturday, October 29, 2022

DUKAN ƊALIBAI

 DUKAN ƊALIBAI

(gajeren labari - 1)

A ƙofar makaranta an rubuta lokacin fara zuwan ɗalibai shi ne ƙarfe 7:00 na safe zuwa ƙarfe 8:00 za a rufe ƙofa, don haka ba yaron da za a bari ya shiga. 

Daidai misalin ƙarfe 7:15 na safen na iso ƙofar makarantar ɗauke da 'yata Ihsan a kan babur don kawo ta makaranta, ba a buɗe ƙofar ba.

“Ko ƙofar makarantar ba a buɗe ba.” Na ce da Ihsan. 

“Abba ko dai har an rufe ne?”

Na duba agogo, “ai lokacin rufewa bai yi ba. Amma sauka in gani.”

Ihsan ta sauka, ni ma na sauka, na kafe babur ɗin, na isa jikin ƙofar, na bubbuga. Jim kaɗan maigadi ya taso, da alamar daga barci yake.

“Maigadi ba a fara shiga makarantar ba ne?”

Yana murje idanunsa, “Gaskiya kai ne ka fara zuwa, don ina kwance da wani ya zo, da tuni ya tashe ni.”

Na girgiza kai, na koma gefe guda ni da Ihsan muka zubawa sarautar Allah ido. Har ƙarfe 8:30 na safe, babu wani malami ko shugaban makaranta da ya zo makarantar, haka dai ɗaliban da ba su wuce su shida ba, muna zaune suka zo.

Tunani na yi, Ihsan ba ta wuce shekaru goma sha biyu ba, bai kamata in bar ta a makarantar babu kowa, sai maigadi ba, sai kuma wasu masinjoji guda biyu. Kuma ga shi ina son in kai wani saƙo ofis, na dubi Ihsan.

“Ke zo mu je in kai wannan saƙon ma dawo tare.”

Muka hau babur, muka tafi. Mintuna ashirin a tsakani daidai ƙarfe 8:50 muka dawo, na riski a lokacin ɗalibai sun zo da yawa, har da wasu malamai a bakin ƙofar makarantar, don haka na ajiye Ihsan, na ce ta shiga makaranta sai na dawo.

*

Lokacin tashi daga makaranta, misalin ƙarfe 1:20 na dawo ɗaukar Ihsan, na riske ta a bakin ƙofar makaranta tana ta kuka, jikinta da hannunta akwai jini, hankalina ya tashi.

“Me ya faru, me aka yi miki Ihsan?” na buƙata a ruɗe. 

“Malaminmu ne ya doke ni.” Tana kukan take gaya min.

“Me kika yi masa?”

“Wai na yi latti ban zo da wuri ba.”

“Latti? Yana ina malamin?”

Yana ciki. Na ja hannunta, muka shiga da hanzari. A bakin ofis na tarar da shi zai fita.

“Malam me ya faru ka doki Ihsan?” Na nuna ta.

“Ba ta gaya maka abin da faru ba? Latti ta yi.”

“Latti, ƙarfe nawa ta zo?”

“Ba ta shigo makarantar nan ba sai 8:51.”

“To kai ƙarfe nawa ka zo makarantar?”

Ya ɗan yi tunani, sannan ya ce. 

“Ina nan tun ƙarfe 8:43…”

Bai kammala maganar ba na zabga masa mari, kafin zafin marin ya gama shiga jikinsa, na bi shi da naushi, kafin wani lokaci na haɗa masa jini da majina kamar yadda ya yi wa 'yata jina-jina. Tuni wasu malamai da shugaban makarantar sun iso wurin suna kallonmu.

“Ƙarfe 7 zuwa 8 kuka ce ɗalibai su zo makaranta, tun ƙarfe 7:15 muna ƙofar makarantar nan babu kowa a ciki har 8:30 na rabi, na ce ba zan bar 'yata a  inda babu wani da zai kular min da ita, na je na dawo da ita ƙarfe 8:40. Duk wancan lokacin ba ka zo ba sai bayan wannan lokacin shi ne kawai za ka doke ta saboda rashin mutunci da rashin sanin aiki. Har kana buɗe baki ka ce tun 8:43 ka zo…”

“Lallai ka yi min daidai kuma ka daki banza.” Cewar wani malami da ban gane ko wane ne ba. 


Mu haɗu a labari na 2

Kabiru Yusuf Fagge (Anka) 



RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...