SHARHIN LABARIN WATA SHARI’A… NA AMRA AUWAL MASHI.
ZAHARADDEN NASIR.
Manazarta su kan nazarci labari ne tun daga bangon littafin (idan bugagge ne) ma’ana publisher, har zuwa kalma, ko harafin qarshe da marubucin ya rubuta ya cikin labarin. Amma kasancewar wannan labarin online ne, to zamu fara ne daga sunansa zuwa abinda ya sauwaqa.
Idan aka ce wata shari’a… to abinda ake tsammanin ya boyi baya shi ne, ko dai sai Allah, ko kuma sai a lahira. Waxanda dukkansu zasu iya xaukar ma’ana xaya ne da ke nufin; tabbatar da haqqi a muhallinsa, ko a muhallin da ba nasa ba, bisa ga bayyanar hujjoji na zahiri. Waxanda zasu tilasta mai haqqin qyalewa dole sai anje lahira, Allah ya yi shari’ar da ita ce ta gaskiya. Ga duk wanda ya karanta labarin, zai ga yadda marubuciyar ta yi qoqarin nuna hakan, tsakanin Salma Abubakar (Gentle) da kuma Aishatu Abubakar (Ummimah), a labarce.
SALO; (plot) A cikin rabe-raben salon bada labarai guda tara da manazarta suka rarraba, marubuciyar ta xauki xaya daga cikin salaye masu wahalarwa wajen bayar da labarin. Inda ta fara bada labarin daga lokacin da lauyoyin nan biyu (mata da miji) suke sharara gudu a mota, bayan sun dawo daga aiki, wanda nan xin kusan tsakiyar labarin ne.
Mixing Plot; salon bayar da labari daga tsakiya, sai a dawo farko, sannan a koma qarshe. Marubuciyar ta yi qoqari wajen bayar da labarin bisa wannan tsarin, ba tare da zaren labarin ya tsinke mata ba. Sannan ta yi qoqari wajen jeranta tunanin mai karatu.
RIKICI; (Conflict) A labari shi ne tarzoma ko savanin da zai faru tsakanin babban tauraron labari, da kuma maqiyinsa. Wanda wannan shi ke haifar da gaba-xaya labarin ma, wanda daga qarshe za a sanya ran ganin sakamako, ko hukunci, har ma da darussan da ake so mai karatu ya xauka a cikinsa. Kamar yadda aka nuna savani tsakanin gentle da Ummimah a wannan labarin, aka kuma yi qoqari wajen nuna sakamako, tare da jefa darussan da na tabbata duk wanda ya karanta labarin zai ci karo da su a wurare da dama. Marubuciyar ta bi wasu matakai guda biyar, na dasawa, da havvakawa, tare da warware rikicin cikin labarin.
Gabatarwa; farko, ko gabatar da wani vangare na labarin, ta yadda mai karatu zai fahimci qashin bayan rikicin cikinsa. Shirya labarin, tare da bayyana taurarin ciki da alaqarsu da juna a cikin labarin. Kamar yadda marubuciyar ta nuna mana labara ne da ya shafi shari’a ko neman haqqi. Sannan ta nuna mana barista Umar, da Barista Sultana miji da mata ne da suke son juna, kuma suna aiki ne a waje xaya. Sannan ta nuna qashin bayan rikicin labarin a lokacin da saqon ku taimaka mata, kar su cutar da ita… yake shigowa cikin wayoyinsu.
Havvakawa; havvaka rikicin cikin labarin, tare da sanya zargin taurarin labarin a zukatan makaranta, da kuma haifar da zararrukan labara. Marubuciyar ta nuna mana hakan a labarinta, lokacin da saqonni suka yawaita shigowa na buqatar a taimaka, tare kuma da voye wanda ke turo da saqon, wanda hakan ya harzuqa lauyoyin biyu.
Tsanantawa; kai wa maqura wajen tsananin da rikici ya kai, tare da sanyawa makaranci tunanin ta ina nasara zata zo, ko ta ina faxuwa zata zo? Ta yadda masu karatu zasu cika shauqin son sanin abinda zai faru a gaba. Mun ga hakan a zaman kotun qarshe ta farko. A yayin da aka nemi Dr. Rafiq shaida ta qarshe da su barista Umar suka dogara da shi aka rasa.
Sassaurawa; nemo bakin zaren matsala, tare qoqarin warwaresu a hankali, ta yadda za a samu wata madogara qwaqqwara da zata jagoranci warwarewar komai. Kamar yadda bayyanar Dr. Rafiq, YB da sarki Manu, suka jagoranci warwarewar matsalar Ummimah.
Warwarewa; qarqare labari, tare da warware dukkan matsalolin da ke cikinsa. Da yin hukunci ga taurarin labarin. Kai tsaye mai karatu zai iya gane a inda labarin nan ya zo qarshe, tun ma kafin alqali ya yanke hukunci.
Marubuciyar ta yi amfani da salon qarqare labara cikin murna, wato Happy Resolution.
TAURARI DA XABI’UNSU
Daga irin rawar da taurarin labarin suka taka, za mu fahimci qwarewar da marubuciyar ta yi a fagen rubutu da kuma sanin xabi’u da halayen mutane.
Duk da kasancewar Barista Umar da Barista Sultana miji da mata ne da suke qaunar juna, tare da qoqarin farantawa junansu, daga rayuwarsu muna iya fahimtar yadda kowanne yake aiki tuquru don ganin ya yi abinda ya dace. Burin Barista Umar shi ne ya sauke haqqin iyalanshi, tare da qoqarin ganin cewa waninsu bai nemi wani abu ya rasa ba. A wurare da daman a labarin, muna ganin yana ajiye aiki a cikin gida duk muhimmancinsa, da zarar matarsa tazo gareshi. Daga xabi’unsa zamu fahimci xabi’ar maza ta rashin damuwa da duk wani abu da ake voye musu.
Burin Barista Sultana shi ne, kula da mijinta, ‘ya’yanta, da tarbiyarsu, da farin cikinsu. Ta yadda idan xayansu yayi kuka za tayi qoqarin sanin abin da ya sanya shi kukan tare da rarrashi. A xabi’unta zamu fahimci yadda mace ke damuwa da abinda ake voye mata.
Haka idan ka bi dukkan taurarin labarin zaka ga kowa ya dace da sunansa, da kuma irin rawar da ya taka.
SAITI
A labari saiti na nufin wuri, lokaci da kuma yanayin da labarin ya faru. Wanda duk za su iya zama na zahiri ko kuma qirqirarru. A labarin Wata shiri’a, marubuciyar ta yi amfani da wurare na zahiri lokaci da kuma yanayi. Kamar katsina, jalingo. Dama tun a farkon labarin muka fahimci a yanayin damuna muke. Sannan ko da ba a ambaci shekara ba, za mu iya fahimtar cewa a wannan zamanin ne labarin ya faru, duba da irin matsalolin da labarin ya qunsa waxanda duk irin na zamanin nan ne.
TSINKAYE
A kan samu nason hali ko xabi’ar mai aikin adabi a cikin aikinsa. Daga cikin abubuwan da zumu iya tsinkaye na halaye, ko buri, ko ra’ayin marubuciyar a cikin rubutunta, sun haxar da; tsafta, kulawa. Mun rula marubuciyar a kaloli tafi son kalar pink, sannan ko dai tana son ta iya sarrafa girki, ko kuma ta qware a fannin. Hakan ya bayyana ne ta wajen Barista Sultana.
Tana da son son ‘yan uwanta, tana son iyayenta, da matuqar yi musu biyayya, sannan tana da saurin kuka. Wannan ya bayyana ne ta vangaren Aisha Abubakar.
Tana da matuqar sadaukarwa, da tsayawa a kan gaskiya.
QARQAREWA.
Daga qarshe, zan qarqare da maganar wani masani da yake cewa;
Ba a amintar da gaskiya a kan cewa zata sha wahala ba, amma an amintar da ita a kan cewa ba zata tozarta ba.ba
Tabbas! Labarin wata shri’a… ya hau kan doron wannan maganar, ga duk wanda ya karanta zai tabbatar da haka.
ALHAMDULILLAHI.
ZAHARADDEN NASIR
07060861140
www.zaharaddennasir9@gmail.com